Sashe 50
Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
cool voice yace "Ammi aure nakeson nakara, please" yay dan shiru sanan yace "Ammi I don't wanna go into details dake but please Ammi aure nakeson nakara ki barni, at least my first marriage namiki abinda kikeso yanzu ki barni na auri wacce nakeso kinji" cikin dan kakkausan murya Ammi tace "Waleed do you even realise you are just 28 ko 29yrz bakakai ba dahar zaka ijiye mata biyu, angayamaka kanada karfin ijiye mata biyune" cikin yanayin dan fushi yace "Ammi nifa namiji ne shine kuma banda karfin managing two wives, Ammi I love her kinji, kina hanani wlh zan iya mutuwa" wani irin kallo tamai irin na yaronan lafiyanka kalau kuwa, hannunshi yamika ahankali yakama hannunta sanan ya shiga bata labarin komi na Widad har zuwa abinda yasameta jiya da daddare, sosai jikin Ammi yay sanyi, Waleed yace "Ammi what if kece kika haifeta, can you imaging me in this life datake ai zakizo ataimaken ko, Ammi that girl needs care, banda haka ina sonta Ammi so sosai, please Ammi inhar kinasona dagaske ki yarda kika yarda ni kinmin komi dan girman Allah Ammi" yay maganan yana rokonta, ganin seriousness din dake idanunshi da tsantsan sonta, dakuma tausayin yarinyar dataji tanaji yasa ta sauke ijiyan zuciya, ahankali tace "Waleed inhar bantayaka son abinda ka kawo kace kana soba menayi, kawai kaga ukuba da dama ne ciki harda Arham, karyazo Arham yaturo yarinyar tama wani abu, but tunda kana sonta shikenan zan kira Mom takawo yarinyar nan itada Ma'u duk saisu zauna anan inyaso saita dinga zuwa islamiyyan su Ma'u, Wata daya za'a saka shima sainai magana da Baffan ka kome yace haka za'ayi" wani irin fadawa jikin Ammi yayi sanan ya manna mata kiss a goshi yace "I love you Ammi thank you" ahankali Ammi tace "but da sharadi" da sauri ya gyara zama, Ammi tace "banson kana zaman gida, zakaje kadinga min managing company na for now harsai an maidamaka da gidan marayun ka, sanan zaka koma chan gidanka, kaje ka gyara inda zaka gyara amaryanka, inhar Amaryanka na nan bazaka dinga zuwamin gida anyhow ba, kaida ka kara ganinta dagayau sai in ankaita gidanka" da sauri yace "na yarda Ammi" dan acewanshi ganinta inhar tazo gidan Ammi abu mai sauki ne, murmushi Ammi tayi tace "kasami lokaci kaje kasami Ilham kafadi mata sanan kamata kayan fitar kishiya, kazama mai adalci" dan shiru yayi yana tunani sanan yace "Ammi is a simple wedding, banson any taro, zan mata kayanta na ijiye mata inta dawo daga wanka I will te her Ammi" shiru Ammi tayi tace "tadaiji daga bakinka, ina zuwa bari naduba yan aikina nasasu min aiki" tai maganan tana tashi daga kan kujera tafita daga dakin, wani irin tsalle yayi kaman dan yaro yafada gadon Ammi, he never knew haka akeji idan zaka auri love of your life, all this excitement baijisu ba dazai auri Ilham ba sai yanzu, da Ammi ta yarda kaman an bashi kyautan kujeran makka. Washe garin ranan Mom da Asma'u da Widad sukazo Waleed baya gida dan tun safe Ammi takadashi company ta, sosai Ammi tadinga kallo Widad da saida Mom tasata ta gaida Ammi ta gaidata sanan takoma wajen Asma'u dake zubamata uban surutu kaman gidan radio, sun dade zaune afalon sanan Ammi ta tashi tai sama Mom tabita, dakin Ammi suka shiga Mom biyeda ita, zama Ammi tayi kan gadon Mom ma tazauna tace "kinga yarinyar ko? Batada matsala Adda, komi sai wanda ka koyamata zatayi and nalura she is very sharp, yau Asma'u na koya mata karatun Al'qur'ani tacigaba dayi da kyau, wlh dadin muryanta saida yasa nafito daga dakina da asuban nan na shigo dakinsu, kinga abubuwan data iya kuwa, magana ne kawai bata waniyi saida Asma'u, but she is good Adda" ajiyan zuciya Ammi ta sauke tace "indai Waleed na sonta shikenan, yarinyar namin yanayi da...." Ammi tai shiru bata karasa maganan ba da sauri Mom tace "dawa take miki yanayi?" dan yatsine fuska Ammi tayi tace "never mind kawai raina ke kirfamin hakan, but basa yanayi, zan baki kwangilan akwatin ta kinji afara shirye shirye, kima mai gyaran jikin nan magana" gyadamata kai Mom tayi tace "angama Adda" sosai suka dade sai plan suke, sai wuraren magrib ta tafi sukuma Ammi tabasu hadadden daki. Wasa Wasa lokaci ke