← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 66

Sashe 9

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NURU kuwa Har suka Isa delah tunaninta bai daina zurfafaba gabaki daya yanzu kanta a toshe yake sai yanda akai da ita yanzu kenan.
Tana Isa sashenta daki ta wuce Kai tsaye ko tubewa bataiba ta kwanta tareda rintse ido.
Washe gari haka akai fita da ita zuwa gurin passport Wanda tun kafin su Isa aka tanadi komai babu Wanda yasamu damar ganin fuskarta sai Wanda ya dauka hotonta dagacan Kai tsaye delah suka dawo washe garima saida aka futa da ita zuwa wani gurin wanda acanma tasake tabbatarda mulki wani abune na daban sbd irin girman da ake Basu ko cikin ansan cewar bama daya daga cikin jinin sarautaceba ita din.

Ranarda ta cika kwana shida da zuwa gidansu ranar aka gama Shirin tafiyarta tsaf a washe gari itada jekadi jirginsu yabar Ethiopia zuwa qasar France.

***********
Breakfast sukeyi zaune su uku akan dining din Wanda suka kwana biyu Basu samu damar cin abinci tareda dad din nasuba sbd rashin zamansa a kwanakin sai yau,
Kallonsa AFIA tayi taga yanda yayi wani irin fresh fatarsa sai wani glowing takeyi tsabar hutu da arzikin dukiya duk da manyancinsa Amma Sam fatarsa taqi bayyana hakan idanma batai kuskure ba saitaga kamar bayan rabuwarsa da mum dinta wani nutsuwa yasamu.

Sake kallonsa tayi wannan karon suka hada ido ya zuba Mata manyan fararen idanuwansa cikin muryarsa me iko yace"

AFIA akwai wani abu ne?

Aje spoon din hannunta tayi ahankali tareda kallonsa gabaki daya cikin taushin murya da 'yar sakuwa tace"

Dad please for how long zamuyita zama haka mum Sarah kwanakin Nan batajin Dadi qafafunta sunfara gazawa Ina tsoron zamu koma rayuwa mu kadai dagani sai farhat sauran maids din babu wani kusanci ko shaquwa tsakaninmu dasu.

Ciki wani irin Isa ya kurba ruwan Black coffee dake cikin farin teacup din hannunsa ya ajiye tareda daukan tissue yakai bakinsa ya goge ahankali ya ajiye tukuna ya dago ya kalleta yaji zancenta ya taba zuciyarsa tabbas suna buqatan abokin zama kada kadaici yayi musu illah gasu yara qananu,
Sam baida sha'awar maidasu zama gizah gurin mahaifiyarsa sbd kada giyar sarauta da mulki ya shigesu Dan kuwa tabbas zai shigesu sbd girma da irin bauta musun daza'aitayi zai gurbata tunaninsu sarauta zatai musu muguwar shiga bazai taba son hakanba Dan haka a yanzu dai baida wani zabi bayan karban negestatin Kaleb Amma bazai taba Bari Susan da hakanba sbd bai karbetaba bakuma zai taba karbantaba zaidai kawo musu itane amatsayin abokiyar debe kewa.

Kallon afian yasake Yi tareda Dan sassauta fuskarsa batareda murmushin yafito dukaba yace"

Akwai abokiyar zama da debe kewa da Kaleb zai Aiko muku da ita ta musamman Dan haka karku damu damuwa ya qare ok??""yafada Yana shafa kan farhat dake kusa dashi tana cin pancakes da Zuma.

Cikin tsananin murna afia tace"

Dad daga delah ne za'a kawo Mana ita?

Gyada Mata Kai yayi cikin Jin dadin ganin farin ciki akan fuskarsu yace"

Yes my angels Dan haka kunada baquwa yanzu Dan haka no worries no sad face no complains.

Yes dady" farhat ta fada tana riqe hannunsa suka miqe tare suna barin dining din Dan yanzu haka yauma tafiya zaiyi zai Kwana biyu acan.

Har mota suka rakasa ya tafi dayake yau weekends ne ba school Yana wucewa suka dawo ciki cikin farin ciki sukaje suna fadawa mum Sarah sunada baquwa tananan zuwa.

