← Book details Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 79

Sashe 17

Two Different Wold Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

about my hypersensitive situation, kaike monitoring minishi kana bani magani, masu irin condition dina can die any moment, na zauna nai tunani na kalleka nakuma karance ka Waleed matama basa gabanka sai aikin gidan marayu, and inaso kai aure inaso naga y'ayan ka my grandchildren kafin nima nabar duniyan nan, batun yau ko jiya nake nema maka mataba, nafara nemama matan aure tun kana 25yrs amman banga wacce tamin ba sai akan khadija, Khadija tayi sauka, tagama karatun ta lawyer ce mai zaman kanta, gata yar gidan mutunci, kuma ranan data fara ganinka na fahimci tana sonka so bakadan ba, inhar ban zabamaka irin matar nan ba wa zan baka maka? But I am sorry, na dauka na isa dakai but I guess I am w......" hannunshi yasa yarufe mata baki tareda girgiza mata kai yace "Ammi kin isa dani, I just didn't wanna get married now ne, Ammi am too young, just 28 fa, and ita yarinyar she is 26 da 2yrs fa na girmeta" dan murmushi Ammi tayi ganin ya sauko ta rungumoshi ta hanyar daura kanshi kan shoulder dinta tace "age is just a number Waleed, nasan tsoro kake kan baka wani girmeta sosai ba bazata girmamaka ba, and you being 28 itakuma 26 baya nufin hakan I know yarinyar dana aura maka tanada dattako she will respect you kaman her king son, are we good now kahakura kadena fushin?" gyadamata kai yayi ahankali yace "yes" dago kanshi tayi ta manna mai kiss agoshi tace "thank you, Allah yamaka albarka, yanda ka rufamin asiri baka kunyatani ba kaima Allah bazai taba kunya taka ba duniya walahira, Allah yakareka daga makiyanka, akwai kaya na mussamman dana maka ordersu daga Morocco "Sherwani masu kyau zakayi kaman wani dan India, dama yarona badai kyau ba ballema yasaka sherwani nan, dan murmushi kawai yayi, ahankali ta shafa kanshi tace "nagode kaji, ka rike amana kaji, ka kulada matarka, Uncle dinka ya shiga villa wai yanada meeting da president saisa baka ganshiba kafin anjima by 8 yatafi Airport dan jirgin su 10 zai tashi" gyadamata kai yayi kafin yatashi ahankali kan jikinta da sauri tace "ina zaka?" ahankali yace "waya zan dauko nakira blood" shiru tayi tareda binshi da kallo kaman yautafara ganinshi, wayan yadauko yadawo yay fillo da kafafunta ya kunna wayarshi yay dialing number Arham wayan yaji akashe hakan yasa ya ijiye wayan Ammi dake binshi da kallo tace "ya akayi? Baka sameshi bane?" dan tabe baki yayi yace "wayanshi akashe" gyadakai Ammi tayi tace "maybe yagaji ne ya kashe wayan dan ya kwanta yay bacci, yasha hidiman bikinka, tunda bikin ka yazo bawan Allah nan bai huta ba" murmushi yayi daya wani irin karama fuskarshi kyau ashagwabe yace "Ammi kinsan menene?" da sauri Ammi ta chusa hannunta agashin kanshi tahau shafawa tace "menene Waleed dina?" dagokai yayi ya kalleta yace "wlh am missing the orphanage so much, yau kawai dabanje be jinake kaman nai shekara I can't stop thinking about those helpless children I know kowa na kewana barinma the little ones" murmushi Ammi tayi sosai ta cigaba da sosamai kai tace "that is why am a proud mother of this hard-working young man, My doctor, I know you are missing dinsu saisa nima I got a surprise 4 you" da sauri yatashi ya zauna ya kalleta yace "suprise Ammi namene?" dan dariya tayi takamoshi ya kwanta tace "to sarkin azarbabi koma ka kwanta" gyara kanshi yayi akan cinyanta yana murmushi itakuma ta maida hannunta cikin gashinshi ta cigaba da massaging tace "kwanaki kafadi mini on the 8th ne zakuje excursion da yaran gidan marayunka a Yankari ko" gyadamata kai yayi tace "so I checked my date sai nagama ma next week ne 8th, so I called the Yankari game resort namuku booking gabaki dayanshi from on the 8th to 16th, kadauki matarka duka kutafi and have fun, if seeing those children da zama dasu makes u happy then am ready to give it to you all, kuje kaida matarka da Arham da yaran all Allah ya tsaremin ku but zakadau bodyguard dinku, kuna dawowa kuma u can resume office" tunda take maganan yake kallonta ta mugun mugun faranta mai rai zai iya cewa acikin plenty gift din databashi da bakin nan nashi this is just the best gift, hannunta yama peck yace "thank you Ammi na, I love you so so sooo much" murmushi tayi ta dagashi tace "ni barni naje nai breakfast kaiba abinda ka iya dafawa balle na zauna adakinka kaje kitchen kamin girki" dariya yayi yace "Ammi Allah ki zauna namiki sakkwara da miyan kubewa" hancinshi taja tana dariya tace "yakuri son ban shirya cin mara dadi yau ba" da sauri yace "Allah Ammi" fashewa tayi da Dariya tajuya tafita kaman ba itaba inkaga dariyan Ammi da danta take. _TWO DIFFERENT WORLD_
Chapter 17 · 0% Book details