← Book details Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 66

Sashe 10

Ubayd Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fada ta miqe ta fice Dan komawa gurin AFIA ta sanar da ita inda NURUn zata zauna duk da Babu Wanda yasani ita tasan babban laifine Kuma bazai yiyuba tabari negestatin maleek ta kwana acikin masu aiki ko bayan shekaru dari ne idan har tana raye tasan wata ran saita fuskanci hukuncin hakan.

Cikin girmamawa Kai aqasa tayiwa AFIA bayanin inshallah zasuji dadin zama da NURU Kuma tana bada hkr amaimakon NURUn.
Murmushi me qayatarwa kawai afia tayi tareda cewa"

Ba damuwa ki dawo da ita dakina takwana.

Angama.

Wannan karon da sanyi tashigo dakin bayan tayi knocking ance tashigo.
Qarasowa ciki tayi ahankali ta iso har inda afia din ke zaune kan kujera tana karatu a iPad dinta batareda ta dagoba tacewa NURUn"

Ki zauna kokuma daima ki kwanta tunda agajiye kuke.

Gyada Kai kawai NURUn tayi tareda zaunawa a qasan kujera afia na ganinta batace Mata komaiba ta qyaleta sbd ganin kamar zata takurata da yawane idan tace yasake dasu lokaci daya duba da irin matsayin dasuke dashi dayasa kowa ke Basu tsananin girma dama mutum take buqata akusa da ita akoda yaushe so ko Babu sakewa atsakaninsu ba laifi tunda dai akwai mutum din.

A kan kujera NURU ta kwana AFIA da farhat dake kwana a dakinta suka kwana cikin makeken lafiyayyan gadon dakin lullube cikin bargo me taushi.
Farhat na zuwa makaranta da wuri shiyasa kusan gidan kowa yatashi da wuri sbd shirinta wannan yayi wannan wancan yayi wancan haka Shirin nata yake.

Bacci ne a idon afia sosai sbd ta Dade da daddare tana karatu Dan haka Bata tashiba NURU ce dake zaune jungum taga farhat din nata yaqin saka uniform ta taso tazo ta durqusa gabanta tareda karban uniform din tana Dan sake siririn murmushin tunowa da meryam dinta wadda Allah yasanya mata tsananin kaunar qanwar Tata shiyasa so da dama takeda son yara duk yaron data gani meryam dinta takeji cikin ranta musamman farhat datake kusan tsara da meryam din.

Ahankali tafara Sanya Mata kayan tana cewa"

Kintashi lafiya?

Kallon fuskanta farhat keyi tareda Kai hannu ta latso kumatun fuskar NURUn dakeda taushi sosai cikin murna tace"

you have a very beautiful face like my Barbie.

Duk da batasan me farhat din tafada ba yanda take kallonta da yanda ta taba fuskanta yasata sakin siririn murmushi tana shafa fuskan farhat din tace"

Lewa (you're beautiful too/kema kinada kyau/kyakkyawa)

Duk da basa wani Jin Amharic sbd mum dinsu Bata musu dad dinsu Kuma turanci ne mafi yaren dayake musu mgn dashi shiyasa Basu wani ji kakarsu ce kawai mahaifiyar dad dinsu ke musu yarensu na amheric Amma dai duk da haka tasan me ake nufi da lewa cikin murnar tasan menene NURUn ta fada tace"

Lewa means beautiful right?

Ido NURU ta zuba Mata sbd batasan me tace ba.

Kamo hannunta farhat tayi tajata tana cewa suje ta rakata cin abinci batason ci ita daya a dining.
Kamar jela haka tabita zuwa dining din saidai Bata zauna ba ta tsaya har me aikin abincin gidan dake tsaye ta zubawa farhat din abinda tasan shi takeci itadai tana tsaye tana kallon ikon Allah dayake jekadi ta Tara masu aikin gidan kaf tayi musu bayanin NURU itama daga delah take su girmamata Kamar yanda suke girmama su AFIA shiyasa me aikin me suna Fana tana gama zubawa farhat komai ta jawa NURU kujera Dan ta zauna cikin girmamawa tace"

Me za'a kawo Miki?

