← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 66

Sashe 55

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wucewa tayi zuwa dakin dake gefen nata Wanda aka tsarashi da komai na yara domin farhat din tana shiga ta qaqalo murmushi tana kallon kallon farhat din data shirya cikin riga da wandon asalin yadin qasar na sarauta me kyau ta qaraso gurinta tana cewa"

Heyy sweetie you look more pretty.

Cikin Jin Dadi ta qaraso gurin NURUn tana fadawa jikinta suka juyo zuwa palo tana cewa"

Aunt jiya Ina Kika kwana Kika barni Ni kadai?

Siririn Murmushi NURU tayi tana kawar da zancen tareda Dan dagowa ta kalli inda afia data bari Palon tana fatar Bata jiyo zancen da farhat din tafada ba ta kamo hannun farhat din suka nufi gefen da dining yake ta miqawa Akira hannunta tana cewa"

Kije da ita taci abinci Ina zuwa.

Komawa bedroom dinta tayi tayi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar royal gown ash ta fito Akira dake jiran fitowarta ta gyara tsayuwa suka nufi sashen Anneti Dan sai yanzu tunanin zuwa Kai Mata gaisuwa ya shigeta musamman tasan tanacan cikin damuwar al'amarin itama tabar afia zaune agurin tana saqa da warwarar yanda zata tarbi al'amarin wa mahaifiyarta sbd ko kowa ya yadda da ita ta aikata hakan bazata taba yadda da mum dinta zata aikata hakan ba.

Koda aka sanarwa Anneti qarasowar NURU gurinta sai farin ciki ya shigeta taji ta Dan samu nutsuwa da saukin abindayake cin ranta ta fito daidai shigowan NURUn data qaraso har gabanta ta durqusa har qasa ta gaisheta cikin girmamawa
Da farin ciki Anneti ta dagota tareda nuna Mata gurin zama tana amsawa cikin kulawa tace"

NURU ya kike?
Kina lafiya dai ko?

Alhmdlh"tafada cikin nutsuwa tana Dan dagowa bayan sun gama gausawar tace"

Ashe abin daya faru kenan¿Allah ya kawo mafitar wannan al'amari tareda tsare gaba.

Ajiyar zuciya Anneti tasake tana gyara zama ahankali cikin bayyanarda 'yar damuwarta tace"

Allah ne kawai masanin wannan al'amarin Amma dai koma Yaya yake
Allah ya fitar da kowa yakawo mafita
Musamman shi maleek da abin yafaru a qarqashinsa Wanda yasa Yan jaridu keta fidda labarai marasa Dadi akai
bana fatan hakan yazamo matsala agaresa, ki kula dashi sosai kibashi kulawa Dan Yana cikin tsananin damuwa na tabbata.

Shiru NURU tayi dukkanin jikinta nayin sanyi da wannan sabon bayanin data samu.
Boyayyan numfashi ta sauke tanajin tsananin buqatar son ganinsa Dan Bata lurada cewa halinda yake ciki ba kenan tun jiyan da bazata baro gurinsa ba gashi yanzu batada ikon maida kanta batareda ya nemi ganintaba.

Miqewa tayi jiki Sanyaye ta fito Takoma tanajin danuwarsa na lullubeta tana shiga Kai tsaye daki ta wuce tafara tubewa ta saka Kaya marasa nauyi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta kwanta tareda lafewa kan gadon tanajin kaman zazzabi na neman shigarta.

Baccine yafara fizgarta cikin tunanin datai nisa daga sama sama taji Ana Kiran sunanta ta bude idanuwanta ahankali dasukai nauyi sbd kanta daya fara ciwo tuni, ta dishi dishi taga kaman jekadi take gani gabanta ta bude idanuwanta gabaki daya tana waresu akanta.
Jekadi data fahimci NURUn Bata gasgata ita bace saita Dan murmushi ahankali tana cewa"

Allah qarawa MUSHRAn maleek kyau da lafiyar bacci.

Da sauri ta tashi zaune har batasan lokacinda tafada jikin jekadin ba ta rungumeta da qarfi idanuwanta na cikowa da hawayen farin cikin ganinta da tausayinta tace"

Alhmdlh Masha Allah jekadi kindawo kindowo.

