← Book details Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 58

Sashe 8

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari ban ɗaga ko tsinke ba a gidan, dan banma tashi a barci ba sai ƙarfe bakwai. Salla nayi nai wanka nai shirin office nai tafiyata, dan har lokacin babu wanda ya tashi suna can suna barci ana jiran jaka ta gama girkawa a fito a ci. To ai na fisu iya tsiya, dan kamar yanda na saba in har aka gunziga min baƙin ciki a gidan sai na maida murtani. Yaya Musaddiq bai san tsiyar dana shuka ba ya ɗaukeni muka wuce a mashin ɗinsa. A hanya nake roƙonsa wannan weekend ɗin muje muga Hafizzullah a Katsina dan ALLAH idan baida aiki da yawa. Bai musa ba yace min in sha ALLAHU zamuje ranar asabar sai mu dawo lahadi. Sosai naji farin ciki, harma na manta da damuwata balle na sanar masa banyi breakfast ba na gudo yau. Yana sauke ni ya miƙamin 1500. Amsa nayi ina masa godiya da yima iyayenmu addu'ar samun rahama. Daga haka na shige shi kuma ya wuce.
         Kasancewar yau inada gabatar da program banfi zaman mintina talatin ba na tashi na fita tare Khalid. Kusan cin karo mukai da Mansoor dake ƙoƙarin fitowa. Baya naja da sauri, sai hakan ya sakani tuzguɗewa na tafi zan faɗi. Kusan tare suka kawo hannu shi da Khalid domin taimaka min, niko nai saurin sake maida jikina baya ta yanda kowannensu bai samu damar taɓanin ba, dan na gwammaci na faɗin kawai. Aiko faɗuwar nayi, na kuma ji zafi sosai, duk da kuwa na fuske Mansoor sai da ya fahimci hakan. Cike da damuwa yakai duƙe gabana tare da sake kai hannu zai riƙo nawa na ɗan hararesa. Murmushi kawai yay ya janye hannunsa yana kaisa saman kansa ya shafa cike da basarwa. Sai kuma ya sake maida idonsa gareni, a hankali ya ce, “Yanzu har kina da damar yin masifa babie. Naga dai hannun ai nawa ne”.
     Sake hararsa nayi tare da ɗauke kai ina ɗan murguɗa baki, na ce, “Sai ka bari sai ka biya ai”. Ina kai ƙarshen maganar na miƙe abina. Dariya ya saki mai sauti da faɗin, “Rigimammiya kawai ai saura ƙiris dai, mi kike ci na baka na zuba. Wata uku bazaki ƙaraba sai da igiya uku na ciff a kanki”.
         Murmushi kawai nayi ina ɗan murguɗa bakina dake cikin face mask ɗina na wuce na barsu a wajen Khalid na tayasa dariya. Sai da na gaishe da kowa kafin na wuce na ɗan ƙara gyara fuskata gaban mirror, suma su Mansoor sun shigo, dama mu zaije kira ashe. Hakama baƙonmu na yau ya iso tuni, dan haka babu ɓata lokaci aka fara gabatar da program ɗin........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕_

