← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 66

Sashe 19

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kammala komai tayi ta diba nata ta jera a tray ta fice daga kicin din tabarwa Fana ta jeresu a dining.
Koda taje daki ta aje abincin tafaraci tana amsawa afia firarta sama sama
Dataga ma ba iyacin abincin zatayiba saita shanye drink din kawai ta bar abincin.
bayan sallar magriba motar data dauko MALEEK daga airport tana shigowa gidan su Kuma lokacin sun gama sallolinsu suna zaune a Palo na biyu farhat na kwance jikinta tana kallon cartoon AFIA Kuma na gefensu itama riqeda wani hardcover t book tana karantawa ita Kuma NURUn tayi nisa sosai a tunanin abinda yake damunta hankalinta gabaki daya yabar jikinta zaune kawai take.

Karan doorbell yasa AFIA kallon farhat sbd sanin Babu masu aiki ko daya yanzu a part din lokacin shigewarsu yayi sun koma part din masu aiki saikuma gobe tace"

Farhat kije ki bude kofa I think Imran ne yazo yanzu.

Sunan Imran din da AFIA ta fada yasata dawowa hankalinta ta juya a hankali ta kalli afia murya a Sanyaye tace"

Kina magana ne?

Batareda ta juyoba hankalinta na kan littafin datake karatu ita afian tace"

Eh inaga Imran Yana bakin qofane doorbell Yana qara.

Kallon hanyar fita palon zuwa palon farko NURU tayi cikin nazari saidai Kuma dama tasan zaiyi wuya Imran din yaqi dawowa yau din sbd sauyin daya gani tattareda ita dakuma nacinsa akan maganar aurensu.

Zame farhat tayi daga jikinta tareda Miqewa tsaye ta nufi daki ta doro qaramin mayafin doguwar riga akan kayan jikinta ta fito ta nufi qofa ta budu Kai tsaye tareda bude Baki zatai mgnar idanuwanta suka sauka kan Mr Omar dake Danna doorbell din gabanta yayi mummunan faduwa ta saci kallon bayansa daidai isowar MALEEK din sai Imran a bayansa Wanda da gani shima isowarsa kenen mr Omar ya juya da sauri yabar gurin ganin MALEEK ya qaraso,
Take taji qafafunta na neman Gaza daukarta tayi saurin kaucewa daga bakin qofar tana sauke kanta sbd wani irin kwarjini da cika Mata idanuwa dayayi saikuma shedan dake dawo Mata da tunanin abinda yafaru dasu a Vegas sai kunyar al'amarin na bayyanuwa atareda ita Wanda yasata dagowa ahankali ta sake kallonsa daidai kawowarsa daf da ita idanuwanta suka hadu da nasa idanuwan dasuka kusa sata zubewa agurin batasan lokacinda ta bude bakiba da siririyar muryarta tace"

Barka da dawowa.

Akaron farko daya bude Baki ya amsa Mata da"
Yawwa.

Gabaki daya Jin tayi tana neman rikicewa har batasan lokacinda ta rufe qofa da qarfiba Wanda ta daki hancin Imran daya fara shigowaba da qarfi har baisan sanda ya saki qara me qarfiba wadda tasata dawowa hayyacinta da sauri ta bude qofar cikin damuwa da kulawa tayi kansa tana cewa"

Oh my God, I'm so sorry Im banluraba na manta kana baya, please let me take a look"" tafada tana duba hancinsa da harya fara ja abinka da farin mutum ga idanuwansa tuni suka cicciko da ruwa sbd hancin daya bugu sosai.

Rufe hancin yayi Yana cewa"

No karki damu ba wani matsala bane buguwane kawai.

Im dan Allah kayi hakuri bansan meyake damunaba bansan tunanin me nakeba.

Shihhhh ya isa haka just relax sweetheart am fine
Duba kiga hancinma ya sauka.

Fuskar tausayi tayi tana sake kallonsa da alamar ban hkr tace"

Shigo ciki na dauko ointment sai a shafa agurin.

Ki barshi zanje gida zanshafa idan naje gidan kishiga gobe zandawo da safe dama nazo Naga ko kina lafiyane kishiga ciki Saida safe.

Im you sure you're ok??tafada tana kallonsa.

Murmushi yasakar Mata Yana cewa"

See you tomorrow.""ya wuce.

Saidataga tashin motarsa kafin ta sauke numfashi Mara sauti ta juyo ciki ta rufe kofa tanajin ba Dadi cikin ranta.

Hanyar kicin ta nufa Dan daukan ruwa tana kaiwa dining room ga tarin dibbin mamakinta saitaga maleek zaune akan dining da kayan daya shigo dasu Wanda ke nuni da kaman tunda yashigo Yana gurin bai qarasa samanshi ba kenan ko su afia Basu San da dawowarshiba.

Fatar wuyansa dake sheqi take kallo har zuwa hannayensa data tuno tsananin laushin dasukedashi da sauri ta Kori shedan tareda juyawa zatabar gurin kamar daga sama taji muryarsa me kamewa yace"

Serve me.

Tsayawa tayi cak daga inda take tsaye sbd Bata taba tunanin yasan da tsayuwarta a gurinba,
saidata sauke numfashi ta daidaita nustuwarta kafin ta juyo cikin nutsuwa ta qaraso gabansa a ladabce tasake bude Baki tace"

Barka da fitowa.