tafiya, time to time Waleed ke zuwa yaduba Ilham da little Arham dudda har yanzu bai gayamata cewan zaiyi aureba, yayinda rabonshi da Widad tun ranan dayabar gidan Mom, babu yan dabarun dabaiyiba akan zai ganta amman Ammi tahana, Widad sai gyara takesha, yanzu tana dan hira sosai, ta mugun sabawa da Asma'u, akwai randa Asma'u taje gida tadawo batajeda Widad ba sabida shegen ciwon maran datake yi dahar saida Ammi tasa aka kawo mata maganin ciwon mara tasha, Asma'u nafita tadinga rusa uban kuka Ammi nata kallonta, kaman ranan tafara ganin yarinyar, charisma din yarinyar na nuna kaman yar babban gidace sanan tanada shagwaba, da kyar ta samu ta lallasheta ajikin Ammi tai bacci. Sannu sannu ance bata hana zuwa, yau dududu bikin Waleed da Widad saura 5days yau, dudda wedding din low-key wedding ne bai hana family fara shirye shirye ba, Ilham itama anata bangaren tanata shirye shiryen fitan arba'in. Wanan kenan ********** Sosai Ilham tawani irin rame tai duhu taki kyau sabida hankalinta ba'a kwance yakeba, yawanci ba'a kawowa wani abune ko Mummy cewa take tsotso ne dan Arham ya iyashan nono, baya bacci in baiji nono abakinshi ba, nan ko tunanin Arham ne ya addabeta, the thought of cewa ta haifan ma Arham yaro amman haryau bai tako ko yama turo mata sako kan cewa yaya danshi ko Yaya takeba abin is killing her, yanzu Arham baya sonta ne, saida ta cuceta ya ciccita ya dirka mata ciki sanan zai mata haka, saitahau kuka. Yau tana zaune da safe a dakinta ta tabude account dinta tana kallon kudin ciki tanada 17m, kudaden sa Waleed yabata ne, sanan da wanda tasamu ranan suna daga yan uwa dakuma su Ammi dan sun aikoma ta da kyauta mai tsada, wani zuciyane yace "kiturama Arham, kina turamai zaku shirya" tunanin hakan yasa da sauri ta shiga mobile dinta ta turamai kudi dan tariga tai saving account dinshi a beneficiary, turamai duka kudin tayi saikuma ta shiga message ta aikamai da sako tace "inkaga alert ka kirani" ko minti uku ba'a daukaba saiga kiran Arham she thought mafarki take dawani irin gudu ta dauka tace "Hello blood, kaine ko mafarki nake" cikin wata irin shakakkiyar murya yace "Maman Arham matan Arham" wani irin fashewa da kuka tayi sosai dan she couldn't hold back her emotions, tace "mena maka Arham? Na haihu koka neman, at least kobaka kira danni ba saika kira dan yaronka ko, mena maka yau duka duka saura 5days my fita daga arba'in" tafashe da kuka sosai, yatsine fuska yayi sanan yace "hey common stop crying wife, kinsan menake so dake" girgiza mai kai tayi tace "a'a" yace "kidau mota zan miki text din address din gidan marayuna, come with my son naganshi, I miss you badly, hope baki wanan kazamin jinin na wayanda suka haihu, ya tsaya"? Da sauri ta gyadamai kai tace "eh shekaran jiya ya tsaya yau 2days" ahankali yace "good, hurry up and come to" gyadamai kai tayi tace "to" katse wayan yayi saiga address ya shigo da sauri ta tashi, magungunan gyaran jikin da Mummy ta hadamata ta deddeba tasha sanan taciro wasu hadaddun kaya lace tasaka, dama yaronta ashirye yake tsaf, tadau wayanta da car key da sabon babysitter na mota da aka bata cikin gift tafito dan yaron na wajen Mummy afalo, taba fara saukowa Mummy tace "ke kodai mafarki kikayi kinyi arba'in da sauran kwanaki fa" murmushi tayi tace "Mummy wlh nagaji da zaman gida, gidansu Salima zani nariga na tambayi baban Arham ya yarda, please Mummy karki hanani dan Allah bazan dadeba" hararan ta Mummy tayi tace "kin riga kin fadima mijinki daman yace kije ina na isa na hanaki yaran zamani" dariya tayi, Mummy ta tashi tace "to direba yakaiki mana" da sauri tace "a'a nidai Mummy dakaina zani, I miss driving wlh" "shikenan Allah tsare muje natayaki sashi a sitter a mota" fita sukayi Mummy ta samata shi itakuma Ilham ta shiga ta kunna motar taja Mummy na daga musu hannu suka fita daga gidan. Kaman zata tashi sama haka take gudu tanayi tana kallon Arham karami tace "kaidan yaron Mamanshi zamuje muga Baba, Baba oyoyo, Baba oyoyo, ka kaso kaga Dady, kace Dady, Dady am coming, am on my way" ta kyalkyace da dariya cikeda farin ciki tace "yarona is excited yau zaiga baban shi for the first time yeeee". _TWO DIFFERENT WORLD_