Kallon kujerar dining din dake zuba qyallin adon zaiba tayi tana kallon bakin Fana din kafin ta kalli farhat data kamo hannunta tana cewa"

Zanyi latti fa ki zauna.

Zama tayi a dosane tareda girgizawa Fana Kai alaman aa Bata buqatan komai.
Ahankali take taya farhat cin abinci ta hanyar Bata ruwan tea ahankali ahankali sbd zafinsa harsuka gama ta goge Mata Baki da tissue suka taso farhat har lokacin tana riqeda hannunta sbd Babu Wanda yataba zaunawa da ita tunda tafara wayo yabata abinci abaki sai yau sai hakan yamata Dadi sosai itakuwa NURU sbd tasabane da bawa meryam abinci abaki duk da tafara girma shiyasa ko yanzu tabawa farhat din musamman dataga gatan da farhat takedashi ko kwatan rabinshi Meryam batada to ai Bata abinci abaki kaman dolene ma.

Bayan tafiyan farhat makaranta saita koma daki ta zauna zaman zugum tareda fadawa tunanin rayuwarta,
Ko atunani da mafarki Bata taba kawo rayuwarta zata juya kaman haka ba daga negestati yanzu Kuma Ana maganar bauta kokuma tace Reno har wata qasa.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda miqewa ta nufa toilet din afia din wanda badan 'yan watan nin data diba a delah ba kafin zuwanta Nan da Babu ta yanda zata iya amfani da wasu abubuwan wanka takeson Yi Amma takasa Yi sbd kada tafara jiqa toilet din AFIA Bata tashi tayi wanka ba wata qila batason wani yafara jiqa Mata toilet Dan itama a gidansu kusan haka take batajin dadin wanka idan wani yafara shiga ya jiqa bayi shiyasa kullum itake rigan kowa wanka a gidansu.

Dawowa tayi ta zauna daga Nan zaune wani baccin ya Dan dauketa sai guraren goma da rabi da AFIA ta tashi motsin shirinta yasata tashi itama tana bude ido ta tashi zaune ahankali tareda bude Baki cikin sanyin muryarta tacewa afia"

Aderiki (barka da tashi/good morning)

Kallonta AFIA ta juyo tayi tareda sakin murmushi tana qarasa Sanya dogon blue jean ajikinta tace"

Morning lewa(beautiful/kyakkyawa)

Shiru NURUn tayi tareda sakin murmushin yaqen dole sbd lewa din kawai tasani batasan meye dayar kalmar ba.

Gane batada ilimin turanci ko kadan yasa AFIA murmusawa cikin Yar hausar amhara da Bata gwanewa ba tacewa NURUn tayi wanka ta shirya suje cin abinci a dining.

Dama jira take ta miqe ta nufi toilet din tashige tareda rufowa tana sauke ajiyar zuciya.
Tana jimawa a wanka Amma dai yau ta taqaita kokuma tace daga yanzu zata ringa taqaitawa sbd yanxu ba Kamar gidansu bane datake cikin gatanta agaban iyayenta Nan Kuma a qarqashin ikon yara ma take sai abinda aka cemata tayi.

Doguwar riga purple tasaka sai qyallin sequence take ta nade gashinta da gyalen rigar ta daurasa kaman dankwali sbd cikar gashinta yasa tafi son daura gyale akan yafawa sosai tayi kyawunta duk da Bata kwalliya Sam batama taba yiba suka fito dining tana gefen afia din suka zauna Koda Fana tasake tamabayarta abinda zataci batasan mezatace ba afia ce tace kawai akawo Mata boiled veggies da kwai sai ruwan tea dinsu na gado wato bitter lemon tea me condensed milk da Zuma.

