← Book details Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 79

Sashe 18

Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_ M SHAKUR 1 _*This novel is 500 Fanmily* _How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD_ _zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA_ FREE PAGE _*MOROCCO _Hausawa sunce sannu sannu bata hana zuwa! Saidai......_ Yau babban ranace ga Ahmad, Widad da iyayensu dan babu wanda ya runtsa cikin dare dan ayau zasu aurar da yaransu da misalin karfe sha'adaya da rabi a katafaren mansion din gidan mahaifinta, inda Family mijin zasuzo ahadu ayi wasu shagulgula da wasanni naban mamaki kafin a daura auren sanan kuma a cigaba da daurin auren. Gidansu Widad duk inda kasaka kafarka mutane ne, ko bikin yar shugaban kasan morroco za'ayi albarka, mutane kaman kudaje sabida mahaifinta mutumne mai farin jini da taimako, Babanta yadauko mutane da dama, tun daga kan masu mata cultural gyaran jikinsu da wankin kafa da hannu, sanan gyaran kai, ga kayan dazata saka yau tai amfani dasu ancire matasu tsaf an ware masu hotuna nata dukansu, kayanta da komi dazatai amfani dasu designers ne da aka kashema zunzurutun kudi kaman baza'a mutuba, batai aureba ma mahaifinta yakashe mata dukiyanshi balle yanzu da dalili auranta, ai sai inda karfinshi yakare. Tun bayan tai sallan asuba tana sanye da plain dogayen rigunan nan nasu na bacci ta nannada gyale aka hannunta rikeda charbi tafito sadaf sadaf tahau rooftop din gidansu, zama tayi a spot dinta ta tankwashe kafa tana kallon sama, yan turarin nan dake fitowa da asuba hade da wata ta kalla, takai kusan minti 10 ahaka sanan cikin muryanta mai dadin sauraro tace "Mahaifiyata"! saikuma tai shiru ta saukar da kanta tadan dau lokaci ahaka sanan takara dagokai tace "Ummy I know duk inda kike kina janna ne da izinin Allah, and I am sure you've been watching over me, kafin kimutu I promised you da I will be a good hard-working young lady that follows her dream, a gurl who let her mind guides her not her heart, you always say this words to me that I called Ummy golden words _"Widad this heart is bias, don't let it rule you, let the mind rule your soul"_ tai shiru tareda dan share hawayen daya zubomata dan batason tai kuka yau ranan bikinta tace "Dearest Ummy, innace akwai ranan dabanyi tunanin ki ba nai karya, I think of you everyday, I miss abincin dakike min ki ijiyemin a kula inadawo daga makarantan sanawiyya, I miss kamshin ki, I miss komi naki saisa Ummy ban fadami ma Aby ba but I promise myself I will dress in your cloth ayau ranan bikina, Ummy I miss you so.....m..uch" muryanta yafara rawa tace "mutum bazai taba gane maraicin uwaba sai inhar kai rayuwa da ita, ka girma da ita, kasaba da ita thinking she will be with you har karshen rayuwanka rana daya kwatsam ta rasu! Kafara rayuwa bata aranan zakasan cewan rayuwanka tai gibin da babu hakorin dazai cikeshi, I miss you so much Ummy" tafashe da kuka nakaman 1min saikuma ta share fuskanta tass tai murmushi tace "sorry Ummy I promise bazan kara kuka ba but ina tayi ko kiyakuri" taidan shiru tanadan cizan lips dinta kafin ahankali tadaura hannunta kan kirji tace "anytime nahau kan rooftop dinan sabida kene dan yana tunamin dake, I remember lokacin tun ina yar karaman yarinya koda fita nayi nadawo nan zan hawo da