← Book details Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 79

Sashe 76

Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR 6 & 6 Agaban dankareren gidan dayay girman wani kauyen security guards suka taresu ina zasu, saukar da glass down akayi Widad ta leko suna ganinta duk mutuwan tsaye sukayi sunma kasa kiran sunanta tsabagen shock itama haka sai kawai suka kwasa dagudu sukai ciki suka budemusu gate suka shiga ciki, suna shiga ciki kafinma motar tai parking tabude marfin motar ta diro kasa, wani irin ihu ta kwala. "Abyyyyyyy, Abyyyyyyy, Abyyyyyyy!!!!!" babu inda baya amsa muryanta agidan nasu. Kaman amafarki yana kwance kan katafaren gadonshi ga karin ruwan da akemai yay busy busu, gumunshi so scatterd ba kyan gani ga uban furfura yana sanye da farin jallabiya da rawani akanshi as usual, Amah nakusa dashi tana shafa kanshi itama takode sosai kaman ba itaba, daidai Umm tabude kofar dakin ta shigo rikeda madara a cup sabida yace madara zaisha sukaji muryan Widad dukansu, Aby dake bacci wani irin zabura yayi yana bude ido yace "Widad!" shafa kanshi Amah tayi tace "mafarki kayi amman nima naji mafarki dan naji muryanta wlh, ga madaran kanan ankawo" sake kwalamai kira Widad tayi baisan lokacin daya zabura ya sauka daga kan gadonba yana cisge karin ruwan hannunshi yay wajen window dakinshi dakenan arufe Amah biyeda shi, wani irin bude window glass din yayi sukai wani irin kara da saida suma su Waleed dake tsaye charko charko atsakar gidan suka dago kansu dan suga meyay kara haka, daidai Aby ya yaye labulen ya kallo tsakar gidan, hada ido yayi da yarshi tilo aduniya Widad tana sanye da bakar doguwan riga, yatsanta tasa ahankali tai pointing fuskar Aby dayamata tsufa sosai kaman bashiba bakinta har rawa yake tace "A........bb.....by" shima kasa magana yayi yace "Wi.....d...." ganin yakasa kiran sunan yasa yajuya dagudu yay hanyar kofa itama Widad takwasa dagudu tai flat dinsu Waleed yabita dan baison yanda take gudun nan karamin cikin dake barazanar fita gareta, a daidai stairs tahadu da Aby tsayawa tayi chak wasu irin hawaye na gangaromata tace "Aby" ahankali yace "Widad" dawani irin gudu tai wani uban tsalle ta dane jikinshi ta kankameshi tafashe dawani mahaukacin kuka daidai Amah tafito tana dogara sanda, tsabagen sauri turgudewa tayi zata fadi Waleed baisan lokacin dayabi ta gefen su ba yasa hannunshi tafado kanshi yatareta, tsabagen dadi rungume Waleed din tayi tamai kiss a kumatu sanan ta tashi ta rungume Aby da Widad dukansu atare Waleed ya tsaya yana kallonsu ajikin benen, wata mata yagani itama fara tana sanye da doguwan riga tafito fuskarta kini kini kaman zata mutu tana kallonsu Aby tazo tagabanshi tawuce bayanta ya kalla tana rikeda wata wuka, daidai takai wajensu ta daga wukan kenan Waleed yawani irin fizge hannunta tareda murdewa ihu Umm tayi da sauri su Aby da Amah da Widad suak juyo, cikeda masifa cikin harshen larabci Umm tace "barni na kashe wanan annobar yarinyar da sabida ita nakasa samin soyayya da kudin mijina hakama y'ata takasa samun both of them, I make sure nama Widad abinda zaisa bazata taba dawowa ba, ubanta bazai taba ganinta ba, amman ya akayi mayyar tadawo, su wayeku, ka sakenmun hannu" cikin harshen larabci Waleed yace "so you are the famous Umm" balle hannunta yayi ras wukar yafadi akasa itama tazube akasa tana ihu, ahankali Aby yaciro wayarshi babban police din garin takura