← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 66

Sashe 3

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallonsu bataiba sbd halinda zuciyarta take ciki gabaki daya a jagule take bazataso auren iyayenta ya rabu ba akan iko,izza da isar dad dinta dakuma taurin Kai da burin duniya na mum dintaba,
Farhat kawai take dubawa sbd yarinyace sosai akanta sbd ita yanzu takeda 8years a duniya bazata iya ganin iyayenta sun rabu ba saidai abu daya tasani shine rabuwa kamarma sunyine Dan Babu abinda zai sauya taurin Kai irin na mum
Dad din Kuma aishi kankat ne Dan yafita zama riqaqqe saidai tana jin tausayinsa sbd mutum ne shi me tsananin qyanqyami na komaima
Suna rabuwa da mum za'a fara kawo Masa 'yayan manyan masarautu kokuma ma za'a iya kawo Masa negestati Wanda tasan tsananin qyanqyaminsane ya hanasa qara aure aure kamar sauran 'yan delah musamman shi dayake ubayd maleek na GIZAH,
Hakan nema yasa ya kebe kansa anan new York da iyalinsa Yana gudanarda rayuwarsa a qaidance yanda yake sonsa ba tarkacen hayaniyar masarauta duk da yasan dole wata Rana zai koma can da zama.

Bedroom dinta ta nufi ta fada kan gado tareda rintse idanuwanta hawayen ciki suka gangaro ta share da qarfi cikin takaici tace"

Bazanyi kukaba mum tunda haka Kika zabar Mana shikenan zamu runguma mu rayu Kamar marayu duk da munada uwa Amma ta zabi duniya akanmu.

Miqewa tayi tafada toilet tayo wanka tana fitowa tashirya a gaggauce ta zari ipad dinta ta fito ta nufi library din karatunsu tana qoqarin fitarda damuwar dake cikin ranta sbd mum tayi nisa batajin Kira sbd sunfi shekara akan wannan mgnar taqi barinta yanxu harta karbi takardun contract din shikenan komai yazo qarshe.

'dagowa tayi bayan ta zauna cikin library din ta kalli qaton makeken hotonsu na family daya cinye kwatan bangon library din ta qurawa dad dinta fararen idanuwanta da nashine ta dauko Zak,
Bawai Dan tana tsananin son dad dintaba Amma Bata taba ganin mutuminda ya hada irin qualities dinda ya hadaba,
Dad dinta is 99% takowane fanni.

Mum dinta takalla ta rintse idonta ta bude tana cewa"

She's perfect, she's beautiful tanada komai but she's nothing compare to dad Amma takeson barinsa meyasa?

Farhat da kanta takalla a hoton take hawayen datake riqewa suka gangaro mata ta miqe tabar gurin tana fasa karatunma.

________
********NURU"" ammi takira sunan cikin tsoro da fargaba,
Abal meyesa kake ganin zabin NURU shine daidai bayan kasan NURU bazata iyaba.

Numfashi ya sauke Yana gyara kwanciya yace"

Padima gidan sarauta kamarna delah zaisa burinta ya fadada zai iya hallaka tunaninta da tarbiyarta.

Amma Kuma abal NURU tayi rauni da yawa kaduba.

Aa jamila kina dai tausayinta ne Amma itace zata fi mutunci a irin gurin sbd me hkr shine zaici ribar zama a delah.

Riqo hannunsa tayi tana marairaicewa da hawaye cikin idanuwanta sai jikinsa yafara sanyi Sam bayason ganin damuwarta sbd tsananin so da qaunarta dayake,
Kusan sati daya kenan sunata muhawarar wazasu bayar din kafin shi ya yanke NURU itakuma ta yanke padima.,
Ajiyar zuciya ya sauke sbd tunanin dayayi na girman Kai da burin padima na zuwa DELAH GIZAH bazai taba barin ta yardar musu ta yarda subadata a delah tanan ba tsaf yasan bijirewa zatayi sanin haka yasa yacewa ammin ya amince abada padima.
#MAMUH#
*_Haske writers💡_*

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_ZAFAFA BIYAR_💘💘💘
_ZAFAFA BIYAR_💓💓💓