.......Yau ma kamar kullum Mansoor ne ya ɗaukeni zuwa gida bayan an tashi. Mun ɗan fara tafiya nake sanar masa aikin da MD ya saka ni. Da mamaki ya juyo yana kallona da faɗin, “What! Dama ke ya bama aikin nan? Taya zai haɗaki da wannan aikin mai wuya bayan yasan wanene wannan mutumin. A tarihinsa fa bai taɓa yarda yayi hira da ɗan jarida ba har yanzu. Kuma karki ɗauka wai ƴan jaridar nan gida Nigeria kawai. A'a har manya-manyan ma irinsu BBC, VOA, Aljazeera da ire-iren su. A duk sanda aka buƙaci hira da shi sai ya haɗa mutane da P.A ɗinsa...”
        “Hu'umm, to amma shi miyyasa yake yin haka? Kamar ba wayayye ba? Ko kuma bashi da gaskiya ne shiyyasa yake gudun hakan?”.
     “To ALLAH kaɗai masanin gaibu, sai kuma shi da ya barma kansa sanin dalilin. Amma dai wasu na ganin girman kai ne kawai da giyar kuɗi dake ɗibarsa. Dan a yanzu fa shine matashi ɗan kasuwa na biyu a duniya dake juya manyan kuɗaɗe, anama hasashen nanda shekara mai zuwa zai iya zama na farko. Wasu kuma na ganin akwai dai wani babban dalili nashi, dan in har da girman kai ne ai zaiso ƙara bayyanama duniya shi ɗin wanene ta hanyar ƴan media ɗin. Wasu ko na ganin ko dodon tsafinsa ne yace kar yay hakan, kin san dai mafi yawan ƴan kwasuwar nan dake shahara a ƙanƙanin lokaci sai a hankali, shiyyasa ake yawan ɗora musu zargi, ALLAH dai masanin gaibu. Amma gaskiya al'marin dai nasa akwai ɗaure kai”.
        “Ƙila to aljanu ne da shi da basa son hira da ƴan jaridar. Ko kuma dai da gasken dodon tsafinne da shi. Dan ni naga yanda kowa ke misalta dukiyar tasa akwai ban tsoro kam”. Na faɗa cikin halin ko in kula. Dariya sosai Mansoor ya sanya, tare da faɗin, “Kai Babie baƙya rabo da wauta ALLAH. Aljanu kuma? Namiji da aljanu? Adai tsaya a dodon tsafin”.
    “To inba aljanu ba shi kam ai abin nasa yayi yawa, dodon tsafin ma kuma ai aljanu ne. Yanda yake nuna kansa a matsayin wayayye irin haka ai ya kamata ace an wuce wannan ajin. Amma ni kam in sha ALLAHU sai na sakashi ya magantu, ni halin nasa ma sai ya ƙara min ƙwarin gwiwar tunkararsa.”
       Sosai Mansoor ya juyo ya kalleni cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene *_MASH!?_* kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”.
        “Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”.
       Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa'a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”.
    “Tami?”.
  “A'a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan”.
       Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina na ɗauke cikin jin kunya, sai dai wani irin farin ciki ne ke ratsa ƙashina da ɓargo har ina jin yanda jikin nawa ke rawa. Amma dai nayi juriyar dakewa. Sai dai ban sake cemasa komai ba har muka iso. Tunda ya tsayar da motar na kasa wani motsi, mun kai minti biyu a haka shi kuma yana kallona kamar ya samu tv kafin ya saki ɗan murmushi mai sauti. “Wai kunyar ce dai Babie?”. Sake kauda kaina nayi gefe batare dana bashi amsa ba. Ya saki ƴar siririyar dariya yana ɗan dukar sitiyari, sai kuma ya juyo gareni yana faɗin, “ALLAH ya kaini randa zan cire wannan kunya dai kowa ya huta, dan bazanyi sakaci ba a daren farko zata kama gabanta. Anya baki haɗa jini da fulani ba Samraah”.
       Hannu na kai ga handle ɗin ƙofar zan buɗe na gudu sai na jita gam alamar ya saka lock. Kasa sake wani yunƙuri nayi, na kuma kasa juyowa dan har lokacin ina jin kallon ƙurullar da yake min.
   “Kayi haƙuri ka buɗemin, zancen ganin Abba kuma ya kamata ka fara ganin Yaya Musaddiq dai first nake ga”.
        Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, sai kuma ya amsa da, “Okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe in sha ALLAHU na samu Yaya a gareji”. Daga haka ya buɗe min. Wuff na fice abina kuwa. Batare da ko sallama nayi masa yau ba na shige gida, har lokacin kuma ina jin idanunsa a kaina. Ina rufe ƙofar gate ɗin na jingina a jiki ina sauke numfashi, sai kuma na kai hannuna saman ƙirjina da ke bugawa da sauri-sauri. Murmushi na saki kafin na buɗe idanuna a hankali na ɗan leƙa gate ɗin naga ko ya wuce. Sai lokacin naga yana ƙoƙarin yin reverse. Bazan ɓoye miki ba ina matuƙar ƙaunar Mansoor wlhy Bilyn Abdull, soyayya nake masa mai ƙarfin gaske da bama zan iya misaltata ba, dan Mansoor ya mun abubuwa na halacci da dama akan soyayya da bazasu iya ƙirgiguwa ba, na tabbata da aure kawai zan iya masa godiya a kansu amma bada fatar baki ko soyayyar saman titi ba.
Chapter 8 · 0% Book details