duk suna tsaye ko 5min ba'ayiba polisawa suka cika gidan abunku da babban mutum yakirasu akazo aka dauki statement dinsu sanan akai gaba da Umm tana kuka, sai a lokacin aka dan natsu Aby yace a zazzauna sanan ma'aikatan gidan suka shiga sintirin kawo musu abinci da abubuwan kwalama Widad na manne da mahaifinta daya kira Family su Ahmad dan Ahmad har yar hauka saida yayi, kafin kace me Family su Ahmad sun shigo, tunda ya shigo Waleed ke kallon Ahmad din dake sanye da kayan larabawan idanunshi kurr kan Widad dake mai wani irin kallon tsantsan so, tashi tayi ahankali zata rungume shi wani irin tsawa Waleed yadaka mata dahar saida su Aby suka kallesu yace "don't hug him Widad!" chak ta tsaya tana kallonshi kaman yanda Ahmad shima ya tsaya yana kallonshi, tashi Waleed yayi kaman wanda yasoma tabuwa yaje har inda Widad din take azuciye yasa hannunshi yakamata sanan yajawota kusadashi yana kallon fuskar Ahmad din babu ko alamun tsoro ko kunya atattare dashi yace "she is my wife Ahmad" shima Ahmad cikin fushi da tsantsan kishi yace "Widad can never be your wife, nobody can become can husband other than me, koma zata auri wani Widad can never marry a man from a Different world daba namuba" cikin wani irin yanayi na jarumta Waleed yasakin mai murmushi yace "let's just say TWO DIFFERENT WORLD meet" cikin fushi sosai Ahmad yanuna mai yatsa cikin harshen turenci yace "DUNIYA BIYU MABANBANTA bazasu taba iya haduwa ba, kataba ganin inda ruwa da desert suka hadu? Ai ruwa daban ne hakama desert, ka yarda dani inna fadamaka mu LARABAWA BAMAYI DAWATA KABILAR" yatsa Waleed yanuna mai yace "ka rubuta ka ijiye daga kaina LARABAWA ZASU KOMAYI DA KOWACE KABILAR" Ahmad zai kara magana Widad ta fizge hannunta daga na Waleed takoma bangaren Ahmad sanan tanuna Waleed da yatsa cikin harshen turenci da ta lura shine yaren dasuke mata tace "listen Dr, your Mom told me you were the one that helped me kamin komi, and I am grateful karubuta mana konawa ka kashemin Aby zai biyaku, Ahmad is my husband, shinake so tun ina yarinya, and nothing and nobody can change that, tayaya kake tunanin zanma iya auren wani daga chan wata duniyar? That's not even possible, please stop calling me your wife, I don't know know and I can never be your wife" wani irin murmushi Ahmad yayi zaiyi magana Aby yadaka musu tsawa yace "quiet" shiru sukayi sanan yanuna ma kowa wajen zama, duk zama akayi sanan ya kalli Widad yace "Widad haka nabaki tarbiya? Irin tarbiyan dana miki kenan? Mutumin daya taimaka miki kikema wanan tijaran"? Saukar da kanta kasa tayi sanan Aby ya kalli Ahmad da kanshi ke kasa yace "Ahmad ko kunyan mu iyaye dake nan wajen bakayiba, kai mutum ne ai da yakamata kazama na farko dazaka godema bawan Allah nan daya taimaki Widad yadawo mana ita cikin koshin lafiya amman kake gayamai DUNIYA BIYU MABANBANTA basa aiki, inda basa aiki aida basune zasu dawo mana da Widad ba da saidai yan duniyan mu larabawa su taimaketa su dawo da ita" dan tsaki Aby yaja sanan ya kalli Uncle wanda ya lura shine babba sosai cikinsu yahade hannayenshi biyu yace "please tuba suke kuma yaranmu hakuri" murmushi Uncle yayi yace "bakomi" anatse Aby yace "kaman yanda kuka gani nine mahaifin Widad, wanan kuma Mahaifiyata ce, kakan Widad" ya nuna mahaifin Ahmad yace "wanan surukina ne kuma abokin kasuwan cina mahaifin Ahmad yaron da Widad zata aura" wani irin ajiyan zuciya Waleed