← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 66

Sashe 20

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa yadda da tafiyar dad dinta zuciyarta tayi dari bisa dari sbd zuwansa zai iya kawo komai na lalacewan faranta da adduar datai shekaru tanayi na ganin dawowar iyayenta tare,
Shin Tata dad zaije delah gizah yanzu bayan zuwansa batareda matarsaba zai bayyanawa duniya cewan sun rabu Wanda hakan daidai yakeda rasa qimarsa da darajarsa hakama Kuma hakan zai jawo kokuma bada damar shigowar wata cikin rayuwar mahaifinsu ko Mata ko negestati.

Dafe kanta dake neman tarwatsewa sbd tsananin tarin damuwa data sawa kanta akan wani irin zazzafan kishi datake jiwa mahaifiyarta Dan haka bazata iya Bari dad yayi tafiyar Nan gizah ba sbd sanin tsananin qarfin iko da dokoki tareda al'adun mulkin irin na delah gizah.

NURU dake cikin Tata damuwar me nauyi tana zaune gefen AFIA din taji yanda takeda sauke ajiyar zuciya alaman Bata cikin kwanciyar hankali ko daya ta bude Baki ahankali cikin kulawa tace"

AFIA kinada damuwan wani abune?kimata sauke ajiyan zuciya.

Kasa waiwayowa tayi takalli NURUn sbd idanuwanta dasukai zuru zuru sbd masifar data sakawa ranta ta kishin mahaifinta ga wata mace
Batareda ta juyoba tace"

Bakomai kawai kaina na ciwo ne shima inaga sbd rashin bacci ne da bansamu nayiba jiyan.

Kafin NURU tayi magana ta miqe ta nufi toilet tashige ta rufo qofa.
Hawaye takeson Yi Amma ta daure tana kallon fuskarta cikin mirror ta rintse ido tana Jin shin mum dinta ta cancanci wannan fadan datake tare Mata kuwa?
Shin idan ta dage ta Hana dad dinta rayuwa da wata mace akan Taya mum dinta kishi tayi adalci a tsakaninsu kuwa bayan mum din itace ta lalata komai tayi watsi dasu ta tafi neman duniya wadda idan ba Allah yasoba har abada bazata samu duniya irinta dad dinsu ba.

Share hawayenta tayi tareda wanke fuskarta ta dauro alwalar azahar datai ta fito tana qoqarin sakewa Dan kawarda tambayoyin NURU akanta.

NURU dake binta da ido ganin babu damuwar komai a kan fuskan AFIA din sai tabar tamabayarta tana sauke numfashi Dan harta fara shiga tunanin kodai maganartane da Imran tazama matsala tunda tasanma kila zuwa yanzu yagama fadawa MALEEK komai.

Farhat ce tashigo daukeda littafi a hannunta tayo gurin NURU ta zauna kan cinyarta tana cewa"

Lewa nakasa gama wannan dubamin kigani.

Sallah Afia ta tayar tana dauke tunaninta daga kansu sbd Sam Babu Wanda zai gane abinda takeji.

Tana idar da sallar tadawo cikinsu suka cigaba da abinda sukeyi da ita Dan tasamu ta fitarda tunani da damuwardake azalzalar ranta.

Har dare tana sintirin yawo tsakanin Palo da 'dakinsu akai akai sbd tanason ganin dad dinta akan ko tafiyarsa delah gizah na Nan.

Har suka kwanta Bata samu ganin dad dinba sbd bai dawoba koya dawo ya wuce sama ya shige Bata saniba gashi tana Kiran Mr Omar Amma wayan Bata shiga haka ta hakura ta kwanta badan taso ba.

Washe gari da safe daga NURU har Farhat sun wuce makaranta ita kadaice Bata tafiba sbd ta sakawa ranta zata zauna harsai tasamu yin magana da dad dinta.