gudu inbangan kiba ina kuma zuwa zan ganki kokina zaune kina kallon gari kokuma kina kwaba kullin flat bread dazaki mana, bayan kin rasu duk in nazo wajen nan hakanan I feel your presence anan hala sabida is your favourite place ne kema saisa nike jin hakan" tadan numfasa tace "Ummy today mark a day da I will embark on a new journey of life, jiya ko runtsawa idanuna basuyiba I am so restless, I am so so scared Ummy, banda sukuni tun jiya da daddare haryau" sama tasake kallo tace "Ummy haka kowace mace kejine ranan bikinta?" saukar da kanta tayi tareda dan murmushi tace "gabana nata faduwa Ummy but I know duk tension din bikin ne da rashin ki anan nasan inda kinanan dakinyi guiding dina, but kinsan wani abu Ummu?" taidan murmushi tace "karkiji komi cus am surrounded with so much love, Aby, Amah, Ahmad gakuma Sabeeha Ummy you need to see yanda take taimakamin da komida nikeso dudda mahaifiyarta batasonmu tare but bata damuba Sabeeha has been so so good to me lately" tai murmushi tace "and I am grateful for everything, Ummy I come to ask a favour from you" tai murmushin nan gwanin ban sha'awa tace "just watch over me kinji, always be with me nasan inhar u are with me babu abinda zai samen, I love you Ummy, Allah ubangiji ya jikanki ya gafarta miki, Allah yakai haske kabarinki Allah yasa kin huta yasa aljanna ce makomarki" da Ameen ta amsa ita kadai zata sake magana aka kwala mata kira. "Widad" da sauri ta juyo Sabeeha ce tacigayu cikin wata jada bakin blouse na mata, tace "wai me hadinki da rooftop ne kinsan karfe nawa kuwa? Kowa na gida ya shirya ke kinanan Amarya har yanzu sanye da kayan bacci, karfe sha daya fa za'a daura yanzu is 20min after 9" ware idanu Widad tayi sai yanzu ma ta lura gari yawaye sosai ita datake nan tun duhun asuba, da sauri ta mike Sabeeha tace "yi sauri zomuje ki shirya" gyadamata kai tayi tace "to, Sabeeha kinyi kyau" shafa kumatun ta Sabeeha tayi tace "kema haka kinyi kyau dudda ai bakiyi kwalliyan ba" dakin Amah suka karasa agurguje akasa tai bayi tai wanka tafito sanye da bathrub, Amah ta watsa mata harara tace "yarinya sai shegen nawa keda yakamata ki riga kowa shiryawa kece ta karshi jibi goma saura" turobaki tayi ashagwabe tace "Amah wai banace kiyakuri ba, aifa bansan lokaci yawuce hakabane fa ko Sabeeha?" da sauri Sabeeha tace "Amah bafa tasani bane kuma tabaki hakuri kinki kodai kishi kike zata kwacemiki Ahmad dinki" fashewa akai da dariya harda masuma Widad din makeup, sanda Amah ta shiga nema hakan yasa aguje Sabeeha tafita daga dakin tana dariya, Widad kuma ta gimtse dariyanta kafin Amah ta rafka mata sandar. Wuraren 11 aka gama shiryata tsaf cikin lebsa r'batia blue(sunan kayan), yanada mugun kyau kayan dogon rigan ne daya amsheta, kalan blue da fari, kunnenta yaji hadaddun yan kunnaye hannayenta da warwarori na zinare, farin gyalen amare Amah ta dauramata kan saman gashinta da aka gyara tsaf sanan tajuyo tamata kiss cikeda so tace "zauna anan dan Amarya bata fitowa akafa, bari naje chan tsakar gida wajen su babanki, yanzun nan neggafa asisitance zasuzo afitar dake, I love you" murmushi tasakin ma Amah tace "jazakillah Amah" gyadamata kai Amah tayi tana dogara sandarta tafita, babu kowa aciki kowa na waje dan nanne ake bikin, duk yan ciki sun fita sabida Aby na raba kyauta. Tana zaune shiru