← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 66

Sashe 8

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiga sukayi bayin tafara nunnuna Mata komai daya bayan daya tareda fidda sabbin setin brush masu tsadar gaske da toothpaste Suma kala kala sai towels da aka jere Suma kusan sunfi guda biyar bangaren kayan wanka kuwa su sabulu da turaren wanka ba'ama magana Nan dai ta tayata komai har kusan wankanma ita tayi Mata Saida suka gama tafito NURUn tasake dauraye jikinta tafito daureda towel dinda yafi kowanne girma shima kusan daqyar ta daurosa kallo daya jekadi tai Mata ta dauke Kai tana sake yabawa da jinjinawa tunanin kaleeb na karbanwa UBAYD MALEEK yarinya 'danya sharaf sa'ar 'yarsa Kamar wannan tabbas za'aga 'yaya masu manyan idanuwa da hanci Dan kuwa NURUn tubarkallah uwa uba UBAYD din da shikam idan shima 'yayan zasu dauko angama magana.

Da kanta ta tsaya tana sake nunnunawa NURUn wasu abubuwan na dangane da shafa da qamshi da sauransu hardai ta shiryata cikin doguwar Bahrain gown blue wadda tasake haskota ta nada Mata gyalen take tayi fes kamar ba NURUn abal ba suka fito tana biyeda jekadi Kamar jela suka fito babban matsakaicin palonta suka nufa inda aka jere Mata abincin sai alokacin hanjinta sukai wani qugin yunwa Dan rabonta da abinci dama tun jiya da a gida ammi tai Mata dole ya Dan ci sbd cushewar ciki da damuwa.

Zama tayi Nan daya daga cikin bayinta tazo ta zuzzuba Mata komai nanma Saida jekadi ta nuna Mata amfanin kowane cokali duk da Bata iyaci dacokali ba tanada nutsuwar cin abinci tun agida kowa yasanta a natse take gudanarda komai na rayuwarta Wanda zaisa Kai tsaye bazaka gane batasan komaiba na wayayyi ko wayayyiyar rayuwa.
Ba laifi taci abincin sosai sbd tana jin matauqar yunwa gashi Kuma bazatace ta taba cin abinci irin wannan ba.
Bayan tagama cin abincin janta jekadi tayi aka sake kimtsata suka nufi gurin Kaleb Dan Kai gaisuwar safe dakuma Kai godiya da zaben dayayiwa NURUn Wanda jekadi a hanya take fada Mata yanda zatayi da yanda zatace.

Suna Isa Saida sukai tsayuwar kusan mintuna talatin kafin akai musu iso suka shiga bangaren tun daga qofar farko NURU ke kallon aljannar duniya danma ba halin bude ido sosai tayi sbd dokace babu Wanda ake Bari yakalli fuskar negestati batareda NEGES dinta yafara ganinta ba bare ita datake ta MALEEK guda shiyasa kusan fiyeda Rabin fuskarta rufe yake cikin burka(hular doguwar rigar dake jikinta)

Duk tarin qofofin Palo palon dasuka wuce akwai masu tsaronsu harsuka Kai wadda tafi kowacce zama babba da tsaro
Nanma Saida akai musu iso tukuna aka bude musu suka shiga aka rufo.

Zubewa jekadi tayi tana kwasar gaisuwa cikin tsananin girmamawa da ladabi.
A natse itama NURUn ta durqusa qasa kanta na qasa ta yaye fuskarta cikin sanyin da nutsuwarta ta gaidashi batareda tayi Masa kirarin dataji jekadi nata jerowaba sbd Bata iyaba.

Kallo 'daya yayiwa NURUn ya tabbatarda nutsuwarta ya dauke Kai Yana amsa gaisuwarsu tareda Basu izinin miqewa.

Basu wani jimaba suka fito zuwa sashe sashe na cikin delah din Wanda wani sashen a mota suka jejje sbd nisa da girman DELAH din,
Ayau ta tabbatarda arziki ma Ashe na wani sunane Dan kuwa taga inda arziki yake magana,
Tabbas delah wani Depot ne na arziki Dan idanuwanta da tunaninta sunkasa daukar wasu abubuwan data gani ahakanma akecewa gizah ta dame delah tabbas idan mutum beyi da gaskeba a irin Nan tsaf imaninsa zai barsa sbd kwadayin dawwama acikin irin wannan daula ta mulki.