Farin cikine yakama jekadi ta zame tana kallon NURUn wadda Allah ne ya hada kauna tsakaninsu tun farko ta kalli idanuwanta dasuka ciko da hawaye tace"

Karkiyi kuka Allah zakiyiwa godia Allah yaqaro haske a rayuwarki kinji,share hawayen ki gyara fuskanki maleek ke buqatan ganinki tareda afia.

Sai alokacin ta tunoda lailah ta kalli jekadi cikin sanyi da tausayin afia dayake sake kameta tace"

Mum din afia fa??

Ajiyar zuciya jekadi tayi tareda dagowa a natse tace"

Tana hannun hukuma haryanzu sbd anyi bincike an tabbatar itace saidai haryanxu takasa tsayawa ta nutsu tayi bayaninda zai taimaketa.

Shiru sukayi dukkaninsu NURU na jajanta abin cikin ranta da yanda Afia zata dauki abin.

Ficewa jekadi tayi tana cewa tana jiranta a Palo itakuma ta nufi toilet ta wanko fuskarta ta fito ta Dan gyara ta sauya Kaya zuwa doguwar jallabiya maroon ta fito tana qamshin turaren _bosslady_ dayake fita ajikinta ahankali Bata saka sosaiba sbd kada taqarawa afia damuwa akan tata hakama Bata shafawa fuskarta komaiba duk sbd afia Dan batason saka Mata damuwar wani tunanin daban.

Data fito kallo daya jekadi Tai Mata tana karanto Mata adduoin tsari daga sharrin ido Dana Baki sbd ko Yaya NURUn tafito ita din kyanta me sanyi ne.
Afia kuwa Batada wani kwanciyar hankalinda zaisa tayiwa NURUn kallon tsaf itama dai tayi kokari ta shirya kanta suka fito jekadi na gaba suna baya sai su Akira dake take nasu bayan har zuwa bakin sashenshi kowa ya dakata daganan daga jekadi saisu suka qarasa ciki a palo na biyu suka taddashi zaune Yana sauraren bayaninda mr Omar keyi Masa hankali kwance Yana sanye cikin wani coffee brown kaftan dasuka fiddo da qyallin da fatarsa keyi kwarjininsa yana sake bayyana tareda cika idon me kallonsa
Yana Jin shigowarsu Bai waiwayoba saima takardun daya bude Yana karantawa na sakin jekadi da akai a yau din
Mr Omar kuwa sauya bayanin dayakeyi yayi da kallon gefensu NURU da cewa"

Barka da shigowa.

Da Kai NURU ta amsa Masa ahankali tana satar kallon gefen maleek din kadan Wanda Bai nuna ya San da shigowar tasu ba
Afia kuwa Batada karfin amsa Masa
Zama sukayi kafin ya dago ahankali ya zubawa NURU idanuwansa dasuka sata saurin cafko numfashinta daya tashi barin jikinta sbd kallon tajisa ajikinta sosai, ta dago fuska ahankali ta kallesa ya juyarda kallonsa kan Afia tausayin 'yar tasa na kaunarta na sake shigarsa sbd yanason 'yayansa fiyeda yanda ake gani
Ya bude Baki Kai tsaye cikin kulawa da kamewa yace"

Afia maleek yaya?kina lafiya dai ko?

Shiru tayi Idanuwanta nason cikowa da hawaye ta dago ta kallesa tana hango kulawa da kaunarta gurin dad din nata sai hawayenta suka gangaro ta girgiza Masa Kai ahankali tana cewa"

Bana cikin nutsuwa dad.

Dan gyara zama yayi Yana ajiye takardun hannunsa ya sake kame muryarsa yace"

Mum dinki itace damuwarki right?

Gyada Kai tayi tana sauke Kai kalar tausayi.

Afia idan kinmin alqawarin Zaki kwantarda hankalinki ki nutsu kodan karatunki da bawa Taki rayuwar mahimmanci ki daina biyewa tunani irin na mum dinki then namiki alqawarin Babu abinda zai samu mum dinki zata fita cikin case dinnan lafiya Amma Zaki Bata shawaran ta tafi ta inganta rayuwarta ta wani hanyar kin saurari abinda nake fada right??

Dagowa tayi ta kallesa da hawayen dake gudu akan fuskarta ta gyada Kai tana cewa"

Yes Dad namaka alqawari Inshallah dagani har ita zamu cika wannan alqawarin.