_(ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL)_

_(HUBILMAHX)🧡🧡🧡_

_ASSALAMU ALAIKUM! INA MASOYA MA’ABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA?!_

_TO KU MARMATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKE KAWO MUKU DA’DADAN LITTATTAFAN NAN ZAFAFA GUDA BIYAR, SUN SAKE ZUWA DA KASHI NA 4._

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_

_RIGIJI GABJI DINFA KENAN, DOMIN WANNAN KARON MA MARUBUTAN SUN SAKE KAWO MUKU WASU DADADAN MASU FADAKARWA, NISHADANTARWA, NISHADANTARWA UWA UBA KUMA AKWAI LAGWADAR SOYAYYAH..._

_*SAFIYYAH HUGUMA:* TAZO DA NATA SALON RUBUTAN MAI SUNA: *ALKIBLA*❤️❤️_

_*HAFSAT RANO:* TAZO DA NATA TAKEN RUBUTUN MAI SUNA: *MABUDIN ZUCIYA*🥰🥰_

_*MAMUH GEE* TA KARA ZUWA DA WANI SAMFURIN MAI SUNA: *UBAYD MALEEK*😘😘_

_NANA- HAFSAT *(MISS XOXO)* TA SAKE ZUWA DA WANI KALAR NA: *DALAAL*💞💞_

_*BILLYN ABDULL* TA KARA ZUWA DA WANI TAKEN MAI SUNA: *MAKAUNIYAR KADDARA*💝💝_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*3*
Tafiya takeyi cikin nutsuwar datafi Kama da jin Kai da taqama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankali shiyasa duk Wanda ta hadu dashi a hanya yake hadiye Mata yawu musamman wainda sukasan padima ai tafi karfinsu sbd kyanta da ikonta tareda sanin Wanda suke soyayya dashi din daga delah yake wato Dan babban sarkin fadawa bama Wanda yake Nanba na can gizah.
Daga gurin karbo baqin lallensu take sbd koyaushe ita mace ce da Bata rabuwa da qyale qyale shiyasa yanada wuya kaganta Babu lalle faratanta na hannu Dana qafa shiyane qarin banbancin tsakaninta da NURU wadda duk wannan ta daukesa Kamar bayyanarda kyawu ne Wanda ita tafi ganin burgewarsa idan kayi aure kayi acikin gidanka.

Daga bayanta taji anriqo hannunta ta tsaya cak tareda wani juya idanuwanta wani qayataccen murmushi na sauko Mata sbd sanin Babu Wanda yake iya riqota haka sai mutum daya saidai kafin ta juyo ta hango su NURU tafe da sauri ta juyo ta jasa da gudu suka boye bayan wata qatuwar bishiya tana Dora Masa hannun abaki qasa qasa tace"

Shihhh su NURU na zuwa.

Wani shu'umin murmushi ya sakar Mata Yana gyada Kai kafin ya juya ya zubawa NURU mayun idanuwansa dukkanin yawunsa na katsewa akan NURUn,
Meyesa ba NURU ce wadda Allah yabasa sa'a akantabane Dan wlh baitaba jin mugun kwadayin maceba Kamar NURU gashi padimanma tai Masa Amma da zaa basa zabi da NURU zai zaba Dan duk Wanda yagama samunta a Mata ko a abokiyar haihuwa yagama dacewa,
Mummunan faduwa gabansa yayi daya tuno da hadda abal dinsu acikin yan sauyin 'yanci take ya waiwayo da sauri ya kalli padima Yana girgiza Kai Dan wlh bazai yadda yabarta tashige zuriar delah ba tabarshi Dan har abada bazai taba samun kyakkyawar mace kamarta ba tunda dai NURUn yasan ba samunta zaiyiba Kuma dai dole cikin dayan biyun ne ko padima ko NURUn,.

Ina Ina ina""yafada cikin ransa da sauri Yana girgiza kafin ya maida kallonsa kan bayan NURU data wuce Yana tunano da kaf delah yanzu duk Wanda za'a kaiwa negestati Babu Dan yaro yaro sbd yara yara shekara daya kenan cif da aurarda yayan masarautar delah din su goma sha daya Kuma a qaida saikayi shekaru uku da aure zaka fara karban negestati sai wainda basuyi aureba sukuma baa Basu negestati sai sunyi aure.

