← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 66

Sashe 50

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru maleek yayi Jin abinda mr Omar yace
Ya Dan sake gyara tsayuwa Yana tunanin Dole akwai dalilin neges na bawa Lailah damar zuwa gizah ta zauna itakuma gata idanuwanta sun rufe gabaki daya batada tunanin komai yanxu saita yanda zata farfado da kanta ta jikinsa take ya yanke shawaran zuwa gizah ya bude Baki cikin nutsuwar murya yace"

Kayi Mana Shirin komai gizah din zamuje wannan karon Ina buqatan tunatarda wasu waye maleek Incase idan sun samu mantuwa.

Yes maleek"Mr Omar yafada Yana kashe wayar maleek din take yakira ya sanarda tafiyar maleek aka garzaya karban tickets da komai.
Yaso barinta anan gidan yaje yadawo tukuna Amma Kuma bazai iyaba sbd duk tsoron dazai Bata hankalinsa zaifi kwanciya idan tana cikin mutane shiyasa ya maidata can gida zibrian gaba daya kafin suka wuce.

A gizah kuwa sosai yakoob yagano akwai abinda jekadi ke boyewa musamman Dama sunsan Dole itakadaice tasan inda padima take sbd itace wadda tashigo gizah din da ita Dan Haka ya kasa ya tsare cikin taku sosai harya gano inda take zuwa acan bayan sassan maleek duk da Bai Isa cikin sassanba ya isa kofar yasan akwai babban abinda maleek yasakata take boye gurin dangane da padima Dan Haka yakoma yafadawa neges komai
Cikin wani irin yanayi neges ya murmusa Yana jinjina Kai yace"

Ayi aike gurin tsohuwar matar maleek lailah cewa nabata damar zuwa muyi mgn.

Allah yaqara ma girma da lafiya."yakoob din yafada Yana yin baya baya ya juya ya fice.

Ta bangaren lailah kuwa yau ta samu damar Isa gurin hutawar neges Dan maganar aurenta da maleek data kawota har cikin palon akai Mata iso ta qaraso gabansa ta gaidashi cikin girmamawa kafin ta zauna cikin tata isar ta zamtowarta Matar asalin me mulkin
Take aka fara shigo da kayan marmari dasu Zuma da kayayyakin tabawa aka cike gurin tsab ta dago ta kalli kayan tareda dauke Kai sbd hakan tamkar cin fuskane ga maleek ace macen dake matsayin matarsa tana zaune gaban wani Wanda ba maleek ba har akawo Mata abinsha Dana ci Ana nufin taci gabansa wannan rashin darajar yayi yawa tana matsayin Matar maleek guda.

Numfashi ta sauke tareda waiwayowa ta kallesa Kai tsaye cikin tausasa harshe tace"

Allah ya taimaki neges me gizah ta yanxu ina maka barka da hutawa tareda barka da ganin wannan lokacin.

Kallonta yayi daka zaman hakimcen dayake ya Dan saki fuska wani murmushin dattijantaka na sauka kan fuskarsa yace"

Neges ya amsa Kuma Yana biki barka da fitowa medakin maleek na gizah.

Lailah tunda tashigo cikin zuriarsu take tsaye a wuyansa sbd mace ce me tsananin son mulki da Isa tareda kwadayin komai yazama Yana qarqashinta da ikonta Dan kuwa Jin take kamarma itace maleek din sbd sosai ikonta da gadararta ke bayyanarda mijintane me kujerar sosai take shigar Masa hanci Yana dannewa sbd taku da zamanta sirikarsa amma zai Bata darasi daidai da ajinta sbd ita takawo kanta gurinsa yanzu neman mafitar matsalarta da maleek.

Cikin nutsuwa da kulawa ya Dan juyo da Kai a kame yace"

Abu dayane akan matsalar aurenku da maleek shine karkata da hankalinsa yayi ta wani bangaren
Ma'ana wani Abu daya rinjayi tunaninsa akan iyalinsa.

Dagowa tayi cikin mamaki tace"

Akwai abinda ya rinjayesa kuwa bayan wannan auren da yayine...

Wani murmushin yakuma saki Yana cewa"

Mace bazata juyarda maleek ba ko wacece kuwa nafi sakaran wani Abu daban Wanda Banda sani akai Amma Dole saikin Saka ido kin bincika kin gano kafin asan inda gyaran zai faro.

Shiru tayi tana nazarin zancensa sbd Bai wani shigetaba zancen Dan kuwa duk me lafiya ya kalli al'amarin dakyau zai fahimci cewan Babu wani dalilin sauyawar maleek zallar halinsane rashin daukan reni ko kadan sai aure daya qara take hasaso wani abun daban Amma tunda yafadi hakan zata bincika tagani Dan a shirye take da maganin dukkanin abinda zai shata Mata layi da zamowa Matar maleek.

Batareda ya kalleta ba yasake Dora Mata tunanin bibiyar daddaqin abinda maleek ke tunani ta hanyar bibiyar jekadi sbd itace mafi amintar maleek a duk gizah da rayuwarsu bayan kaleeb da Mr Omar ko mahaifiyarsa Anneti batasan sirrinsaba sai wainnan mutanen uku.

