← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 66

Sashe 36

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa'a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace"

Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?

Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace"

Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.

Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace"

Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al'amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.

Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.

Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899*_Mamuhgee 29_*

_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _*08095215215/09044191709*! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_

**********
Harta Gama zuba Masa ta ajiye Bai Bai Kuma waiwayowa ba amfani yake da wayarsa sai farhat dayake tankawa ahankali,
Juyawa tayi zata fice batareda ya kalla inda take ba yace"

Kijira ki tafi da kayan.

Dakatawa tayi tareda sauke ajiyar zuciya boyayya sbd atlas dai yanuna yasan da shigowar mutum ba farhat kadaiba.
Juyowa tayi ahankali tadawo daga gefe ta tsaya tana Dora kallonta kan tv dake aiki Sam bama murya kusan gabaki daya Wanda ta fahimci qaidar iya muryar tv dayake buqatane ahakan.

Ganin tsayuwar Kamar zata damesa saita sulale ahankali Takoma palonsa na farko ta zauna tana kallon tsari da haduwar palon Wanda kusan komai na palon milk ne.

Juya idanuwanta tayi kan wani qaramin hoton LAILAH dake cikin qaramin milk frame tana tareda maleek din dukkaninsu cikin qananun Kaya black shi Yana zaune gabaki daya hankalinsa nakan wayar dake hannunsa itakuma ta rungumosa tana dariya fararen haqoranta tas a bayyane sunyi kyau.

Dokawa taji qirjinta yayi ta dauke kanta daga kallon hoton tareda Dan hadiye yawu tana qoqarin Wasa da yatsun hannunta.

Kasawa tayi tasake juyowa gabaki daya ta qurawa hoton ido tana qarewa LAILAH kallo.
Kyakkyawace da kyanta yake a bayyane,gata da kyawun jiki Kamar ba ita ta haifi afia ba Kamar dai yayarta,
Wayewarta ko acikin hoton a bayyane take sbd yanayin shigarta da yanda take nanuke ajikin MALEEK Wanda son datake Masa yake bayyane afili shima alamunsa da yanda hankalinsa ke kwance qarara a hoton ya bayyanarda soyayyarsa ga matarsa.

Sake dauke kallonta tayi daga hoton jikinta nayin sanyi bugun zuciyarta na qaruwa ta waiwaya gefenda kofar dakin lailah din saitaji jikinta na Gaza Mata ta miqe tabar gurin ta koma cikin palonsa wannan karon sallamarta daqyar ta fito qasan maqoshi sbd shaqewar dataji maqoshinta yayi.

Qarasowa tayi kanta a qasa ta dauki tray din ta fice batareda tabi takan farhat ba dasukazo tareba.
Tana saukowa kitchen takai kayan ta wanke da kanta ta maidasu gurinsu ta fito ta nufi daki batareda Takoma gurin padima ba.

Tana zuwa daki ta fada kan gado takwanta tareda rufe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciyarda batasan Kota mececeba.

Har dare Bata sake fitowa daki ba Koda padima tazo ta tambayeta ce Mata kawai tayi kanta na ciwo hutu take buqata.
Padima Bata damu da hutun da NURUn tace tana buqataba ta zauna gefenta tareda kallonta Kai tsaye tace"

NURU inason zankoma gida Kuma cikin gaggawa sbd kwana biyun Nan inata mafarkai marasa Dadi na abal da ammi kaman dai da akwai babbar matsala Dan haka Ni inaga zankoma gurinsa kada ya zamto babuke akusa Babu Ni.

Tashi zaune NURU tayi tana kallonta da yanayi na damuwa tace"

Amma ai nayi waya da abal ko dazu Kuma banji alaman matsala ko wani damuwaba bayan haka meye amfanin zuwanki kema idan Baki ga likita ba akan Taki lafiyan.

Yamutsa fuska tayi tana cewa"

Kibar maganar nawa ciwon sbd bana tunanin zan tsaya ganin likita naji sauqinsa sosai Dan dama kila hadda damuwar rashinki akusa ne yasa abin yayi tsanani yanzu Dana zauna dake naji saukin komaima kawai damuwata anan iyayenmu ne kiyi tunani kema kinsan Koda damuwa abal bazai taba Bari kiganeba barema Koda na baro fa bayajin Dadi kwana biyu Yana fama da ciwon tari...