Yana barin gida direct airport aka nufa dashi ya Jima Yana tunani kafin ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya lalubo numbern jekadin kakarsa wadda yasan itace maganar negestati take gurinta Kira daya tana ganin me Kira ta daga cikin tsananin girmamawa hadda durqusawa duk da ba agabansa takeba tahau jero gaisuwa Yana sauraronta kafin ya dakatar da ita ta hanyar amsawa a gajerance cikin nauyin murya kai tsaye yace tanason bayani akan negestatin Nan tahau jero Masa asalin NURU da sunanta dakomai akanta cikin gajiya da zancen ya katse Kai tsaye yace"

Kada su afia su taba sanin waccece ita da matsayin datazo dashi.

Angama MALEEK ubayd sarki me kujerar delah gizah.

Yana kashe wayar ya kasheta gabaki daya tareda ajiyewa Yana daukar iPad karanta wani saqo.
Suna Isa airport ba Bata lokaci yashiga jet suka daga.

Sukuma a washe garin aranar jirginsu ya sauka qasar Kai tsaye babbar mota tazo daga gidan daukarsu daga ita sai jekadi ne Dan haka suna isowa makeken gidan na UBAYD MALEEK aptrmt dukkanin masu aiki suka fito suna musu barka da zuwa akai ciki dasu suna shigowa babban palon gidan dayasa NURU Shan jinin jikinta sukai kicibis dasu afia dasuka fito tarbonsu afia na ganin NURU ta tsaya cak tana kallonta cikin yanayi na Jin dadin wannan ai qawace ma aka kawo Mata tasaki fuska sosai tana cewa"

Jekadi wannan ce wadda zata tayamu zaman?

Da sauri cikin girmamawa jekadi tace"

Eh ranki ya dade itace.

Jin haka farhat ta riqo hannun NURU tana cewa"

AFIA tanada kyau sosai kaman Barbie Dina ko???

NURU bayan zare ido Babu abinda takeyi tana kallonsu hankalinta nakan gidan Wanda yasa taji tsoron duniyama gabaki daya na shigarta.

Dakin mum Sarah jekadi tasauka itakuma NURU dakin AFIA afian tajata tana sake tambayar sunanta duk Dadi ya isheta sbd take taji tanason NURUn.
##MAMUH*
HASKE WRITERS.

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899
[9/6, 6:12 PM] Anty Rabi'at: _*Mamuhgee 7*_
Bin bayan afian take da kallo cikeda mamaki da 'dan Jin shakka shakka tareda tsoron binta zuwa dakinta sbd ko daga dirowar tasu ta fahimta tareda shedar da irin tsananin girman dasuke dashi na iko Dan duk Wanda jekadi ta russunawa Kai ba qarami bane me cikakken ikone na sarautar delah.
Suna Isa qofar makeken bedroom din afia ta bude qofar tareda fara shigewa tana juyowa fuska asake tace"

Welcome to my world beauty.

Tsayawa NURU tayi tana kallon dakin daga bakin qofa jikinta nasake yin sanyi da mutuwa sbd a wannan gabar takai qarshen shiga rikicitaccen tunanin inane wannan duniyar da aka kawota?.
Ganin kamar tashiga tunani da wasi wasi yasa AFIA kamo hannunta ahankali ta janyo hannun tana janyota cikin dakin ta tura qofa ta saketa ta nufi kan couch din dake dakin ta zauna ahankali tana waiwayowa inda NURUn ke tsaye har lokacin tace"

Kishigo karki tsaya anan Zaki gaji da tsayuwa.

Dan cika umarnin AFIA din ne kawai yasa NURU fara takowa tana qarasowa cikintsakiyar dakin fuskarta a qasa sbd yanzu Kam tafara tunanin bauta aka kawota tayi anan ba wai maganar negestati ba.