Guraren 11 na safe kuwa saigashi ya sauko qamshinsa na gauraya palon ahankali ahankali sai kyakkyawar fuskarsa dake kame kamar koyaushe
Tai Masa kallon qaunarsa amatsayinsa na mahaifinta datake tsananin kauna da alfahari dashi ta miqe tsaye tana aje laptop din dake kan cinyarta tana amfani da ita ta saki wani siririn murmushi tana qarasawa gurinsa tace"

Good morning dad,barka da fitowa.

Kallon kyakkyawar fuskarta dake yanayi da tasa yayi Yana alfahari da ita sbd juriyarta da iliminta tareda hakurinta ya bude Baki da muryarsa me amon iko yace"

Morning li'iliti(princess)

Murmushi tasake saki tana kallon dining din dayake qoqarin zama tace"

Dad can I join you?

Batareda ya dagoba yace"

Sure princess.

Janyo kujeran dining din tayi ta zauna tana cewa" thank you abal.

Tsit gurin ya dauka suna cin abinci Babu me mgnar sai ita dake cin abincin ahankali sbd son fara kawo zancen tagaji da wasi wasin yin zancen ko kartayi kawai saita kasa dannewan ta aje spoon din hannunta a natse ta kallesa da taushin murya tace"

Dad Yaya jikin Anneti(sarauniyar mahaifiya/mahaifiyarsa)
Zaka tafi tafi gizah kenan dad?

Dan kallonta yayi tareda sassauta fuskarsa ya gyada Mata Kai.

Sake gyara zama tayi cikin tausasa harshenta da bayyanarda damuwar data Dade da dannewa cikin ranta da biyayyarta ga dad din nata tace"

Dad maganarku da mum zai fito fili idan kaje....shiru ta Dan Yi tana kallon kamewar fuskarsa ta daure taci gaba da cewa"
Idan zancen ya bayyana cewan mum ta tafiyarta tabar...... kallo daya yayi Mata da fararen idanuwansa takasa qarasa sauran zancen ta marairaice fuska tace"

Dad please ko zaka duba kagani kodan sunan mum da naka dazai iya baci.

Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa tsaye ya kalleta yace"

Take care princess"ya wuce.

Kasa motsawa tayi kanta na toshewa sbd hakan na nufi zancenta be karbu ba agurin dad dinta sbd hakan da yayi shine rashin amintarsa ga zance idan ankawo Masa.
Miqewa itama tayi tabar gurin Takoma daki ta zauna ta jawo waya ta Nemo numbern mum dinta tafara tunanin takira ko karta Kira,
Fasa Kira tayi tai wurgi da wayar tareda Miqewa tsaye ta sauya Kaya ta fito tashiga mota ta fice daga gidan Dan zuwa dauko NURU datasan yanzu ta Isa gamawa tunda ita yau Bata samu zuwaba.

Tunda suka dawo taketa qoqarin cire damuwarta sbd kada NURU tagane saidai NURUn tana lure da ita saidai batason takura Mata da tambaya sbd batasaniba ko matsalar ta sirrice.

Kwana sukayi ahaka suka Kuma yini ahakan har akai kwana biyu
cikin kwana biyun duk ta Hana kanta sukuni da tunanin al'amarin Wanda take ganin rushewa familynta zaiyi idan wata tashigo cikinsu amatsayin matar dad dinsu ko negestati
Itadaima tafi son iyayenta su shirya koma menene hakan yafi shigowar wata cikinsu.

Ganin dai dagaske AFIA na cikin damuwa me qarfi boye kawai take yasa NURU kallonta bayan sun kwanta tace"

Afia koma menene abindake damunki please ki rage idan bazaki iya ciresaba ko hakura dashiba sbd wannan damuwan naki bamajin dadin ganinki ahaka ko farhat dake qaraman yarinya tafara cewa menene akaiwa AFIA.
Please AFIA kicire koma menene kibarwa Allah a rayuwa dama akwai hakan duk da nasan ke koma menene damuwan ba wani babba bane sbd Babu wani abu najin dadin duniya da Kika rasa Dan Allah ki cire damuwan please baby.