Kallonsa padima tayi da manyan idanuwanta tana cewa"

Yaya dai?
Tunanin me kakeyi?

Wani murmushin bazata ya sakar Mata Yana sake jawota jikinsa Yana shafa hannuwanta Yana matsawa ahankali ya kashe ido Yana cewa"

Padi padi,
Padi nidai maganar gaskia zanje nasamu abal dinku yasan da maganarmu sbd so nake kafin kwana talatin dinsa tacika kinzama tawa mun wuce gizah..

Da wani kallo ta katsesa tana Dan zamewa idonta akansa tace"

Kwana talatin kamar dai wadda aka gaji da ita,
Amed nafada maka banason auren gaggawa sbd inason aurena yazama abinda zai burge kowa,
Banice baiwa ba abal dinane bawa Dan haka Ni inada damar yin bikin aurena kamar na kowanne 'yantacce,
Hakama Ina buqatan shiga boyon wankan ruwan madarar nono na tsawon sati biyu hakama Ina buqatan siracin nonon raqumi na tsawon sati biyun Shima sbd ranar dazan fito muka isa gizah aranar za'a tabbatarda nafi fiyeda Rabin matan sarautar kyawu.

Wani murmushin manufa tasaki tana sake riqe hannuwansa cikin kisisina Dan kuwa itadai babban burinta tasamu isa delah gizah inda asalin arxiki, mulki da sarauta suke
Kyawunta shine zai cika Mata burinta shikuma amed shine mukullun tafiyarta.

Cikin marairaice fuska yace"

Padima bazan iya Bari kwana talatin din abal dinku yacikaba sbd zai iya zamtowa kece zai bada bazan iya rasakiba padima mutuwa zanyi idan bake.

Wani kallon rashin fahimta take binsa dashi fuskarta na sauyawa tace"

Badawa Ina?

Gyara tsayuwa yayi Yana sake tamke hannunta yace"

Abal dinku ya karba shedar sauyin yanci.

Wani irin bugawa kirjinta yayi tana qwace hannunta daga nasa cikin son qara tantancewa tace"

Negestati??

Gyada Mata Kai yayi Yana cewa"

Eh padima Kuma Nanda kwana talatin ne za'a karba wadda zai bada kowane lokaci za'a zo afara gyaran ko ke ko NURU.

Wani irin daure fuska tayi zuciyarta na harbawa da qarfi a matuqar zabure take cewa"

Meyasa abal zai Mana haka?
Meyasa zai yanke hukuncin badamu negestati baiyi shawara damuba bama wannan ba"" da sauri ta rqio hannunsa son tabbatarwa tace"

Amed ko kasan waye za'a karbanwa negestati din?
A delah tanan ne ko a delah gizah be?
Fadamun da sauri amed inason sani ne idan a delah gizah za'a Kai.

Kallo biyu yake Mata,
Kallon Sonta da kallon yasan manufarta akansa Dan haka cutar cuta za'ayi yasani Sarai sbd yace gizah zasu take taredashi ta yanda idan an isa zatasan yanda zatai ta watsar dashi ko negestati ta zama acan din ta yarda shikuma Yana sane Sarai ba gizah din dazashi hakama yasan wannan tambayar datake Masa Dan taji idan Wanda za'a kaiwa negestati a gizah ne tsaf zata samu abal dinta tace abadata Amma yasan yanda zaiyi da ita ko taqi ko taso ita din tashi ce shi daya.

Bata fuska yayi kalar tausayi ya riqota Yana cewa"

Padima shiyasa bazan iya Bari abadaki ba sbd anan delah ne za'a bada Kuma qarin cikin abin a yanda naji abeela za'a kaiwa qila mutuminda shine kusan babba acikin jikokin delah ya tsufa ko me zaiyi da mace yanzu?,
Padima bazanso kije rayuwarki ta gurbata ba Zaki samu arziki da mulki Amma baida amfani sbd bazaki more rayuwarki yanda kikeda buri ba gwara muyi aure mutafi gizah acan nasan rayuwa zatai Mana dadi.

Jin Wanda za'a bawa negestati din yasake daga hankalinta tafara girgiza Kai tana cewa"
Chapter 3 · 0% Book details