AFIA batason maimaita zance shiyasa ta miqe tareda fitowa dakin tasaka aka kirawo Mata jekadi tace tabiyota zuwa dakinta suna zuwa ta kalli NURUn kafin ta kalli jekadi Kai tsaye tace"

kiyi Mata bayanin banason wannan kakkamewan datake idan batada sakewa kokuma bazata iya sakewa damuba kawota baida amfani tunda sbd mu aka kawota anan Dan debe Mana kewa.

NURU dake sunkuye da Kai da sauri ta Dan dago ta kalli bakin afia din Jin ba maganar negestati ne yasa aka kawota ananba kenen Reno zatace kokuma aikatau kokuwa bauta zatace duk da taga afia din bazata wuce tsaranta ba Amma dai tana fatan koma tsaran meryam dinsu zataiwa bauta ba kamar afia datake tsaranta ba yafi mata tsari da nutsuwa akan zamowa abokiyar kwanciyar kokuma abokiyar nishadi neges dinta.

Kamar daga sama taji jekadi takira sunanta tana cewa"

Biyoni muje.

Sanyi jikinta yasakeyi ta juya anatse tabi bayanta tana sake sunkuyar da kanta harsun Kai qofa zasu fice afia tasauke ajiyar zuciya ta nufi kujera zata zauna tace"

Jekadi kibarta kawai kun gaji sbd doguwan tafiyan da kukai kuje da ita can ku huta kuci abinci da sauran abubuwan tukuna.

Yanda kikace haka za'ayi li'iliti(princess/gimbiya/'yar sarki)

Wucewa sukayi suka qarasa ficewa suka nufi can dakin da aka sauke jekadin.
Abinci suka fara ci Wanda NURU takasa ci sbd damuwa da tsananin tunanin Ina shin Ina rayuwarta ta dosa ne tare Kuma da fargaba haddama tsoro ta yanda za'ace anan za'a barta to tayaya zata iya rayuwa acikin wainda Bata saniba bama ta taba ganiba.
Ganin ta shiga damuwa da firgici sosai yasa jekadi Dan daka tawa tareda kallonta ta dauki cup din danyar madarar turawa me sanyi ta miqa Mata cikin kulawa tace"

Karba wannan Kisha zakiji dama daman damuwa sbd wata damuwar yunwa na shigowa cikinta.

Ba musu ta karba ahankali cikin sanyin murya tace"

Ameseginalehu(thank you/nagode)

Tana shanyewa ta miqe tashiga toilet din dakin tayo alwala tareda wankan da jekadi tace tayo Dan anan so biyu ko uku zata ringa wanka sbd ko masu aikin gidan tsaftarsu abin koyi da burgewace bare ta masu gidan.

Bayan fitowarta jekadi da kanta ta nuna Mata inda abin sallah ke shimfide Yana kallon gabas ta qarasa bayan ta Sanya doguwar jallabiya fara da lullubin sallah ta tada sallar.
Bayan ta idar duk sallolin da ake Binsu ta gyara zama jiki amace cikin damuwa.

Saida jekadi tayi sallolin itama kafin ta fuskanci NURUn tafara jero Mata bayaninda maleek ya buqaci datai na boye matsayin NURUn na negestati a zaman dazatai agidan kasancewar lefine zatayi nayiwa negestatin UBAYD MALEEK guda yasata Dan dauke kallonta daga NURUn tace"

Kicire damuwar komai ki kwantar da hankalinki sbd rayuwarki zata inganta zamanki anan din,
Kinzo Nan ne sbd Yaya 'yayan MALEEK UBAYD zama badan komaiba haka zalika maganar negestati gabaki daya anbarta inaga saikin dawo delah
Kwanciyan hankalinki shine na iyayenki dan haka yanxu Kam ma Kamar umarnin li'iliti AFIA ne ki sake acikinsu wata babbar sa'ar rayuwace Kika samu wadda kowace mace dake daular ethio ke marmarin samu Amma bazaki gane hakan ba wata qila sai gaban idan kinada rabo kenan Dan haka aikinki ayanxu kawai shine kulawa da 'yayansa cikin kulawa me kyau duk da li'iliti AFIA tsaranki ce bazaki iya Bata kulawaba Kamar farhat Dan haka farhat yanzu a qarqashin kulawanki take.
Chapter 9 · 0% Book details