Da wata sabuwar damuwar NURU ta kalleta tana cewa"

Amma meyasa tun zuwanki Baki fadamun abal bayajin dadiba padima?

Kinga shine ya gargadeni akan kada na fada Miki Kuma ko yanzu kada kiyi Masa maganar Dan zaisan cewa nafada Miki
Nidai gida zankoma jibi kiyi Shirin duk abinda Zaki bani da Wanda Zaki karbomin daga MALEEK,
Ni bana wannan ba NURU meyesa nakeganin kaman ba zaman aureba kike a gidan nan??
Dan Babu wani alamari daya danganci aure danaga Yana faruwa dake.

Shiru NURU tayi tareda dagowa ta kalli padiman tsawon mintuna sbd batasan me zataceba tunda kusan gaskia padiman tafada, ta sauke numfashi tareda Miqewa tana cewa"

Kidaina wannan tambayar padima
Ba lallai komai ake bayyanawaba
Tunda dai akwai auren komaima ahankali za'ayi.

Miqewa padiman itama tayi tana cewa"

To dai iyayenki saisu daina dukan gaban 'yar so tana auren MALEEK na delah gizah Dan kar ayi zaton wuta a maqera ajita a masaqa.

Juyowa NURU tayi ta kalli padiman da manyan idanuwanta ta matso daf da ita harsuna shaqan juna tace"

Ko a kasuwa za'a jita ba ruwanki bane ki Kama bakinki kadaki fadawa su abal abinda zaisasu damuwa sbd padima ba ruwanki da abinda zai kawo musu bacin Rai ko damuwa.

Murmushi padima tasaki cikin isashiyar muryarta tace"

Kiji da matsalar gabanki ta zaman aikin gida da renon mijin wata Ni kibarni zanji dasu abal din naki idanma labarin yakaimusu wata Rana Dan yanxu banjin zanyi lokacin isar musu da wannan labarin inada nawa sabgogin kawai dai kishirya min komai nafada Miki gida zankoma.

Wucewa tayi ta fice daga dakin tabar NURU nabinta da kallon takaici takaici sbd halin padima dai haka yake tun suna yara saidai kwana biyun Nan datazo musu tayi tunanin tafara sauyawane shiyasa taketa kiyayewa sbd kada suyi halinsu agabansu afia subarwa kansu abin takaici.

Zaunawa tayi kan kujera tana furzar da numfashi tace"

Zanyiwa jekadi magana ta maidaki tun kafin mufara halin acikin gidan Nan tunda kinji kingani kinfasa neman lafiyar ai shikenan kije ko Dan lafiyar iyayenmu.

Da daddare har daki tasamu jekadi zata zauna jekadi tayi saurin miqewa tana cewa"

Ba girmanki bane mushrah idan kinason ganinane duk inda kike zan sameki naji bayaninki ko umarninki.

Murmushin yaqe kawai tayi sbd duk ranta a jagule yake yau din daga wannan sai wannan.

Daga tsayen ta kalli jekadi da taushin murya da zallar gajiya da damuwar komai tace"

Jekadi padima zata koma gida jibi nafadawa Mr Omar yayi muku komai na tafiyar,
Idan kunje kibata wadataccen kaso acikin wainnan dukiyar dake can na dukiyar auren......kasa karasawa tayi sbd Jin nauyin fadar kalmar aurenta
Itakuma jekadi Jin tayi shiru tace"

Yanda kikace haka za'ayi Inshallah"sbd ta fahimci abinda take fada.

Gobe ku shirya saimu fita akaiku kuyi siyayyar abinda kuke buqata.

Godiya jekadi keyi Allah yaqaro girma da kusanci tsakainki da MALEEK tareda tabbaciyar qauna.

Shiru tayi batareda tace komaiba saima sanyi da jikinta yayi ta juya zata fice jekadi tadago takalleta cikin tausayi da kaunarta saitaji bazata iyaba ta gyara tsayuwa tareda aje matsayinta na jekadi takira sunan NURUn cikin tsananin kulawa kaman yanda ta Saba a da.

Tsayawa NURUn tayi tareda waiwayowa ta juyo gaba daya damuwarta na raguwa sbd tasan jekadinta ta Da ce kafin tazama Matar maleek.

Takowa jekadi tayi tazo har gabanta takamo hannunta tajata zuwan kan kujera ta zaunar da ita kafin itama ta zauna ta fuskanceta cikin kulawa a natse tafara cewa"
Chapter 36 · 0% Book details