Sai magriba suka samu damar dawowa sashenta duk da haka bawai koina suka samu zuwaba Kai gaisuwa saidai duk inda sukaje babu Wanda yaga fuskarta andai tabbarmusu da sabuwar negestati ce.
Tarin tukuicin dukiyar data samu ayau din Bata bayyanuwa danma asalin tukuicin na tafe ne ranarda za'a tabbatarda budurcinta delah ta sheda.

Kallon uban dukiyar zinarai da situru tayi tana rintse idanuwanta cikin tsananin azabar gajiya Dan qafafuwanta har wani numfashin azaba sukeyi daqyar ta miqe ta daddafa tashiga toilet tayi wanka ta gasa qafafuwanta tana tsiyayar hawayen tausayin kanta da kewar iyayenta itafa shikenan yanxu haka zataita rayuwa daga ita sai bayi sai idan neges dinda take tasa ya buqaci ganinta a turakarsa.

Tunanin hakan yasa kukanta tsananta tafara kuka sosai cikin bayin tana cusa kana cikin qafafunta Dan zaune take cikin bathtub.
Da kanta ta rarrashi kanta tasake dauraye jikinta tayi alwala tafito tazo daqyar ta tsaya akan qafafunta tayi sallolin da duk basuyiba yau din tana idarwa da kanta ta sidado ta fito cin abinci da yunwama Kamar ta kusa kasheta.
Tana zama dakanta ta zuba abincin sbd duk basanan suna gurin sallah Suma Dan Suma Kam sun gaji hannu tasaka Bata tsaya saka wani cokaliba kadanma taci sbd cikinta daya qulle tasha lemun sabuwar abarba ta miqe ta nufi daki tana shiga ta kwanta kife take baccin wahala yayi gaba da ita.

Washe gari ma yini tayi daki kwance abinci kawai ke fiddo da ita Palo har dare bataga jekadi ba sai washe gari da yamma tazo bayan ta tabbatarda NURUn ta huta daga wahalar shekaran jiyan kafin suka fara gudanarda aikin dake gabansu.

Sannu ahankali jekadi take koyarda ita komai na al'amuran rayuwar gidan sarautarsu ta delah,
Duk wani abu dayakamata NURUn ta sani Kuma ta iya Ana kan koya matashi Kuma tana 'dan ganewa duk da hankalinta tashi yake idan Ana fada Mata wasu abubuwan ko koya Mata sbd batasan ta Yaya zata gudanar da rayuwarta ahakan ba,

Ta bangaren iyayenta kuwa tuni ta aika musu da dukkanin tarin dukiyar tukuicin data samu.
Ga kaleeb ta bangare daya kullum saita je takai Masa gaisuwa Wanda jekadi ce ta 'dorata akan hakan bawai Dan al'ada bace kawai tanason Gina qauna me qarfi ne tsakanin NURUn da kaleeb sbd sanin irin tsananin qauna dake tsakanin Kaleb da UBAYD MALEEK.

Sannu ahankali tafara sabawa da rayuwar delah ga jekadi ma data Dan shaqu da ita sbd tana Mata kallon uwa kokuma tacema Kaka musamman sbd itama jekadin tsakani da Allah taji tana qaunar NURUn sbd nutsuwa da biyayyarta ga rashin son hayaniya sai hakan kesake saka Mata nutsuwa da shigar NURUn rayuwar UBAYD koba komai UBAYD Kamar 'dane agareta sbd agabanta aka haifesa yagirma.

Tsawon watanta biyu a delah Amma haryanxu ko a zance bataji maganar waye aka bada ita gurinsaba,yaushe za'a kaita,Ina yake haryanxu shiru duk bataji komaiba Abu daya tasani shine jekadi ta fada Mata wata me kamawa za'a kaita wani guri.
Da farko hankalinta ya tashi Jin tafiya wani guri Amma sai jekadi tafara kwantar mata da hankali da cewar zasu dawo bawai zaman dindin bane itadai Sam hankalinta yakasa kwanciya ko bacci yanzu kasawa takeyi saitajin Kamar rabuwa zatai da gida har abada.

