← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 66

Sashe 32

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon tsaf jekadi Tai Mata kafin tayiwa abincin da aka kawo din ta tako ahankali tana kallon abincin takai hannu ta bude tayi Masa kallon tsaf tareda Dan Kai hannunta a kaikaice taji dumin abincin Wanda baida dumi ko kadan ta dago ta kalli padiman kallon tsaf tasaki wani murmushin bazata dayasa padiman Dan washe Baki itama tace"

Saida safe ki huta lafiya"" ta juya ta fice batareda yiwa padima sauyiba ko alamar komai.

Tana fita padima ta sauke ajiyar zuciya tareda warware gashinta tasake gyarawa kullin zama cikin yalwataccen gashinta.
Ta zaro uwar dukiyar data boye tana tunanin inda zata kaita kafin tadawo.

Zagaye tafara cikin tsananin tsoro da firgici Dan ganinta da wannan darhaman masu tarin yawa zasu iya kaita lahira, gabaki daya tsoro da tashin hankali takeji wace masifar ce wannan daga zuwanta ko Paris din Bata qetaraba ta hadu da wannan balain yanxu idan taqi Yi ance abakin ranta,
Idan tafadawa wanima abakin ranta,hakama idantace zata tona tafada gskia batasan waye ya aikoba Dan aikenma fuskarsa rabi arufe babbar masifar datafisu shine idan ta aikata tayi kisan Kai ga Wanda tasan ko gunduwa gunduwan gawarta Kare suka samuci tayi arziki to ita Kam wane tashin hankali ne wannan.
Tana hada wani mugun zufa ta dauresu waje daya tareda cusawa cikin kayanta na sawa takoma gefe ta zauna har lokacin gumi take hadawa ta Nemo numbern amed sbd sanin shikadaine abokin cin mushenta na rayuwa.

Yana ganin kiranta yasaki ajiyar zuciya sbd abinda yake jira kenan Dan mahaifinsa ya fada Masa komai Dan shine yaje gurin padiman.
Dauka yayi cikin matsewa sbd har lokacin takaice yake da ita yace"

Lafiya dai ko Kira da wannan tsohon daren.

Wani wahalallen numfashi tasaki cikin qasa da murya tace"

Amed inason ganinka a Giza komai tsanani gobe Dan Allah.

Kallon mahaifinsa yayi sbd tun Rana ya iso Giza din yau shima sbd wannan tarkon nasu ya Dan sake Bata murya yace"

Sbd me zanzo kiranki?
Kinga karki rainamun da hankali Mana.

Cikin rawar murya tace"

Dan Allah amed kazo kokuma idan bazaka samu zuwa ba ka hadani da mahaifinka wlh Ina cikin wani mummunan tashin hankali ne na..... shiru tayi tana tuno maganar da Dan Aiken yafada Mata dazu hawayen cikin idonta suka gangaro Mata ta sauya zancen da cewa"

Akwai dukiyar NURU ce a hannuna inason baka ka Adana min harna dawo sbd bazan bataba batamasan da itaba.

Washe Baki yayi Kai tsaye Yana cewa"

Ganinan tafe yanzu kuwa.

Da mamaki tace" yanxu Kuma?
Kana gizah ne dama?

Da sauri yahau gyaran zancen da cewa"

Aa inanufin zan fadawa mahaifina zaishigo ya karba ta sirrance.

Bata yadda dashiba Dan taji gargada a zancensa Amma yanxu tunda tanason kubuta daga wannan saita ciro maganin da aka Bata ta Raba biyu ta bude gaban wata sarqar daham dake cikinsu tasaka dayake qaramine saiya shige ta maida Dan locket din ta rufe tana cewa"

Idan ta 'batarmin acan tareda zamuje qasa Dan ga shaida nan nasaka acikin kayan Kuma bazaka taba ganowaba.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899*_Mamuhgee 26_*
Washe gari sakayau taji ta Dan rage tashin hankalinta sbd ta rabu da dukiyar Dan hakanan taji Kamar jakadi Bata yarda da itaba ita yanxu data tabbatarda mutuwa ba abin Wasa bace data ji tafara Jin kamshinta zuwanta gizah sbd jiya harzuwama yanxu cikin matsanancin tashin hankali takejin kanta gabaki daya kusan Rabin zumudin tafiyar yabarta tsoro da shakkun abinda zai iya faruwa gaba shine yafi komai cikata yanxu gefe daya gasu abal tana Isa sukaji wani abun yafaru ayanda tasan abal dinsu dakansa zai iya bada shedar kome yafaru itace...

