← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 66

Sashe 4

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Badai ni padima yonas ba,
Sam rayuwata bazata mutu ba agurin bautawa tsohoba duk ya zugemin kyau da quruciyaba,
Padima darajata ta wuce Nan wlh bazan yardaba saidai NURU koma meryam za'a bada abada nidai wlh bazan yardaba.

Juyawa tayi ta nufi hanyar gida cikin tsananin tashin hankali batareda ko takansa tasake biba,

Duk rashin hankalinta da girman kanta bazata iya bijirewa iyayenta ba saidai zata fada musu bataso idan sun nace bazata iya musu taurin kaiba saidai
Abu biyune tasani matuqar aka bada ita negestati to rayuwarsu kaf tana cikin hadari sbd duk Wanda aka kaiwa ita ya kwana da ita zaijita ba budurwa ba Wanda hakan babban laifine hukunta kisa itada iyayenta duka idan sunada jini acikin delah wadda ta taba zama negestati shine zata roqar musu sassauci baza'a kashesu ba saidai za'a koresu daga qasar gabaki daya to gashi basuda Yar uwa ko daya delah dama burinta ta auri amed sukoma gizah inda tasan kyawunta saisa kaitsaye tasamu Dan sarauta bayan tasan yanda tayi ta rabu da amed yanzu ga wannan babbar maganar ta bullo yau ita wazata fito tafadawa kada abadata sbd ita din ba budurwa bace.

Koda ta isa gida har wani murdawar tashin hankali cikinta keyi tayi danasanin bawa amed kanta yafiso cikin kwando dari Dan kuwa Sarai tasan masifar hakan a addinance dakuma al'adance.

Tana shiga gida dakinsu tayi da sauri ta ajiye kayan hannunta tafito ta zari buta ta nufi bayi tana kaucewa kallon inda abal da amminsu ke zaune suna binta da ido.
Koda tashiga bayin kasa yin komaima tayi tafito tana qoqarin sakewa tazo gurinsu abal din ganin su NURU sun dawo ta zauna anacin gasasshen dankalin dasukeci da ita.

Kallon NURU abal dinsu yayi hakanan yake sakejin hankalinsa yafi kwanciya da zuwan NURU sbd ita din tafi cancanta duk da baisan waye za'a kaiwa ita ba Amma dai yasan delah basuda tarihi mara kyau Dan haka duk Wanda za'a kaiwa baida fargaba ko shamaki.
Padima yakalla yasake kalla zuciyarsa  nasake tabbatar Masa da kamar kaita wani kuskure ne koba komai yafison yabarta ta aura Wanda take Dan burintane ita Kuma NURU bada ita ba'a shiga haqqintaba sbd batada wani buri sai wanda su iyayenta suka yanke akanta.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonsu cikin nutsuwa yafara koro musu bayani komai tareda dorawa da cewa"

Padima kiyi hkr da wannan al'amari daza'a Kira da qaddararre sbd tabbas kowane uba zaiso ganin ya aurar da dukkanin 'yayan da Allah ya azurtashi dasu,
Naso ganin hakan Nima kamar kowane uba saidai Allah be nufa zanga na dukkanin 'yayana ba saidai biyu daga ciki Dan haka padima Ina Baki hkr dakuma umartaki dakiyi biyayya wa Ni mahaifinki dakuma al'ada da dole ki karbi wannan qaddarar dan haka saiki nutsu Zaki daina fita daga gobe sbd za'a fara Miki wanka da siracin sabuwar Madara za'a fara kawowa daga DELAH.

Tsit sukayi dukkaninsu kamar ruwa ya cinyesu musamman padima da jikinta yadauki mazari tafara hada zufan tashin hankali Wanda yasa umminsa shiga tunani me firgitarwa kafin wani yayi magana padimar ta bude Baki murya na rawa tace"

Abal...abal NURU.... NURU..Ni inason A....zungurinta umminsu tayi tareda katseta da cewa"

Kutashi kuje kuyi tunani inshallah Zakiyi farin ciki da hakan ba dama gidan arziki da mulki kikeso ba Inshallah zakiji Dadi.

