← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 66

Sashe 13

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tafiyansa zamanta tayi apalon tana kallon cartoon sama sama sukuma suna can daki NURU na kwance idanuwanta arufe baccin dole nason daukarta.
Har dare a kame take da kanta acikin daki hakanan idan abin yadawo Mata sai tsoro yasake shigarta sbd tasan da a delah ne hakan yafaru Allah ne kawai yasan hukuncin dazata fuskanta akan ko hada hanya da MALEEK bare kusan karo Wanda taji lokacinda jikinsu ya 'dan shafu sbd itace me tudun qirji.
Afia taso fahimtan akwai wani abu atareda da sanyin NURUn Amma Kuma sanin halin NURUn na yau shiru gobe sakewa yasata sharewa Bata tsaya tambaya ba har sukai bacci.
Washe gari ma ko breakfast a kicin tayisa kafin suka wuce school tanaji afia na maganar dad dinta tafiya zaiyi yau itadai Bata iya cewa qala ba sbd duk lokacinda su afia da farhat suka dauko maganar dad dinsu Bata taba Koda kuskuren saka Baki ba sbd sanin matsayinta be Kai na saka Baki a zancensaba.

Weekend nayi Barr IMRAN JALALUDDEEN 'dan babban yayan lailah dake qasar ta France shima wato babban tsohon chief minister na esthern ambassador Wanda bayan manyancinsa yakoma gida Amma shi 'dansa IMRAN na zaune anan qasar haryanxu sbd anan yake karatu tareda aikin gamayyar wani sashen kamfanin MALEEK dake qasar yazo gidan da maraice cikin lafiyayyar motarsa white jaguar Yana sanye da designers qananun Kaya dark blue na _Jimmy choo_ wainda suka fito da asalin kyawunsa na Dan Africa sai qamshin Mara hayaniya dayake fitarwa kallo daya afia tayi Masa kaman koyaushe data Saba tace"

Hmm Uncle u look great.

Murmushi yasaki Yana kallon NURU dake gefenta zaune kan kujera tana qoqarin hada wasu kalmomin English a iPad tana sanye da riga da wandon Palazzo me Fadi sosai rigarce kawai takeda shape itama Bata roba bace chiffon ce sai gashin kanta dake dunqule cikin Dan qaramin scarf da turkian gabaki daya hankalinta nakan abinda takeyi dan Monday zatayiwa malamarsu Mrs Edward presenting karatun shiyasa hankalinta baya kansu tunda ta Masa Ina wuni bayan shigowarsa.

Dauke kallonsa yayi daga kan NURU cikin basarwa yasaki wani boyayyan murmushi yana cewa idan sun shirya su taso suje a Kai farhat garden datakeson zuwa.

NURU bataso zuwa ba sbd karatun daya gama daddaure kanta da tunaninta Amma farhat ta takura akan ita da ita takeson aje dole badan tasoba tashiga ciki ta sauyo dankwalin kanta zuwa veil Mara datayi Rollin sai takalmi data sanyo loafers sabanin Afia datai ado bame yawaba itama kusan irin kayan NURU ne ajikinta suka fito suka wuce afian ce Agaba sai farhat da ita NURUn a baya wadda Sam ko kallon sosai bataiwa Imran ba bare ta lura da Yana Dan kallonta akai akai sbd gabaki daya ita bataso fitanba taso tsayawa tayi karatunta Dan yanzu data fara sanin kanshi da wayar karatun batada babban burin daya wuce samun ilimi me zurfi domin tsayuwa da kanta da iyayenta shiyasa yanzu kwata kwata batada lokacin batawa sbd karatu.

Duk wani yawo da tarin siyayyan da akayo a fitar basa kanta gida tamatsu su koma Dan haka harsuka gama yawon suka dawo bazatace ga takamaimai na kamannin Imran jalal ba Amma shikam yagama karanceta tsaf kaman yanda yake buqata musamman dayayi fira da farhat Sosai yagama fahimtar babban burin NURUn yanzu karatu ne sai hakan yasakashi farin ciki sbd dukkanin wannan na daya daga cikin abinda yake tsananin so ga irin matarda yake ra'ayi.