Gyaran muryan jekadi ya dawo da ita zurfin tunanin data shiga ta dago ta kalleta jiki duk amace ta Dan rusuna ta gaidata
Jekadi ta amsa cikin sakewa tace"

Bismillah zamu wuce Inshallah.

Janyo Jakarta tayi suka fito daganan har sassan Anneti aka fara kaita ta gaidata cikin tsananin girmamawa da tsarguwa kafin suka fito bayan sun Isa gate na biyu Dana uku Saida aka bincike kayanta tsaf kafin suka fito main gate inda dakarun tsaro suke sunfi guda ashirin suka fice daga delah gizah zuwa airport manyan motocin tsaro biyu na bayansu har airport.

********
Yau tunda safe suka fice duk su dukansu sbd exams dasuka fara ayau din ga uwa uba ita NURU tana gama da ciwon Mara sama sama dam idan zatayi period kusan kowane wata saitayi ciwon Mara ga uwa uba Imran da kwanakin Nan tunaninsa yakasa barinta Jin cewar bayada lafiya sosai
Tausayinsa takeji har cikin zuciyarta saidai tasan matuqar ba afiace zataje ganinsaba tabita itadashi iyakaci addua.

Suna fitowa yau sbd sammako dasukayi cikin itace agaba tana gyara daurin kanta na scarf fari shikuma Yana fitowa daga geamin dinsa wasu qananun zufa dasuka fiffito Masa suna gangara daga fatarsa da tsantsinta ya hanasu zama ta dago ta kallesa wata irin mummunan kunya ta kamata tayi sauri dauke Kai kasa batasan lokacinda tace"

Gud morning ba.

Kallo daya tayi Mata daga sama zuwa qasa ta dauke kansa ya wuce Kamar bai lura dasuba afia dayake tasan halin dad dinta saitayi gaba sbd sanin jinin mulkin ya motsa akansu su 'yayansa.

NURU ma hakanan tabi bayan afia tana kashe wayarta suka fada mota suka wuce.

Sai yamma lis suka dawo Kai tsaye daki suka nufa kowa yayi wanka ko abincin kirki NURU bataciba sallah kawai tayi ta janyo laptop tareda wasu takardun tahau karatu afia ma libry ta wuce Dan ita tafi ganewa karatu acan.

Daqyar kowaccensu tayi sallar ishai sbd bacci da gajiya suka Dan sake tattaba karatun bacci yayi gaba da kowaccensu a inda take.

Sai cikin tsakiyar dare su padima suka iso Dan haka ko cikin main gidan ba'a Bari sunshigo ba sbd MALEEK na Nan Dan haka part din masu aiki suka sauka akan seda safe zasu Shiga cikin gidan.
Tunda safe sukuma su NURU suka wuce school sbd jiya bacci be barsu sunyi karatunba sosai shiyasa Koda safe dasu padima suka samu shigowa su NURU sun wuce aka sauketa dakin dake kusadana mum Sarah na jekadi ma Yana gefen nata saiya zama sun sanya dakinta tsakiya.

Kallon aljannar duniya takeyi hawaye na silalo Mata a fili tace"

Wannan wane irin masiface take bibiyata,
Amed Kaine ka cutatarda rayuwata wannan rabon ya subuce min.
Kallon dakin da aka sauketa tayi Wanda aka Kira Dana saukan baqi Wanda tasan har abada kila ko a mafarki bazata samu irinsa ba matuqar ba aikin da aka Bata tayiba dasukai Mata alqawarin cikar buri.

