← Book details Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 79

Sashe 15

Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kai Salima tayi tace "eh suna falo, ke Khadija dama haka Dr naki yake? My God he is damn cute but yanada wulakanci sosai wlh" murmushi amaryan tayi tareda juya idanu tace "don't tell me u expect handsome rich guy mai status nashi yazama kaman all this random guys you use to know on the street? Angaya miki irinsu Mubarak dinki ne? Cheap guys?" ta bushe da dariya mai makeup din itama tafashe da dariya, ganin mocking dinta Ilham keyi yasa Salima ta tashi ko kadan bataji dadin abinda Ilham tamata ba, tasaba da halinta dan sabawa amma ta tsani tacimata fuska agaban wasu, ganin ta tashi zata fita batare data cemusu komiba yasa da sauri Ilham tace "me haka kekuma daga wasa dadina dake saurin fushi Salima, yakuri to pls dawo kinga fa ke zaki kaini kasa bai kamata na sauka kasa nikadai ba kekuma wai bazaki gama min daurin bane?" da sauri mai makeup din tadauki pin tana sosokewa a ashoken. Dawowa Salima tayi ta tsaya akanta, karasa soke daurin tayi Ilham tamike ta kalli Salima ganin ta daddaure fuska yasa tawani fada jikinta tareda rungumota tace "dalla na face miki sorry please karki damu anjima zan baki labarin Dr kinji ni yanzu kiyakuri dan Allah" yanda duk takaiga fushi saida tai murmushi tace "shikenan" tace "kinga yanda kikai kyau kuwa kaman bakeba Ilham" murmushi tayi tace "yi sauri muje naga Dr dina" hannunta Salima takama sanan tabude kofan suka fita sau daya tasaci kallonshi ta sunnar da kanta kasa ganin bashi kadai bane, shi hankalinshi ma nakan wayan hannunshi yana danne danne yay wani irin kyau da saida taji gabanta yafadi hakanan taji wani kishi yataso mata yanzu duka matan dasuka cika gidan nan su ganshi ahaka, da kyar ta iya ta danne kishin suka cigaba da sauka daga stairs ahankali, Hasim ne da Abdul suka tashi suna murmushi "wow, Amaryan Ya Waleed" karasa sauko da ita Salima tayi tana musu murmushi sanan takaita harkan kujeran da Waleed ke zaune two sitter ta xaunar da ita a gefenshi tace "Dr ga amaryan ka nan nakawo maka yanzu kwa barni nahuta" maganan dayaji yasa yadan dagokai ya kallesu sanan yadauke kai, juyawa Salima tayi tai waving su Hasim tace "bari naje waje" da sauri Abdul yace "bari muma mubiyoki mubama love birds some space" dan dagokai Waleed yayi ya watsa musu harara suka kyalkyace da dariya suka fice abinsu falon yarage dagashi sai Ilham dake zaune kusada shi dukansu sunyi shiru. Almost 5min suna zaune basucema junansu komiba sanin zasu iya kwana ahaka bai cemata kalaba dan tasan magana wuya takemai yasa ahankali tamika hannunta dayasha lalle ta daura kan hannunshi daya ijiye kan laps dinshi ta kama hannun gam, atare suka dagokai suka kalli juna, tasake matse hannunshi dat feels so soft kaman hannun mace smiling, ahankali tace "Dr is our wedding are u not excited? I feel so happy because am getting married to love of my life, I love you so much Dr Waleed Warbai" tai maganan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, dauke kai yayi da sauri he don't really know abinda ma zai cemata, ko 1 single feeling baidashi akanta, ganin baice mata komi ba yasa cikeda son janshi zance tace "waye best friend din naka cikin wayan nan da kazo dasu?" ahankali yace "bayanan, this are my siblings" murmushi tayi tareda lumshe ido tana bala'in son jin yana magana, maganan shi dadi sosai wlh, voice dinshi bala'in dadi, murmushi tayi tace "yana ina shi? Maisa baizo tareda kaiba?" dan dagokai yayi ya kalleta suka hada ido sanan yace "I left him in the office you will see him later" gyadamai kai tayi cikeda sonshi tace "kayi kyau sosai" dauke kai yayi yace "thanks" yadanyi shiru saikuma yace "you look beautiful as well" wani irin cikakken murmushi tasaki cikeda jin dadi sosai tace "nagode Dr" sukai shiru, agogon hannunshi ya kalla sanan yadago kai ya kalleta hada ido suka sakeyi dan idanunta na kanshi har lokacin, hannunshi yatura cikin aljihu yaciro duka rapan kudin daya taho dasu ya ijiye mata akan cinya yace "use it for anything you need, will see you later" gyadamai kai tayi ya mike tsaye tashi itama tsaye tayi itama batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi tsam tsam murya chan kasa tace "thank you Dr, sai anjiman kaji" sanan tasake shi da sauri yajuya yafita daga dakin batare daya kalleta ba yafita daga gidan. _TWO DIFFERENT WORLD_
Chapter 15 · 0% Book details