Ko kafin Monday karatunta tagama fahimatarsa sbd takuran data saka kanta ta saka afia Saida ta tayata bayani harta fahimta dakyau dakyau shiyasa Monday din harsuka je suka dawo cikin annashuwa take musamman data fara da samun yabo gurin Mrs Edward.

Imran jalal kuwa da zuciyarsa takasa hkr da rashin bawa kasa dama agurin NURU yasashi dawo da ziyarar daya Dade da daina kawowa gidan ahankali ahankali tun Bata wani bi takan sha'aninsa dasu afia harta fara sabawa dashin musamman akan karatun dayake dorata akai sosai Dan hakan sai sabo yashiga tsakaninsu duk da baitaba nuna wata alamar so atareda Shiba sbd yasan Basu Isa fara soyayyaba ayanzu tunda karatu ne agabansu sai sunshiga University Koda zasu fara bawa wata soyayya dama.

A bangare makaranta kuwa karatu tuni yadau hanyar nisa Dan kuwa yanzu tana farkon shiga aji uku ita kuwa Afia tana shirye shiryen zuwa _Las Vegas_ karatun shekara daya kafin tadawo tashiga University anan Paris dan haka sai suka Dan shiga damuwa sbd sunrigada sunyi wata irin shaquwa yanzu wadda Sam basa iya ko yini batareda junaba gashi zasuyi rabuwan shekara daya duk da zata ringa zuwa hutu.

Ranar dazata wuce tareda dad dinsu zata tafi Dan haka rakiyar NURU iyakacinta palon ciki Bata fito babban ba har suka wuce cikeda kewar juna.

Bayan tafiyan AFIA sai Kamar wani babban nauyi yahau kan NURU sbd yanzu itace shugabar gidan ita ke bada umarnin komai ta bangare daya ga karatunta ga kula da farhat wadda itama kewar afia ta tabata Amma kasancewar yanzu tamkar ma uwa take ganin NURU sai Bata wani jimaba cikin damuwan tafiyan AFIA din takomawarta Kiriniyarta.

Yau Kam amatuqar gajiye take sbd Suma sunfara shirye shiryen fara midterm exams Dan haka karatu take Babu sauqi ta Dan hakan tana dawowa daga school wanka tayi bayan ta tabbatarda farhat tayi baccin Rana sai itama Takoma daki tayi Mata wankan ta Sanya riga fara mara nauyi da dogon pencil jeans Wanda yakama siraran cinyoyinta tareda bayyana fadin hips dinta ta sanyo hular dabata rufe kanta dukaba ta fito taje kicin tasamu fresh milk me sanyi sosai Tasha tareda lumshe fararen idanuwanta dasuka gama galabaituwa da gajiya ta fito riqeda sauran madaran tazo Palo ta zauna tana daukan wayan afia data kirata suka fara waya tun tana sawa har bacci me Dadi yafara Dan fizgarta Dole sukabar wayar ko motsawa batai daga gurinba bacci me nauyi yayi gaba da ita a palon.

Farhat data tashi nata baccin tana fitowa palon taga NURU tayi bacci kan kujera ta kalla kyakkyawar fuskarta datai fresh sbd samun hutu da gyara saita saki murmushi tareda qarasowa zata gyara Mata kwanciya ganin kaman zata fado tana Dora hannunta akanta taji dirin motocin dad dinta yadawo cikeda farin ciki ta miqe ta nufo qofa da sauri ko ta bude tareda rumgumesa cikin qasa qasa da murya tace"

Welcome dady.

Kallonta yayi cikin kulawa da mamakin meya samu muryanta take magana ahankali
Duk da qarancin shekarunta ta dade da sanin dad dinsu ba komai yake budewa Baki yayi magana ba da kallo ma kawai suna gane maganarsa Dan haka ta fahimci mamakinsa tasakeyin qasa da murya cikin rada tace"

Dady Lewa na Palo and she's sleeping tagaji sosai da yawa koyaushe batada time din hutawa yanzu tasamu tayi bacci please dady kadamu tasheta.

