← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Shiga dakin farhat ya saki hannunta ya janyo rigar abayarta dake kan gado ya miqa Mata ta karba jikinta ba karfi ta Sanya ta ya sake kamo hannunta suka fito ta gaban lailah da afia suka wuce
Farhat dake hannun mum Sarah ta kwace tabiyosu da gudu ta riqe hannun NURU wadda ta tsaya sai alokacin idanuwanta suka fara kokarin cikowa da hawaye ta kalli farhat din tana sake qanqameta ta dago ta kallesa ya kalli hawayen dake kokarin sauko Mata yace"

Zakije da ita?

Gyada Masa Kai tayi da sauri
Ya kamo hannun farhat din da hannunsa daya suka fice
Suna fitowa Mr Omar ya budewa NURU kofa tafara shiga kafin MALEEK ya zagaya mr Omar din ya bude Masa shima yashiga ya rufe kafin ya kamata hannun farhat ya bude gaba ya sakata ya zagaya ya shiga motar yaja suka bar gidan.

Lailah datayi mutuwar tsaye hannu take neman dorawa akai Amma kunyar 'yartama data masu aikin ta hanata kurma ihu ta zame kan kujera tana kokarin shanye hawayen dake ciko Mata idanuwa su koma.

Afia kuwa kuka tasake wiwiwi me qarfi tareda zubewa qasa Dan kuwa mum dinta tagama da rayuwarta Kamar yanda tagama da tata Dan kuwa tafi kowa sanin halin dad dinta musamman yau da zallar bacin ransa ya fito danma agaban masu aikine yasa ya Hana fushinsa bayyanuwa.

Mum Sarah na ganin hakan ta juya da sauri tayi ciki ta Isa part din masu aiki tace kowa ya shirya kayansa yanzu yanzu za'a kwashesu zasu bar gidan zuwa sabon gidan NURU.

Da sauri suka mimmiqe suka hau hada 'yan kayansu na sawa
Mum Sarah din tafito ta nufi harabar gidan ta sanarda securities saqon Mr Omar daga maleek take suma suka tashi dama Babu me wani kayan shirgi komai na gidan a tsari yake har masu Aiki da masu tsaro.
Tana Gama sanarwa kowa ta nufa nata dakin ta jera kayanta cikin akwati tsaf ta fito ta nufa dakinsu farhat ta hadawa NURU da farhat kayan buqatansu cikin Yar karamar akwatin farhat din sai schoolbag din farhat Amma bataga kayan NURU ba dayake suna dakin afia sai Bata daukar Mata kayaba ta fito dasu takai dakinta daganan Babu Wanda yasake fitowa sbd tashin hankalin da masifar dasuka gani tsagwaro atareda lailah.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899
[9/27, 7:25 PM] Anty Rabi'at: *_Mamuhgee 36_*

_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_

****************
Suna fitowa Kai tsaye wani qaramin underground gidansa dake cikin anguwar suka nufa Wanda keda 2 bedrooms rak da manyan Palo guda biyu sai kitchen me hade da dining acikinsa komai na gidan is milk Mr Omar ne kawai yasanda gidan Babu Wanda yasan gidan nasane Haka gidan komai a kip kip yake anan yake wasu private wayoyinsa da ayyukansa hakama wata maganar me buqatan tsananin sirri anan suke zuwa suyita da Mr Omar.

Parking Mr Omar yayi yafito ya budewa MALEEK yafito kafin yabudewa NURU ita saiya zagaya ya budewa farhat tareda kamo hannunta suka biyo bayan maleek dake gaba tareda NURU dake tafiya ahankali sbd ciwon Mara.
Suna shiga palon NURU ta dago ta kalli koina cikin palon cikeda mamakin tsaruwar gidan da cikin yafi wajenma kyau sosai saidai sbd yanayinta bazata iya qarewa koina kalloba a matse take data samu guri ta kwanta Tasha ruwan zafi masu zafi Sosai ko zata Dan fada Mata tasamu period din ya sauko wahalar ta rage Mata.

A palon farko ya dakata tareda kallonta Yana nuna Mata kofar palon qurya inda bedrooms suke cikin nutsuwa yace"

Ki Shiga ciki zanyi mgn da Mr Omar.

Dan dagowa tayi ta kallesa har lokacin ita yake kallo ta gyada Kai ahankali ta juya farhat na riqeda hannunta suka wuce cikin.

Palon cikin baiyi girman na farkon ba Amma yafisa tsaruwa ta juya gurin bedrooms din ta nufi Wanda yake damarta ta murda tareda budewa ahankali batasan lokacinda ta sauke ajiyar zuciyaba sbd ganin girma da tsaruwar dakin ga makeken gadon daya kusa cika dakin komai fes fes sai qamshi koina gidan keyi da Alama kullum Ana gyara koina agidan ayi mopping Dan ko yau kila anyi Dan qamshin dayake koina dagaji sabon gyarane.

Tana Isa bakin gadon ta sulale ta haye tareda kwantawa tana dungulewa guri daya tana dafe mararta rufe idanuwanta tana Jin Dan dama dama data kwanta din.
Sai daga baya ta bude idanuwanta ahankali ta kalli farhat da duk tayi wani iri sbd halinda aka shiga sai taji yarinyar tasake shiga ranta sbd tausayinta ta cire hannu daya takamota kusada ita ta bude Baki daqyar tace"

Sweetie kadakiji tsoro ko damuwan komai kinji daddy Yana Nan Nima Ina Nan Afia ma zatazo komai lafiya Inshallah,yanzu Kinga Banda lafiya I can't treat and drss your wound kije kifadawa daddy Akira mum Sarah tazo ko Dr aduba kafanki kafin anjima nasamu naji Dan sauki kinji.