Bai amsaba sbd fuskarsa dake kame
Ta matso sosai tareda fara bubbude abincin ta zuba Masa Kamar yanda ta kwatanci zaici ta juya zuwa kicin ta bude fridge ta dauko qaton royal silver jug na fresh fruit juice ta kawo daidai fitowar farhat data biyo bayan NURUn ganin ta dade Bata dawoba daga bude kofar sbd matuqar NURU na gida Bata iya dadewa ba ajikintaba.
Ta kofar Palo ta hango dad dinsu a dining zaune cikin tsananin farin ciki ta qaraso da gudu tana cewa"

AFIA Daddy is back.

Qarasowanta da gudu yayi daidai da tsayuwan NURU a gefensa Dan zuba Masa juice ta fada jikin NURUn da qarfi wadda dama ita kuma ta fada jikinsa gabaki dayanta har ita har jug din juice din daya zube ajikinsu duk su biyun da sauri ta dago ta kalli fuskarsa da idanuwansa suka sauya launi ta kalli kanta datake zaune dare dare kan cinyoyinsa fuskarta da tashi na tsiyayan ruwan juice a rude batama saniba tsaban firgici ta zame qaramin gyalen kanta takai fuskarsa zata goge ya kauce fuskan sai hankalinta yayi mummunan tashi ta sakata tafin hannuwanta masu wani irin taushi ta Dora kan fuskarsa tahau gogewa arude jikinta na rawa Kuma har lokacin tana kan cinyarta.
Ahankali ya bude idanuwansa masu sake rudata ya zubawa hannayenta ya dauke Kai tareda sake kame fuskarsa ya dago hannayensa duka biyun zai janye jikinsa kamar daga sama muryar AFIA ta sauka da cewa"

What's going on here????

Kallon tsananin mamaki da tsoro tareda firgici da rudewa take musu musamman NURUn dake zaune kan cinyar dad din.

A zabure NURU ta miqe jikinta har Yana rawa ta kalli afia batasan lokacinda ta qaraso gabanta ba tana cewa"

Juice ne farhat ta turo ya zube.

Kota kansu baibiba ya miqe yabar gurin gabaki daya Yana zare agogon hannunsa daya jiqe shima.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899*_Mamuhgee 17_*

*_Turare by awwaba_*
*Assalamu alaikum warahmatullah,  shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu  a instagram *@turare_by_awwaba mungode*

****************
Washe gari tunda safe yasake dawowa gidan Dan ganawa da maleek Amma sbd rashin sa'a Koda yazo maleek din yafita haka ya juya jiki amace yakoma gida da niyar ya dawo anjima Dan Dole Dole tsakanin yau zuwa gobene damarsa ta qarshe ta ganawa da maleek sbd jibi Ana fara aikin Santiago Babu ranarda zai samu kansa harya samu damar magana dashi.

Ta bangaren NURU itama gabaki daya ta rasa sukuni da walwalarta akan zancen Dan ko abincin kirki tadaina ci kullum saidai tea sbd fargaba da tsoron abinda zai iya kaiwa ya komo
Duk yanda Afia tayi tayi da ita akan abinda yake faruwa takasa Mata bayani dataga kaman ran afian ya baci ne saita fada Mata da Imran nason turowane ita Kuma tana tsoron karatuntane kawai da haka afia ta zaunar da ita tabata wani qwarin gwiwan barin Imran din yayi zancen tahakane zataji idan abin me yiyuwa ne.
Hakan yasa tadan rage damuwar abin cikin ranta tafara jiran tsammani.

IMRAN kuwa Kai yayi mugun daukan zafi sbd duk wata hanyar dazai gana da maleek ta toshe har abin yafara bashi tsoro sai kawai ya yanke shawaran fadawa mahaifinsa Dan shi dakansa ya nema MALEEK din.

Zaune suke a dining suna dinner Kiran FORMER M.AMB JALALUDDEEN yashigo wayarsa yayiwa wayar kallo daya yaci gaba dacin abincinsa a natse harsaida yagama zuwa lokacin yayi Masa Kira kusan hudu sai Ana biyar din ya daga cikin kamewa da ikon sarauta dake yawo cikin jikinsa ya amsa sallamar M JALALUDDEEN suka gaisa a mutunce gaisuwa irinta dattijai manyan mutane kafin M JALALUDDEEN yafara da cewa"

MALEEK nayi kirane akan maganar aure da Imran yakeson yarinyar gurinka wadda yace sunriga sunfahimci juna sosai da ita to.....
Wata nutsatsiyar gyaran murya MALEEK yayi a natse wadda duk wanda yasan mulki da sarauta yasan dakatarwane ga zancen da ake Dan haka M JALALUDDEEN ya dakatar da abinda yake fada
Kai tsaye MALEEK cikin kamewar muryarsa me nuna isarsa yace"

Wannan maganar ba'ayin irinsa a waya.

Hakane tabbas Bata waya bace MALEEK to kabada lokacinda zamuzo sai ayi maganar akai qarshe Inshallah.

Kallon agogo yayi alamar zancen na shiga lokacinsa Dan haka Kai tsaye yace inada tafiya gizah agabana banida lokacin bayarwa idan nasamu time zangani Inshallah.

Daga haka sukai sallama Yana aje wayar AFIA dataji ya ambaci tafiya gizah hankalinta yayi mummunan tashi ta kallesa cikin son tabbatarwa tace"

Dad zakaje delah gizah??

Yana miqewa yace"

Eh Anneti tasamu attack na zuciya yau da safe.

Yana fadar hakan ya wuce gabaki daya.

Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na bugawa tana nanata zancen tafiyar.
Chapter 19 · 0% Book details