Kallonta yayi suna qarasowa tsakiyar palon dan dama yasan tsawon shekarun Nan farhat Bata mgnar daya biyu saita lewa,my Lewa,my beauty kunnuwansa harsun gaji dajin sunan abakin farhat.

Dan juyi tayi daga kwancen ta sulmoyi zata fado da sauri farhat tayi kanta ta tareta Amma sbd NURUn tafita girma da nauyi saita kasa tareda saima danneta da NURUn tayi batasaniba sbd baccin yayi Mata nauyi sosai Dan tajima Bata baccin kirki Koda daddare.

Da sauri farhat ta kalli inda yake tsaye cak Yana kallon qanqanuwar yarinyar dabatafi AFIA shekaru da girman jiki da komaima.
Cikin wuya farhat tace"

Dady hannuna zai karye aunt NURU nada nauyi sosai.

Cikin wani irin taku da izzar data gama kame jininsa ya iso gurin batareda ya kalli NURUn ba ya Dan ranqwafo yakai dogayen hannuwansa masu siffar qarfi tareda tsananin taushi ya zura qarqashin bayan NURUn farhat tasamu damar janye hannunta tana yarfewa tayi dakinta da gudu tana cewa hannuna zai kumbura Bari nashafa ointment da sauri kada ya kumbura aunt NURU nada nauyi sosai.

Idanuwansa dake raunana kuzarin Wanda duk ya zubawa su ya waiwayo ya zubawa fuskar NURU wadda take wani glowing na zallar asalin kyawun da Allah yayi Mata.
Gangarowa yayi da kallonsa kadan zuwa jikinta a qirjinta ya dakatar da kallon tareda dauke fuska Yana zare hannuwansa daga qarqashinta yabar gurin sai ayau yasan babban shirmen da Kaleb ya tafka da jekadi kenan tsarar 'yar cikinsa suka kawo Masa amatsayin negestati,
Ta Yaya suke tunanin wannan yarinyar tsarar afia zai iya hada shimfida da ita?Tama Yaya zata iya daukan nauyinsa ko ciki baya tunanin kwsmkesonta zai iya dauka bare haihuwa... unbelievable" yafada cikin zuciyarsa a 'dan takaice sbd tunano 'yarsa afia dake tsararta baya tunanin ko Nanda shekara biyar zai aurar da ita Dan ganin kaman tayi mugun qanqanta amma shi ba saurayiba ko 'dan samari akawo Masa wannan.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899
[9/8, 4:31 PM] Ummuanwar🥰: *_MG 11_*
Sai magrib ta farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi sosai tana kallon inda take ta lumshe idanu tana sake tabbatarda tabbas ta gaji matuqa gabaki daya rayuwarta yanzu hutu takeso Dan hakan zata sassautawa kanta tunda dai karatun yanzu yazaunu a kanta.
Tashi tayi zaune tana shafa wuyanta dayayi Mata sakayau sbd yanayin yanda tayi kwanciyar.
A kasale ta miqe tayi ciki tana duba qaton agogon dake bangon palon ta shige palon ciki ta doshi hanyar bedroom dinsu tashige.

Saidayi sallah kafin tayi wanka ta Sanya doguwar riga Mara nauyi black me dogon hannun Kuma har qasa take komaima Bata sanyo akantaba ta fito ta nufi dakin farhat tana Kiran sunanta.

Zaune take tana homework NURUn ta shigo taqaraso kusa da ita ta zauna farhat din ta haye cinyarta tana cewa"

My Lewa dubamin kigani yayi daidai kuwa?

Murmushi NURU tayi tana karba tafara dubawa tana cewa"

Ni danasan farhat Dina nada kokari Babu homework da bazata iyayi daidai ba Amma dai yanzu kinajiye muje kici abinci tukuna daga baya a qarasa lokacin cin abinci yayi.

Kwantawa tayi jikin NURUn tana cewa"
Chapter 13 · 0% Book details