Da wannan tunanin sosai lailah tasakawa jekadi ayar tambaya Dama tajima da sanin jekadi maqiyiyarta ce ba kauna atsakaninsu munafukartace kodan yanda tasamu cikakken bayanin jekadi itace tsaye akan komai na NURU a rayuwar maleek Dan Haka ta kanta zata fara saita rusa yardar dake tsakaninsu da maleek bayan tasan menene matsalar tukuna.

Bayan tabaro can sassan Anneti ta nufa akaiwa Anneti shelar isowarta tashigo cikin shigar alfarmarta kamar koyaushe ta zauna ta gaida Annetin Kamar dai yanda suka Saba cikin yanayi na Ni Matar neges nikuma Matar MALEEK Babu wata qarin Hira akai sbd Lailah har cikin ranta duk tsanarsu da qiyayyarsu takeji sbd sune munafukanta dasuka tsayawa NURU akan auren MALEEK Dan Haka Bata wani tsayaba ta wuce tabar Anneti da bin bayanta da kallon mamakinda baigama sakintaba saidai bazatani takan zancen lailah ba zata jira maleek yazo tana buqatan bayanin dawowan lailan.
##MAMUH#
[10/2, 7:32 PM] Sadeeya: *_Mamuhgee 41_*

Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is the time to glow🧖‍♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️

*****************
Tun dasukai magana da neges tasakawa jekadi ido sosai akan motsinta takai har bibiyarta tafarayi Amma sbd jekadin ta iya takunta fiyeda tunani lailan Bata taba samun damar sanin komai dangane da wani baqin yanayi ko sirri atareda jekadin ba harta fara sarewa daga bin daddaqin na jekadi sbd Sam ba dabiarta bace Dan ita ta dauki kanta tanada abinyi hakama ba girmanta bane tsayawa irin wainnan labe laben ga abun duniya yafara sakota gaba sbd yanzu rayuwarta ta wayi gari kowa baya tareda ita tun daga kan mijinta har yayanta su danginta ba'a magana sbd ta Jima da watsar dasu dama mahaifiyarta ta Dade da rasuwa mahaifintane kawai shima tsufa yacisa sosai har baya gane kowa sai anfada Masa wannan waye shiyasa batada lokacin kowa saina Gina rayuwarta sbd gidansu kaf kowa yazamo wani hamshaqan kansu duk da ita kadaice mace sai tana alaqanta kanta da matsayinsu suda suke maza bazata taba yadda itama ta zauna tana amfani da alfarmar wani ko sunansa so take ta Gina kanta da kanta ta yanda za'a fadeta da matsayin datake dashi badai da matsayin wani datake a qarqashinsaba shiyasa ta rufe ido ta watsar da 'yayanta da komai Amma yau ta wayi gari ko 'yan aiki batadasu sai guda biyu kacal da ganinsuma baqin ciki yake sanyata sbd Kamar Saida aka zabo wainda suka fi Muni da rashin kakkamtuwa aka Aiko matasu batada 'da, batada miji, batada gidan kanta bare matsayin kanta ko sunan Wanda zatace a qarqashin alfarmarsa take batada Dan Haka gabaki daya yanzu Jin take kamar ta rasa nustuwa da tunaninta Bata iya tunanin komai kanta ya toshe zuciyarta bayan kwashe kwashen tunane tunanen duniya dasuka kusa haukatata Babu abinda takeyi tarasa wazata zauna dashi ko masifa tayi ta rage abinda takeji bare.
Tunanin 'yarta afia ne yafado Mata Rai take taji idanuwanta na neman cikowa da hawaye ta hadiye tana miqewa zuwa bakin window ko zataji sanyi sanyi Amma takasa Saida hawayen suka tsinke Mata ta zauna bakin windon tana fashewa da wani irin kuka Mara sauti tana buqatan mutum atareda ita Wanda zai dubeta ya saurari damuwarta.
Afia take tsananin buqata ayau din sbd ta Dan duk duniya yanzu 'yartace kawai me iya rarrashinta ta rungumeta ta saurari duk haukar dazata iya fada da wadda zata iyayima kaf duniya yanzu 'yartace kawai me iya Mata wannan bayan ita ko maleek tasan bazai taba kallonta da idon sauki Kona mutunciba
Dan Haka hankalinta yaqara tashi tana jinta cikin mummunan yanayi na baqin cikin rayuwarta da Kamar tayi hasara.

Ta Jima Yana boyayyan kukan daya Gama kumbura idanuwanta da fuskar datake masifar ji da ita sunyi jajir sunyi suntum duk da hakan bataji wani sauki ko sassaucin komaiba ta miqe ta nufi toilet jiki amace ba kwari ta wanko fuskarta tareda yowar alwala Dan ko wankan batada karfin Yi tafito ta goge fuskarta ta tayarda sallar ishai da akai tun dazu bayan tagama akaro na farko bayan tsawon lokaci yau ta daga hannu tana rokon Allah sassauci da mafita sbd ada ganin tagama samun komai na rayuwa yasa sallah data zama Dole kawai takeyi Amma adhkar da sauran adduoi gurin ubangiji basa gabanta sbd duk abinda takeso tagama samu.
Chapter 50 · 0% Book details