Babu Wanda yasamu damar cin abinci agidan Saida sukaci tukuna kowa yakeda damar karyawa Dan haka suna gamawa afia tayiwa NURU bankwana ta wuce school.

Yini NURU tayi adaki a kwance daga juyi sai tunani sai bacci har lokacin dawowarsu yayi farhat tafara dawowa Wanda yasa kadaicin NURU rayuwa ta jata dakinta acan ta tayata tubewa tayi wanka ta tayata shiryawa suna fitowa daga dakin AFIA na dawowa ganinsu tare yasata Dan Jin dadin ganin walwalar farhat Dan haka tace su jirata itama tayo wanka suci abinci.

Tare sukaci abinci farhat na zaune gefen NURU kusan ko yanzu abaki take Bata abincin Koda suka gama janta farhat tayi zuwa dakinta sbd tanada drowings dazatayi tana neman abokin dazai tayata iccen mangwaro akace ta zano Nan suka baje NURU na tayata cikin nutsuwa.

Sunfara Jan kwanaki da zuwansu jekadi tasaka ido sosai akan zaman NURU duk da dama ta yarda da NURUn nada natsuwar da kowa zaiso zama da ita musamman yanda su afian suka jata ajiki sosai Dan kuwa afia Jin take kaman tasamu babban aminiya yanzu qarin qaunarta da NURU shine yanda take tsananin qaunar farhat take kulawa da ita Dan kuwa yanzu kusan itace ke Shirin farhat na zuwa makaranta.

Ta bangare daya ita kanta AFIA yanzu kusan komai fadawa NURUn takeyi Bata iya riqe bakinta idan suna zaune Jin takeyi kaman ta amayo Mata dukkanin damuwar data shiga da yanda iyayenta suka rabu Amma tana riqe kanta sbd sirrin iyayentane saidai kusan duk wani abu yanzu NURU tasani akansu musamman labarin dad dinsu da tsawon lokacin Nan bai dawoba saidai kullum suna waya dashi bama Kamar farhat da yagama haddace sunan lewa abakinta Dan qiri qiri suka maida sunanta lewa.

Abu dayane matsalarsu da ita gurin fira rigima sukesha sbd batajin turanci ko kadan sukuma yaren bai kamasu ba shiyasa idan suna fira sukeshan dariya sbd wani abin kafin tagane kwatancen kurame sukeyi da ita.

Ganin komai inshallah yayi yasa jekadi tattarawa Takoma tabar NURU da kewa saidai tayi Mata alqawarin ringa zuwa dubo Mata iyayenta akai akai tana bugowa tafada Mata.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899[9/6, 6:12 PM] Anty Rabi'at: *_Mamuhgee 9_*
Sun Dade a can Saida afia taduba agogo taga lokacin fitowan dad dinsu yayi yasata aje karatun tana kallon NURU data dage tana kallon dabbobin duniya wainda wasu batama taba sanin akwaiba bare ganinsu sai take kallon abin cikeda mamaki da burgewa fuskarta ma ta nuna hakan
Afia ta dafa littafin tana cewa"

Ma'am Muje saikuma gobe mudawo ki Dora daga inda Kika tsaya.

Murmushi NURU tasake tana cewa"

Inason sanin sunayensu duka.

Karki damu ko farhat zata koya wannan yanxu dai muje inajin yunwa.

Fitowa sukayi NURU nasake wanyewa da qaton gidan sbd saiyau tun zuwanta ta fito ta zagaya cikinsa AFIA kuwa sai sake Mata bayanin komai takeyi tana nunnuna Mata.

Suna shigowa MALEEK UBAYD na gab da shigewa dining room tareda farhat dake gefensa cikin sauri AFIA tace"

Dad NURU na gaidasheka.

Jin haka yasa NURU saurin durqusawa muryarta na rawa tace"

Barka da fitowa cikin yarensu sbd a rikice take batasanma wane kalar yare shi yakejiba ko yake amfani dashi.
Chapter 10 · 0% Book details