Shafa kanta tayi taji maganin na ciki ta sauke ajiyar zuciya tana bawa kanta qwarin gwiwan aikatawa.
Da wannan tunanin tayini tana kallon kanta a madubi sbd ko tsaron dake Nan gidan ba qarami bane tsaf zatayi ta bakin ranta ba duniyar ba lahirar Dan haka Dole Saida taka tsantsan.

Da yamma suna dawowa farhat tafara tarbonsu da gudunta tayi musu oyoyo tana sanardasu isowansu padima Wanda yasa NURU sakin wani qayataccen murmushi tana 'dan wartsakewa daga gajiyarta taqarasa ciki cikin farin ciki.

Jekadi ce tafara fitowa ta russuna cikin girmamawa tace"

Barka da dawowa ikon MALEEK na gizah.

Da murmushi ta matso tareda girmamawa itama tace"

Allah yaqarawa jekadi matsayi
Kun iso lafiya?
Ya kuka baro Anneti.

Murmushin ganinta cikin sabon sauyi jekadi tayi sbd lurada Kamar taqara Dan sakewa fiyeda da tace"

Anneti na miqo gaisuwarta gareki da sauran iyalan MALEEK gabaki daya.

Muna amsawa tace tana kallon kofar da padima ta fito fes hartayi wanka ta Sanya doguwar riga me Fadi sosai ta qarasa da Dan sauri suka rungume juna suna yare tana tambayarta su abal da ammi da meryam.

Duk suna lafiya ta amsa tana yiwa afia barka da dawowa cikin 'yar girmamawa.

Tareda padiman suka qarasa dakinsu sunata yare Wanda yasa afia keta Binsu da murmushin burgeta dasukai musamman NURU daketa nuna kulawa ga 'yar uwarta saitaji NURUn na sake Shiga ranta tace"

Baby am jealous fa.

Murmushi NURU tayi tana cewa"

Karki damu itafa tafiya zatayi tabar Miki NURU.

Padima da batasan me sukace ba farko sai Binsu take da ido kishinsu na sake ciketa musamman NURU da idan ta tuni asalinta.

Wanka sukai kowa ya shirya cikin qananun Kayan Shan iska suka baje karatu suna fira da padiman at the same time.

Har dare tana dakin suna first gida Dana ciwonta Wanda take ce musu ba laifi tanajin kaman tafara Jin sauki sbd wani magani da abal yabata.

Sai dare sosai NURU ta rakata har cikin dakinta suka zauna suna dasa sabuwar zancen gida Wanda duk yasake tadowa NURU kewar gida da iyayenta ita kuwa padima satar kallon tsadaddun kayan baccin dake jikinta takeyi Wanda itama anhadota da daya na sawar yau Amma saitakega kaman na NURUn sunfi kyau da tsada Wanda batasan cewa daga jikin NURUn ne.

Sai after 12 tafito daga dakin Takoma nasu ta kwanta tanajin farin cikin saduwa da 'yar uwarta.

Washe gari ma sammako sukayi sai yamma Amma ba sosaiba suka dawo zuwa lokacin farhat tadan fara sabawa da padima dake kokarin zama kamar yarinya itama tana Taya farhat din Wasa itadai jekadi idanuwanta na bude qyam akan komai dake wakana a gidan.

Kwata kwata su NURU basa zama sbd exams shiyasa Basu ma dauko maganar ciwon padima ba Bari sukai saisun Gama exams sunsamu lokacin kansu isashe tukuna itama padima Bata damuba Dan so take kadama su Gama exams din da wuri Dan kada a tado maganar tasamu ta aikata aikinta ta tattara Takoma Dan ita anan ko gurin zama Bata ganiba dan haryau datake batun cike sati biyu da zuwa Bata taba saka maleek a idontaba Dan haka gwara tayi wannan aikin Takoma can Giza kila nata rabon acan yake tunda anmata alqawari.
Chapter 32 · 0% Book details