← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 66

Sashe 12

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NURU Jin tayi kaman tace zata zauna da farhat din ta janyota tana shafa gaban gashinta tace"

Zamu dawo da wuri Inshallah kinji kadaki Bata fuska.

Daki NURU Takoma ta sanya doguwar rigar datafi ta jikinta budewa da daura gyalen rigar akanta sbd su daura sukeyi suka fito afia na sanye da dogon jean da riga me tsayi har qasa saidai gefenta a tsake yake inda ake ganin dogon jean din.
Har jikin mota farhat ta rakosu tana riqeda hannun NURU har suka shiga mota suka fice.

Sai dare suka dawo lokacin farhat harta fara bacci jikin mum Sarah tana jinsu tataso da gudu ta fada jikin afia tareda riqo hannun NURU dake gajiye sbd yawon dasukai na gurare neman wasu text book na afian Kuma sukaje saloon akaiwa afian gyaran qafa itama hadda ita kanta.

Direct daki suka nufa afia tafara shiga bayi alwala kafin tafito itama tashiga tayo wanka tareda alwala tazo kusan atare sukai sallah suna gamawa afia tafara wucewa cin abinci kafin NURUn tabiyota abaya tareda farhat dataketa tambayan Ina da Ina sukaje.

Kamar ko yaushe ita tafara gamawa Amma sbd afia Bata gamaba Bata miqe ba Dan ganin kamar rashin girmamawa ne wa afian datake kamar shugabarta na matsayi.

Saida afia tagama suka miqe dukkaninsu sukai daki afia dakinta ta wuce ita Kuma NURU farhat ta raka dakinta ta sauyo Kayan bacci takaita tayo brush suka dawo dakinsu ta kwantar da ita gefen afia kan gado kafin itama tadawo kujera ta kwanta tana rufe idanuwanta sbd afia tuni tafara bacci Dan agajiye suke.

Washe gari dad dinsu zai dawo Dan haka gidan a natse yake anata gyara da girkin ire iren abincin da akasan su yakeci Dan shi mutum ne da bai cika cin abinci me maiqo ba ma'ana soyayyan Abu bai damesaba kodai dafaffe ko Wanda aka gasa.
Cikin farin ciki farhat take da dawowan dadynta hakama afian Dan haka da wuri tadawo school yau sbd tasan tareda dad din zasuci lunch Dan baya tafiyan dare yawanci da wuri yake dawowa idan yayi tafiya musamman irin wannan daya Dade.

Qarfe biyu da rabi da mintuna hudu jirginsa ya sauka suna zaune a babban Palo suna kallon wani film da NURU afia ce ke fassara Mata me suke cewa tana gyada Kai ahankali sbd kallonma kaman na dolene takeyi afiance ta sakata zaman dole Amma ita tafi Jin dadin zaman daki.

Sunajin diran motan isowanshi da sauri suka miqe farhat da gudu tayi kansa tana Kiran sunansa tana Isa yayi sama da ita Yana sake Mata wani irin murmushin daya kusa sumar da NURU data Dan waiwayo setin qofar idanuwanta suka sauka kanshi da sauri ta dauke kanta daga gurin tana sauke Kai tayi saurin miqewa tana barin palon tsoro na mamaye zuciyarta Dan tabbas laifine yiwa jinin sarautar delah kallon quri bareshi dayake maleek guda na delah gizah Dan haka hanyar daki ta Kama har qafafunta na Dan hardewa sbd tsoron kallon datai Masa Wanda takasa gane laifin ne ya tsoratata kokuwa.
Tana shiga daki toilet ta wuce tana shigewa ta rufo.

Afia ma riqo hannunsa tayi tareda dorawa a goshinta tace"

Dehina metahi ya abal(barka/sannu da dawowa mahaifina)

Kallonta yayi da fararen idanuwansa masu maiqo aciki wani boyayyan annurin ganinta cikin nutsuwa data samu na bayyanuwa cikin ransa ya bude Baki cikin muryarsa me Dadi da sirkin mulki da iko na Koda yaushe yace"

Da akwai wani sirrin wannan boyayyan farin cikin danake gani akan fuskan AFIA UBAYD MALEEK ne?

Wani murmushin farin ciki tasaki suna yowa cikin Palo tace"

Sirrin na farin cikin dawowan abal din afia ne.

Daddy bana dawowankane ba kawai AFIA tasamu best friend yanzu tana surutu da NURU acikin gidan Nan Amma daddy nidai NURU tawace sbd tanada girma irin na AFIA ne suke friends.

Kallon bakin farhat din yayi Yana sauketa cikin palon yace"

Hmmm farhat inaga you are the talkative anan.

Masu aikin gidan ne suka jero mum Sarah ce agaba suka rurrusana suna Masa barka da dawowa cikin tsananin girmamawa batareda kowannensu ya dago Kai ba ya daga musu Kai kawai suka juya suka bar palon Wanda idan ba aiki suka shigoba Babu me shigowa sai mum Sarah.
Har sama farhat tabishi ita Kuma afia ta ja luggage dinsa tabishi dasu iyakacinsu Palo qaida Babu me shiga master bedroom dinsa sai matarsa lailah Dan haka kosu 'yayansa Basu taba shigaba bare Susan Yaya yake.

Suna saukowa daki afia ta nufa inda tasamu NURU zaune tana kallon window inda take hangen library din karatun su AFIA sai datazo Nan takejin tabbas Ashe ilimin boko me yawa yanada amfani tunda gashi yanxu acikinsu Takoma tamkar wani kurman dabba da magana saidai a kwatanta Mata sbd duhun rashin ilimin bokon.

Dafata AFIA tayi tana cewa"

NURU Baki zo kinyiwa dad barka da dawowaba gashi harya shige se yafito cikin abinci Kuma.