Daukan takardun gabansa yayi ya bude tareda karban biro a hannun Mr Omar yasaka hannu cikin takardun tareda rufewa ya miqawa Mr Omar yace"

Ka sameta tabaka sunan lawyernta shine zai qarasa aikin yakai takardun can zasu saketa kada abari 'yan media su sani ko kadan infact dagacan a haura da ita tabar qasar gabaki daya.

Da sauri afia ta qaraso gabansa tana Masa godiya cikin tsananin farin ciki tace"

Imran ne lawyern mum zankirasa zaizo ayau Inshallah dad.

Sunan Imran data ambata yasa NURU kallon afian ta sauke kanta.

Fita afia NURUn ma ta miqe zatabi bayanta jekadi zata dakatar da ita maleek yayi Mata kallon ta barta ta wuce.

Bayan fitarsu ya kalli Mr Omar yace"

Ayi Mata takardun ganin likitan tabin hankali kada a taba barin afia tasan mum din Tata tasamu tabin hankali sbd shock din wannan al'amarin
a fitar da ita abar Mata gidan Vegas tazauna can taringa ganin likita akai akai har Allah ya yaye Mata
Afia Kuma iyakacinta da ita airport.

Allah yaqarawa maleek tausayi da adalci.

Sai maganar Dan jaridar daya fara wallafa cewan 'yar uwar.....'dan shiru yayi Wanda yasa Mr Omar da jekadi kallon juna suna Dan murmushin dasu kadai sukasan ma'anarsa
Mr Omar ya karbi zancen da cewa'

Za'a shigarda bayyananniyar qarar shariar sama akan Wanda yafara wallafa labarin ankashe 'yar uwar mushrah sbd haryanxu bayan mu da hukumar dake hannunka babu Wanda yaga asalin gawar ta Yaya yasan wacece aka kashe hadda alaqarta da mushrah,
Dan Haka inda bayanin yafara fitowa zai fada.

Ahankali maleek ya gyada Masa Kai Yana cewa"

Daga gobe kada abarsu fitowa kowa ta zauna a sashenta a tsananta tsaro a hanyoyin bangaroransu sbd komai zai iya faruwa idan aka fallasa zancen qarar Dan jaridar sbd kada asan inda yasamu zancen.

Juyawa sukai suka fice suka bar sashen nasa sbd wayar dazai fara da kaleeb.

Sbd tsaro Koda afia Takoma sashenta doka aka bayar kadata sake fitowa sai gobe Dan Haka ita Bata damuba take tasaka aka kawo Mata sabuwar waya dayake tana tareda layinta na qasar saita Sanya ta nemi numbern Imran.

Cikin tsananin damuwar halinda suka samu labarin abindaya faru cikin tsananin damuwa yake tambayar afian Yaya case din ke tafiya sbd case ne na masarauta babu me halin Shiga danma sunyi mamakin da hukuma tashiga zancen Dan masarauta irin delah gizah sune suke hukuncin komai daya shafesu da kansu Amma Kuma ace MALEEK dakansa ya bawa hukuma damar shigowa ciki duk da hukumarma tasace sai abinda yace suke amfani dashi.

Cikin nutsuwa afia tace"

Ni yanxu duk wannan bana tunaninsa yanxu sbd ya amince zai sa asaki mum a sirrance tabar qasar Dan Haka kana buqatan isowa cikin gaggawa gobe ka isarda takardun abaka ita ku tafi
Dan Allah kamun alqawarin zaka kularmin da ita sbd nasan yanzu tana cikin tsananin hali na tashin hankali.

Dan shiru yayi Yana cewa"

Bazai yiyi nazo gobe ba sbd Kar takardun nikadai lawyer bazan iya zuwaba Dole sai munje tareda wani lawyern Wanda zai duba takardun dazanje dasu agurin dama wannan Dole 2 lawyers ne suke zuwa Dan Haka Ina buqatan time Zan nemo wani lawyer din Wanda zai bamu time dinsa yazo taredani.

Shiru afia tayi cikin tsoro da tashin hankali tace"

Baza'a iya jiraba damace dad yabawa mum Dan Allah kazo kawai an zamu samu wani lawyer din.....

Shiru tayi cikeda nazarin abin data tuno na cewan NURU ma lawyernce
Wani sanyi ya lullubeta ta maida wayar kunnenta tana cewa"
Chapter 55 · 0% Book details