Gyada Kai tayi tareda juyawa ta fice zuwa gurin daddynta din.
Tana fita NURU tasake nadewa guri daya kaman jira Marar keyi ta kwanta tasamu nutsuwa sai ciwon yasake taso Mata wani irin zafi da zufa suka fara karyo Mata ta tashi zaune daqyar ta kunna AC Takoma ta kwanta tana shigewa cikin bargon dake kan gadon me tsananin laushi fari tas.

Kallon Mr Omar maleek yayi yace"

Kasan abinda zakayi next idan an daukosu din.

Gyada Kai Mr Omar yayi Yana cewa"

Za'a kaisu wancan gidan ne na 7579 zibrian kowa yasan aikinsa yakama suyi gyaran koina Kafin zuwa gobe ko jibi ku Isa can din.

Gyada Masa Kai maleek yayi Kai tsaye zai juya saiga farhat ta qaraso gurinsa ta shige jikinsa tana cewa"

Daddy aunt NURU batada lafiya bazata iya duba ciwona ba tace Akira min mum Sarah ko Dr" taqarasa fada tana nuna kafarta.

Kallon kafar sukayi dukkaninsu inda ruwan zafin suka zubar Mata a kafa sai alokacin sukasani ga 'yar farar kafar tata har tayi ja
Maleek ya dago ya kalli farhat din yace"

Aunt dinki bazata iya duba Miki qafanba ta gyara?

Eh daddy tun jiya da daddare aunt NURU tace cikinta na ciwo haryanxu be Dena ba gurin karbo Mata tea ne ruwan zafin ya zuba a kafana mum taketa fada.

Shiru maleek yayi kafin ya dago ya kalli Mr Omar dayayi saurin rage kansa Yana cewa"

Za'a kaita gurin Sarah acan zibrian ta kula da qafar kafin ku iso zankira Dr Damien ma yazo ya duba kafan Inshallah.

Kama hannun farhat Mr Omar din yayi Yayi gaba suka fice ya nufi mota ya bude ya sakata ya zagaya yashiga Yana waya da Edward akan idan sun Isa zibrian din da kowa yace Masa eh ankai kowa Babu Wanda aka baro a tsohon gidan sai tsohuwan madam da princess afia.
Kashe wayarsa yayi ya fita harabar gidan yahau hanyar zuwa zibrian din Yana yiwa farhat 'yar Wasa tadawo yanda take sbd yarinyar ta Dan razana da komai daya faru.

Bayan tafiyar Mr Omar ya juyo Kai tsaye ya nufi hanyar dayan bedroom Wanda ba nasaba ya Murda Kai tsaye ya tura yana kallon koina baiganta acikiba ya fito tareda rufo qofar ya nufi bedroom dinda yake gefe dabam Wanda yake matsayin nasa Yana zuwa ya bude kofar ahankali ya shiga tareda rufowa yana kallon yanda ta kwanta a dungule ya ajiye wayoyinsa kan qaramin glass table dake gefen sofar dakin ya qarasa gadon tareda tsayawa akanta Yana kallonta har saidataji mutum tsaye akanta ta bude idanuwanta ahankali ta dago dasu ta kallesa ta Mayar ta rufe tana yunqurin tashi zaune ya dakatar da ita ta hanyar Kai hannunsa daya ya maidata kwance Yana kallon wuyanta daya taba yaji zafi.

Wayarsace tayi blinkin na wuta batareda ya daukaba ya waiwaya ya kalli wayar yaga massage din Mr Omar ne daya rubuto" _Dr Damien na ya iso Yana kofa_

Zaunawa yayi bakin gadon tareda yaye bargonta ahankali tareda tayarda ita zaune da kansa Yana kallonta ahankali yace"

Dr Damien zai dubaki.

Zuba Masa idanuwanta dasukai laushi tayi tanason ce Masa Bata buqatar likita Amma sai batace komaiba ta gyada Masa Kai tana matsowa bakin gadon ta zura qafafunta qasa ya miqa Mata hannunsa ahankali ta dago ta kallesa kafin ta Dora nata akai ta Kama nasa ya miqar da ita hannunta cikin nasa suka fito Palo suka sake wucewa zuwa na farko acan suka tararda Dr Damien tareda Mr Omar dake tsaye Yana ganin fitowarsu ya sauke Kai tareda juyawa ya fice Dan Basu guri.

Daga yanda Dr Damien yafara tambayarta tabashi amsa Kai tsaye Dr Damien ya fahimci ciwonta yace"

Bawani matsala bane menstrual pains ne kawai
Ya Bata pain reliever da wasu maganin ya miqe ya fice.

Kallonta maleek yayi Kai tsaye yace"

Kina buqatan wani Abu?

Gyada Kai tayi tana miqewa suka nufi ciki tana cewa"

Zanyiwa Mr Omar texting dinsu.

Kallonta yayi bayan sunshiga dakin ya matsota jikinsa sosai ya ranqwafo da kansa daidai fuskarta yace"

Kiyi online shopping akawo daga can Mr Omar baya buqatan sanin abubuwan dazaki buqata.
Chapter 44 · 0% Book details