Cikowa idanuwanta ke neman yi ta girgiza Kai tana cewa"

Ammi ba hakan bane ni...Ni..

Kuje nace padima.

Kamata NURU da jikinta yagama sanyi tayi Dan ita gabaki dayama ta firgice dajin abinda yake faruwa sbd ita ko delah akace za'a saitaji duk ta firgice bare ace itace zata shiga delah ta zama jininsu Sam firgici ma tunanin hakan yasata shiyasa tausayin padima yashigeta me tsanani duk da tasan padima ita zata iya duk da idan tashiga ita din ba komai bace Amma dai gwara ita zata iya.

Suna shiga daki padima ta zube kan shimfida tana sake shiga tashin hankali wlh Bata shirya mutuwaba,batason mutuwa Ina zata saka kanta dole ta samo mafita.

Duk irin lallashi da kulawarda NURU ke Mata cikin tsananin tausayawa Sam Bata fahimta sbd hankalinta baya jikinta.
Abu biyu da biyu ga zama negestatin tsoho mara amfani,ga tsoron agano ta taba kwanciya da wani Kuma ta shiga delah ga tsoron hukuncin hakan duk saitaji tana neman haukacewa wlh bazata iyaba Gwara abada NURU Dan ita tunda duniya Bata dametaba zata iya rayuwa da tsoho ko baida amfani itadai ba ruwanta can su qarata.

Har gari ya waye Bata rintsa ba sbd tsananin tashin hankali Koda ta fito da safe babu Wanda bai fahimci Bata hayyacintaba duk ta firgice gashi tanason ganin amed suyi magana Kamar me ba halin fita Dan idan Bata samu magana dashiba komai lalacewa zaiyi.

Da maraice saiga manyan bayin delah kusan guda goma sha biyu sunkawo tarin kayan wankan Madara daza'a fara Mata washe gari tana ganin hakan hankalinta yasake tashi jama'ar gari kuwa suna gani suka tabbatar aka fara zarya gidan tayasu ammy murnar samun yancin abal da murnar shigar 'yarsu delah.

Kwanaki goma sun shude da fara gyaran Negestati padima Amma Sam hankalinta a hargitse take takai yanxu ko rintsawa Bata iyayi tun abin na wasa tadawo ko abinci Bata iyaci take tafara wata irin rama da duhun tashin hankali daganan sai kukan dare Wanda yayi masifar daga hankalin NURU da duk duniya taqi jinin ganin damuwa akan fuskar iyayenta da 'yan uwanta ta tashi cikin tsakiyar dare tareda lalubar qaramar fitila ta kunna taga padima zaune hannunta riqeda wuqa tana faman wani irin kuka da sauri ta qaraso ta fixge wuqar cikin tashin hankali da tsoro jikinta yadau rawa sbd ita qaramin abu ke firgitata tace"

Padima me Zakiyi da wannan tafada ta wurgi da wuqar cikin tsananin tsoro.

Sabon kuka padima tasake tana qwacewa tace"

Mutuwa zanyi tunda ko ban kashe kaina yanxuba naje delah mutuwa zanyi.
#MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN K xxAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899[9/6, 6:12 PM] Anty Rabi'at: *_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*4*
Cikin tsoro da rawar murya NURU tace"
Padima kidena cewa mutuwa kina bani tsoro sosai kidaina kuka menene Dan Allah ki dena kina bani tsoro.

Ganin yanda NURU duk ta firgice cikin tsananin tsoro yasa tadan sassauta tayi tunanin amfani da tsoron NURU sbd dama can ita abu kadan yake Bata tsoro saita sake marairaice fuska tana faso wani kukan tace"

NURU idan Banga amed mukai magana ba akwai babbar matsala wlh komai zai lalace zamu rasa komai da iyayenmu duk mutuwa zamuyi.

Zaro manyan fararen idanuwanta NURU tayi jikinta na daukar rawa tana sake padiman takasa magana tana neman yin baya ta fita a rude padima ta riqota da qarfi tana cewa"

NURU wlh dagaske nake idan bangansa munyi magana ba komai zaifaru Dan Allah kimin hanya naganshi idan nadawo zan fada Miki komai Amma wlh rayuwata na cikin hadari danasu abal ma..