Waiwayowa tayi ta kalli afian tareda dauke kai tace"

Darajana bekai naje gabansa harna tsaya na gaishesa.

Murmushi kawai afia tayi tana nufar mirror tace"

NURU kinason dakusar da darajanki anan gidan meyasa haryanxu kinkasa sakin jiki damu ki kulamu da qaunarmu yanda muke jinki?
Farhat na Miki kallon 'yar uwa Kamar ta jini Amma koyaushe kina Mata abubuwan dakesata tuna akwai banbanci me girma a tsakaninku,
Nayi iya duk yanda zanyi Nima ba nuna Miki irin qaunar damuke Miki mundaukeki 'yar uwa Amma Sam kinkasa sakewa Dani Nima meyasa?
Ko bakyajin dadin zama damu ne?
Rayuwanmu be Miki bane?

Tsoro NURU taji na shigarta na maganganun afia din ta juyo ta kalleta tana girgiza Kai tace"

Wlh ko daya Babu wannan sabo ne kawai matsalata inada wuyan sabawa da waje Amma wlh inajin farhat kaman meryam Babu wani abu dabaiminba anan hasalima wani irin girmane kukedashi aguna Wanda yasa bazan iya sakewaba sbd tamkar rashin girmamawa ne.

Ahankali Afia ta dawo takama hannunta tana cewa"

Karna sakejin wannan zoki rakani gurin karatu daganan zanfara koya Miki turanci.
Binta tayi zuwa libry dinsu dakeda wani irin girma da tsari da kyau ga littafai ko wani shagon Saida shagon littafan albarka.

Zama sukayi akan wasu kujeru masu kyau da taushi AFIA ta dauko wani littafi tana ajiyewa gaban NURU tace"

Kiyi kallon zanen dake cikin wannan littafin kafin nagama karanta wani abu cikin wannan littafin na hannuna idan nagama zanfara koya miki.

Karba tayi boyayyan murmushi na bayyana kan fuskarta Jin Wai tayi kallon Zane tsabar toshewar kanta kenan kaman wata yarinya kamansu meryam.
Budewa tafarayi tana kallo aikuwa zanen ne aciki na dabbobi da sunayensu irin su biri,doki,Kare,mage,zomo hardasu bera abin saiyaso Bata dariya ta murmusa harsaida haqoranta suka bayyana AFIA na lure da ita itama sai yanayin NURUn yasata boyayyar dariya.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899[9/8, 4:31 PM] Ummuanwar🥰: *_MG 10_*
File din hannunsa yasake rufewa ya dan kalli bayan file din tareda yamutsa fuska ahankali cikin yanayi na kamshin zai damesa ya bude Kai tsaye yayi signing inda zaiyi ya rufe tareda miqawa Imran din batareda yace komai ba cikin girmamawa Imran ya karba Yana sake Masa bayanin sauran paparworks din dasuke pending.
Sauraronsa kawai yakeyi idanuwansa akan makekiyar TVn data kusa cike Rabin bangon palon Yana Jin dukkanin abinda Imran din yake bayani akai saidai kaman hankalinsa nason kasuwa gida biyu Dan zuwa yanzu Kam yafara tunanin sauyin qamshin dayake shaqa a hancinsa daga inda yake zaune ne kokuma daga kayan jikinsa Dan yanzu ya tabbata ba file din daya miqawa Imran bane wani abin ne dabam shidaima koma menene qamshin na damunsa sbd qamshin na kaman turaren matane sbd lailah ta taba amfani da irinsa.......

Cak ya tsaya da tunaninsa guri daya tunowa da kusan karon dasukai da mace a palon hakan na nufin suturar jikinsu ta hadu data juna Dan idan ba hakaba Babu yanda zaayi qamshin ya maqalu a kayan jikinsa.

Miqewa yayi yabar palon Yana dagawa Imran Kai alamar amsawa daga gaisuwan a huta lafiya maleek dayayi masa ya shige Palo na biyu yakamata hanyar hayewa samansa.

Daidai fitan dad din daidai shigowan Afia data baro daga dakinsu tana ganin Imran ta saki wani qayataccen murmushin farin ciki tana qarasowa ta zauna tana cewa"

Barr uncle Imran yaushe kashigo?shine ko atambayi Ina afia.

Kallonta yayi da milky idanuwansa Yana sake murmushin daya sata qara kallonsa tana sake kyakkyawar fuskarta cikin muryansa me class kaman Koda yaushe yace"

AFIA MALEEK kinyi saurin tambayane Amma kinsan bazanzo nafitaba batareda naganki ba Dan haka ma nemanki dole ne.

Hmmm that sounds like a bribe.

Dariya yaso saki ya daure Yana miqewa tsaye riqeda hannun farhat Yana cewa"

Ina sauri zantafi zan dawo zuwa weekend zamu fitama inshallah Amma dagani sai farhat.

Tsalle farhat ta buga tana murna da cewa"

Amma zamuje da my lewa?

Kallon tambaya yayi wa afia data tsuke fuska tace"

Don't give me that look bazan fada maka wa take nufi ba tunda ku kadai zakuje kuje muma zamuje inda mukeda buqata.

Juyawa tayi zata tafiyanta yayo gurinta zai hanata tayi gaba da gudu tana cewa"

Kowa yaje da Wanda yakeso bazan fada ba.

Wata 'kayataccitar dariya yabita dashi cikin ransa Yana cewa"

Naga wadda kike nufi kawai inason sanin wacece ita din.

Juyowa yayi gurin farhat tareda shafa kanta Yana cewa"

Sainazo weekend din ko Uncle's princess.
Chapter 12 · 0% Book details