Ganin kwana biyu har wata rama ta sakota gaba da tunani da damuwa yasa jekadi takwai Kaleb zancen sai tunani ya shegesa yace anfasa Kiran zuwan UBAYD sbd idan yazoma kowa zai San shi keda negestatin Kuma Kamar yanda akasan MALEEK da ikonsa bazai taba karban negestati ba matuqar ba baya tareda matarsaba hakan zaisa afara tunanin sun rabu Wanda za'a iya amfani da wannan gurin muguwar manaqisar mulki akawo suka ga karban mulkinsa Wanda keleb bazai taba Bari hakan tafaru ba yafison koda za'a San ubayd da matarsa sun rabu zuwa lokacin sun samu wata Matar aure kawai za'a daura idanba hakaba da matsala babba Dan haka yasa aka matso da tafiyar NURUn tareda Bata damar izinin zuwa ganin iyayenta da daddaren yau.

Qatuwar baqar Mercedes Benz beymach ta ajiyeta gefen gidansu da qarfe goma sha biyu na dare Wanda shine lokacin barinsu fita delah tana kallon qofar gidansu jikinta yayi mugun sanyi taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta ziro qafarta waje ahankali tareda fitowa.
Kai tsaye itace agaba jekadi na gefenta tana cewa"

Karkiyi kuka gaban iyayenki Zaki daga musu hankali Kuma laifine babba yin kuka was umarnin masarauta Dan haka ki kula.

Batace komaiba itadai burinta ta Isa cikin gidan taga ahalinta cikin sa'a kuwa har lokacin abal dinta da ammi na zaune tsakar gidan kan shimfida suna Shan iska sbd tsananin zafin da akeyi yau din meryam ma na kwance gefen ammi tayi bacci ammin na Mata fitar sauro.

Da budaddiyar murya jekadi ta rangado sallamar da har maqota anaji sbd asan da zuwan NEGESTATI ne.

Da ammin da abal lokaci daya suka miqe suna kallon qofar dasu NURUn ke shigowa wadda qamshinta tuni yafara cika tsakar gidan da hanzari ta qaraso ta fada jikin ammi tana riqo hannun abal duk alokaci daya tana sake hawayen farin cikin ganinsu batareda ta iya cewa komaiba.

Cikin tsananin farin ciki ammi ke Mata yare tana cewa"

Ya Allah NURU munyi kewarki matuqa.

Murmushin farin ciki kawai abal ke saki Yana kallonta ta cikin hasken farin wata Yana sake godewa Allah daya bashi ikon ganin 'yarsa 'daya tasamu gidan zamanta na rayuwa saura daya itama Yana fatan Allah yabasa ikon ganin yayi Mata aure ta tafi nata gidan.

Zama sukai tana tsakiyar iyayenta Meryam ma tuni NURUn ta tayarda ita sbd bazata iya tafiya basui mgn ba tana ganin NURUnta tafada jikinta da qarfi tana ihun murna Wanda ya tado da gimbiyar gidan wato padima ta fito cikin wani irin laushi tana jujjuya ido ta bude da kyau tana kallon mutanen idanuwanta suka sauka kan NURU tasake dubawa dakyau taga NURU ce da sauri ta qaraso tana cewa"

NURU????
Kece yanxu?

Dagowa NURUn tayi fuskarta daukeda murmushin kewar padiman ta taso suka rungume juna tana cewa"

Nayi kewar dukkaninku padima.

Zaman sukayi padiman nabinta da wani kallon kurulla da zallar mamaki tanson yin tunanin fahimatar wani abu kanta Yana toshewa da mamaki dakuma tausayi tausayin NURUn da rayuwarta ta lalace.

Shagala sukai sosai harsaida lokaci yaja jekadi tashigo da cewar zasu tafi Nan jikinsu duka yayi sanyi Amma hakanan suka bawa NURU qwarin gwiwa abal yabita da wasu irin adduoin Sanya albarka masu zafi wainda suka Sanya jikin kowa yin sanyi suna amsawa da Amin.

Har mota suka rakota tashiga padima sai kallon komai take cikin mamaki tana qaryata abinda idanuwanta ke gane Mata sbd tasan ba komai bane duk wannan akan irin rayuwar da ita zatayi a Nan gaba.
Chapter 8 · 0% Book details