Kasa fahimtarta NURU tayi sbd firgici sai rawa da jikinta keyi ganin hakan yasa padiman taja wani qaramin tsakin takaici tareda girgizata da qarfi ta jawota ta direta zaune tafara shafa bayanta tana hura Mata iska tana kiranta ahankali ahankali hartafara nutsuwa tana dawowa hayyacinta saidata rarrasheta tadawo hankalinta tsaf tukuna ta janyota ta kwantarda kanta kan cinyarta tafara Sabin hawayen samun yaddar NURUn tasake fada Mata abinda tafada Mata da farko NURUn daketa ajiyar zuciyar ta qanqame padima cikin tausaya Mata murya amatuqar sanyaye tace"

Padima idan kikaga amed din shine zesa bazaki kashe kanki ba ko?

Eh NURU bazan kashe kainaba Ni sbd ma kune nakeson ganinsa na nema mafita.

Haka ta lallaba NURU taringa marairaice Mata da kuka hartayi nasarar cika tunanin NURU da tausayinta akan alamarin shiyasa washe gari da za'aje wankan ruwan Madara saita lullube fuskarta taje amaimakon padima bayan tayi Mata hanya sunyi sauyin kaya ta fitar da ita gidan masu wankan dasuka ganta saisuka tambaya tace ai yanzu ita za'a ringawa ba padima ba dayake bayin qasane gabaki daya saisuka yarda sbd manyan bayi basa fitowa delah bare akawo musu irin wannan.

Dama Shima NURU taje ta sanar dashi padima zata fito tanason ganinsa shiyasa yaje inda suke haduwa Yana jiranta danshima a mugun qage yake da ganinta Dan wlh Shima be shirya mutuwaba tunda yasamu labarin ita aka bayar yasan qaryarsa taqare kashesa zaayi duk ranarda akaji shine yafara kwanciya da ita.

Kamar munafuka haka take tafiya tana waiwaye tana boye fuska harta iso Yana ganinta da gudu ya qaraso yakama hannunta suka nufi can nesa da gidajensu cikin wani lambu bayan bishiyar ayaba ya rungumeta Yana cewa"

_Ya Allah Padima nafekushi_
(Ya Allah padima Nayi kewarki sosai)

Kuka tafashe dashi tana turesa daga jikinta tace"

Amed duk mutuwa zamuyi
Banason mutuwa guduwa zanyi da qasarnan zanshiga duniya bazan tsaya akasheni ba...

Riqota yayi da sauri Shima cikin firgicin yake yace"

Padima ki nutsu musamo mafita Nima angaya Miki na shirya karban wannan hukuncin ne?
Bazan iyaba nikaina mafitar nake nema.

Zamewa tayi qasa tayi zaman dirshan tana cewa"

Amed kayi gaggawar samo mafita kokuma kawai mu gudu.

Mu gudu muje Ina padima?
Idan muka gudu burirrikanmu fa damuka Dade muna....

Cikin masifar tashin hankali ta katsesa da cewa"

Burin banza tunda Saida rayuwa zamu cika burin,
Ni kaga kawai musan abinyi wlh na cikin masifa wannan wane irin balai ne nasaka kaina aciki amed ka cuceni...

Kinga yi hakuri kidaina kukan yanxu mafitarmu dayace ajanye badake abada NURU.

Wani kallon takaici da baqin ciki tai Masa tana cewa"

Sun San da NURUn suka badani sbd tunanin ita wawuyace batada wayo Ni bansan inda zansaka kainaba zuciyata fashewa zatayi....

Da sauri ya durqusa gabanta cikin Dan samun sa'ida yace"

Muyi amfani da sanyin halinta kiyi Mata wayo ki gurbata Mata tunani da tsananin tausayinki ki Bata tsoro da rayuwar iyayenku da kanta zata bada kanta.
Chapter 4 · 0% Book details