Tunda tafara magana afia ke kallonta sbd wani tunani daya shigota na sha'awar bin dad dinsu gizah Dan koma menene tafison tanacan zatafi samun saukin hanawa kokuma handling maganar rabuwar iyayenta taqi barin ta fita Dan kuwa tasan daga lokacinda maganar ta fita MALEEK na gizah bazai qara awa ashirin da huduba Batareda Matar aure ko negestati ba Dan haka zasu bishi Dan toshe yiyuwar hakan Dan kuwa idan hakan tafaru dad dinta bazai karbi mum dintaba har abada Wanda ita Kuma akan hakan ko kamawa tayi tayi amfani da NURU zatayi Dan Hana wata shigowa rayuwar dad din daidai NURU tayi hkr but she'll have to use her innocence.
Wani numfashi mara karfi ta saki tareda kallon NURUn cikin kauna da kulawa ta riqo hannunta ta rungume tace"
Thank you my NURU" ta rufe idanuwanta ahankali bacci na daukanta.

Washe gari haka ta tashi cikin walwalarta da sakewarta har hakan yasanya NURU da farhat farin ciki sosai har wasan ruwa da basketball sukai yau da yamma a playground Wanda duk abinda sukeyi dad dinsu na gidan dan haka Koda daddare yau taredashi sukai dinner Banda NURU dataqi fitowa tea kawaima Tasha sbd karatun data duqufa dayi Dan gobe tanada zuwa wani court yin wani aikin 4hours dake cikin karatunta.

Acan dining kuwa AFIA ta sanarwa dad dinta sunason binsa Dan Suma su dubo Anneti.

Kallonta yayi kadan tareda maida kallonsa kan farhat dake cewa"

Yes daddy Nima zanje Kuma zamuje da Aunt NURU ma ko AFIA?

Kallon bakin farhat din dako yaushe yake furta sunan NURU ko lewa yayi tareda dauke Kai Yana goge bakinsa yace su zama ready jibi ne tafiyar.

Cikin murna dukkaninsu sukace thank you dad.

Bayan fitarsa NURU tafara wucewa court kafin afia ita Farhat yau Babu zuwa school dinsu.

Sai yamma sosai suka dawo duk su dukansu Koda ta shigo tana waya da Imran da duk yabi ya sukurkurce Mata da cewan amatse yake da MALEEK yabawa su dad dinsa lokacin zuwa.

Murmushi kawai tayi sbd Bata taba tunanin maleek daya Bata ingantacciyar rayuwa tareda 'yayansa zai Bata ingantacciyar rayuwa ta har abada ba ta hanyar bada damar azo neman aurenta Dan tunda haryace idan yadawo zai Basu Daman zuwa ayi magana kenan da yiyuwar barinta tayi aure da rayuwar aure kaman kowaba babban mamakinta data kasa yadda dashi shine yau itace tasamu damar ace MALEEK na Delah gizah guda shine da kansa zai bada aurenta tabbas wannan tunanin idan yafado Mata kanta da tunaninta kasa dauka suke.

Ga tarin dibbin mamakinta tana shigowa Palo Imran suka tarar zaune Yana sako Mata murmushi da wani irin kallon Sonta daya gama yiwa tunaninsa da zuciyarsa mugun kamu saiyakejin kamar bazai iya rayuwa Babu itaba Dan kuwa komai zai iya faruwa dashi idan bai samu NURU ba amatsayin matarsa uwar 'yayan dazai Haifa.

Afia na ganin hakan ta wuce ciki tana Masa dariya da cewa"

Uncle Imran take it easy fa kada ka rasa 6sense dunka akan soyayya mu shiga uku barr IMRAN jalal ya zauce.

Da wata Yar dariyar qarfin hali yabi afia da zancenta idanuwansa suna Jan NURU dake tahowa cikin dogon wando da farar riga sai black scarf daure kanta duk da agajiye take sosai kyawunta ke bayyane tana qarasowa gap dashi ya miqa Mata cup din drink me sanyi da aka kawo Masa Yana cewa"

Have this my love kingaji ko?
Chapter 20 · 0% Book details