yasauke da saida kowa ya kallai adakin, saikuma Aby yacigaba yace "ranan bikinsu ana gab da za'a daura aurensu aka nemi Widad aka rasa" shiru yayi kaman wanda ke tuna ranan sanan yay murmushi mai kama dana ciwo yace "anyway I don't want to remember wat happen that day, I dont want to remember wat I and my Mum went through dakowa namu it was terrible experience anyway Alhamdulillah, baya yawuce let's just face the present banda hakama Allah ya riga yatona asirinta, Allah kuma yataimaken ban maida komi nawa ma sunan yarta datai aureba yanzu haka Sabeeha na gidan mijinta suna Dubai ma tabishi yin wani aiki, komi yawuce, ko zaku iya sanar damu yakuka sami y'ata maisa danku ke kiranta da matar shi" wani irin zama Uncle ya gyara sanan yashiga basu labari tiryan tiryan kafin yagama tsaf yabude yar briefcase din hannunshi yaciro marriage certificate dinsu yabama Aby, sanan yakarake da "yanzu haka Widad na dauke da juna biyu na wata daya dayan kwanaki"! Shiru kakejin dakin kaman ruwa ya cinyesu. Iyayen Ahmad kasa ko motsi yayi, Ahmad idanunshi sukai ja dan wanan ake cewa murna da bakin ciki duka atare, ga murnan ganinta gakuma bakin cikin wanan bakin labarin dayakeji yanzu, Widad wani irin kuka tafashe dashi tafada jikin Amah tana kuka, shi karan kanshi Aby da takardan ke hannunshi na certificate kasa magana yayi, ahankali yace "aure ciki!" gabaki dayan labarin ya diran musu as a shock ne, ganin duk yanayin dasuke ciki yasa Uncle yay murmushi yace "Alhaji mudai yanzu zamu tafi zamu koma masaukin mu, zamu baku lokaci kuyi tunani dan bazan boyemaka ba daga danmu har yarku suna bala'in son junansu sosai, sai yanzu data farfado ne but kubata lokaci karku yanke hukunci da wuri barinma wanan babban rabo haka daya gitta tsakaninsu na ciki, kubarta ta dawo hayyacinta da kyau komi daya sameta bayan tai losing memory din yadawo mata tasan waye mijinta Waleed, tagane shi sarai kafin ta yanke hukunci" tashi dukansu sukayi suka sake gaggaisawa da Aby da iyayen Ahmad suka rakosu har tsakar gida suka shiga motocin su sanan suka tafi suka barsu cikin tsantsan tashin hankali. Koda suka kai gida, kasa komi Waleed yayi, after seeing her family and everthing he's so scared of losing her, yasan larabawa tun mahaifinshi nada rai suke yawan zuwa garuruwan larabawa saisama yadan iya larabci, one thing he knows about them shine basa bama wani yare yaransu, basa auren bare, yisu yisu suke aurensu, balle ma shi dayake daga wata duniya daban chan Nigeria tayaya DUNIYA BIYU MABANBANTA zasu hadu harsuyi tarayya irin ta aure dasu? Dafa shi Uncle yayi yace "trust me everything is gonna work out fine" gyadama Uncle kai yayi yadaga kai yana kallon yanda Ammi ke kallonshi, cool smile tasakinmai sanan tashiga kitchen. _Bayan kwana bakwai_ Yau satinsu daya chur kenan agarin amman haryau basu sake kiransu ba, basu kuma sake kiransu ba, ga Uncle yahana su zuwa sujira kiransu acewansu, wasa wasa Waleed har neman xarewa yake, gani yake kaman sun kwacemai matarshi kenan, baya iyacin abinci baya iya komi baida aiki saidai ya shige daki ya rungume kayanta. Yaudai kaman kullum ganin yana neman rasa gane kanshi yasa ya shirya tsaf, yafito compound mota, mota daya yadauka cikin motocin su direban yajashi har zuwa gidansu Widad, ana ganinsu ba'a hanasu shiga gidan ba, shigasukayi direba yay parking bude motar yayi ahankali yafito yay falonsu,
Chapter 76 · 0% Book details