adaki tana kallon kanta a madubi ganin kyawun datayi yay yawa sai kewan Aby take sabida tun safe bataga Aby ba gashi aka'ida Amarya bata gani iyayen ta sai an fitar da ita acikin (amaria) a kaita wajen daurin auren dan Amarya bata tafiya da kafanta, tana cikin yan tunane tunane ta akai knocking kofar dakinsu faduwa taji gabanta yayi da sauri tajuyo tareda bada izinin shigowa wani ma'aikacin gidansu ne ya shigo yana sanye cikin wani uniform blue da purple, cikeda girmamawa yace "ga amaria ne abakin kofa anbamu izini mufito dake baya, Aby nason magana dake kafin mukaiki wajen daurin auren, motarshi na wajen" murmushi tayi tace "Aby" gyadamata kai yayi yace "bismillahi" mikewa tayi ahankali cikin blue embroidered dress din lebsa r'batia tasake kallon kanta amadubi sanan ahankali tafara tafiya, bude mata kofa ma'aikacin yayi tafita anan taga maza guda shida, dama a adaltance maza bakwai da ake kirada negaffa assistance ke daukan Amarya bayan ta shiga cikin amaria su daura hannayen abin akan kafadarsu sukaita chan wajen daurin auren, bude mata kofan sukayi ta tsugunna ahankali tashiga ciki ta zauna tare da tattare kasan gown dinta, cike da girmamawa yace "kin zauna da kyau? Are you comfortable?" gyadamai kai tayi tace "Alhamdulillah thank you" maida kofar yayi yarufe sanan yasauke labulen daya rufe kofan tabaya da akama ado ta yanda babu wanda zai iya hango amarya, daukan kafafuwan sukayi suka dagata sama suka daura akan kafadunsu instead of suyi tsakar gida sai sukai kitchen da ita, bude kofan bayan kitchen din sukayi suka fice babu kowa ata wurin, sanan suka cigaba da tafiya sukai gate din dake ta wurin bude gatedin sukayi suka fita, babu kowa ta wajen sabida daman Babanta yasai filin wajen babuma mutane sai wata katuwar bakar mota dake wajen, karasawa sukayi har gaban motan sanan suka sauketa, suka bude tafito ahankali, kallon wajen tayi sanan ta kalli daya daga cikin motar mahaifinta data gani awurin a pake murmushi tayi tace "Aby na ciki?" gyadamata kai sukayi, ahankali tasa hannunta tabude bayan motan daba kowa zata shiga taji saukan wani abu kaman tsumma a bakinta da hancinta within 3 good secs dip kanta yadauke, da sauri suka rirrike ta suka shigada ita cikin motan sanan wanda yazo yakirata yama direban da fuskarshi ke sanye da mask magana "yi sauri kutafi, yanzu mu zamuje daukota adaki as scheduled kumuje yara" da gudu suka dauki amaria suka tafi shikuma direban yaja motan dawani fitinannen gudu yabar anguwan. Wanan kenan!!! Ahankali take bude idanunta sabida kanta dataji yamata wani irin mahaukacin nauyi kaman an dauramata buhun simenti, jikinta namata nauyi, irin nauyin nan da jikinka kakeji yamaka bayan alluran kashe zafin ciwo ya saki, wani irin mahaukacin iska dataji yana kadata yasa tabude idanunta da kyau tangaran tana kallon inda take data kasa gane inane, hasken datake gani yasa tajuyar da kanta saitin hasken, kofa tagani abude wani wagagegen kofa saikuma fili haka datake hangowa na kasa bayan clean filin kuma bishiyoyi ne da shukoki take hangowa, cigaba dabin filin tayi da kallo taga jirage ne kaman irin jiragen airforce dinan amman wanan bana airforce bane guda uku, da duka karfinta ta daddage ta lallaba ta tashi zaune tana dafa fuskanta tana kara bude idanunta dakyau kafin da sauri
Chapter 18 · 0% Book details