← Book details Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 58

Sashe 48

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

      _Ai ni kaina idanun nawa a waje. Abba al'amarin ka ya fara ban tsoro da mamaki. Ya rabbi kasa mu rayu da ƴaƴanmu, maraici da banne wlhy a rayuwa😭_.

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_

........ Musaddiq ne kawai yay murmushi yana mai girgiza kansa. Ganin Kawu Musa na neman fusata dan dama shi akwai zuciyar tsiya yay saurin faɗin, “Uhm Kawu inaga babu damuwa ai. Kuma na wajenku ku barsu. In sha ALLAHU babu abinda zai gagara na sadakar. Ko daga gobe in ALLAH ya kaimu ake son fara duk abinda ya dace ni a shirye nake.”
     Sosai suke kallonsa zukatansu na ƙara rauni. Yaron jarumine na gaske da kowaɗanne irin iyaye zasu yi alfahari da shi. Gaba ɗaya halin Musaddiq irin na mahaifinsa ne. Ga sanyin hali ga haƙuri ga kirki da jarunta. Sun nuna masa zadai su bashi kuɗin amma ya dage kan bazai amsa ko sisi ba. Dole suka haƙura suka barsa. Ƙyawawan halayen yaron na sake saka musu jin kunyar wofamtar dasu da sukayi a lokacin da suke matuƙar buƙatar tallafinsu, amma kuma bakin alƙalami ya riga ya bushe yanzu kam sai dai haƙuri, dan ta wani ɓangaren suma ba laifinsu bane. Ƙanin mahaifiyarsu ne ya nuna musu shi ɗan boko ne kawai sjiyyasa sukai zuciya suka bar masa su.

        Kaf abinda ya faru a zaman sai da Mum ta tsare Abba ya sanar mata. Aiko ta sake zugesa akan babu wata addu'a sun zo ne kawai su yaudaresa su amshi kuɗin. In ba hakaba wace addu'a ce za'a wani ce sai da kuɗi. Daga ƙarshe ta sake ingizashi kan ya binciki Musaddiq duk yanda akai yaron kuɗine da shi, in ba hakaba taya komai ya taso sai yace zai yi. Daram kuwa ya hau ya zauna ko kunyar ALLAH babu washe gari yay kiran Musaddiq yay masa tujara. Ya kuma ce yana buƙatar 1mil a wajensa da za'aima Samraah kayan ɗaki, sannan ya bada kuɗin kayan kitchen suma Mum zatayi masa list ɗin komai. Sai da ya gama sauraren Abba kaf sannan yay murmushin sa mai sanyi. Cikin nuna rashin wata damuwa a fuska ya ce, “Ba damuwa Abba ka saurareni zan samo in sha ALLAHU”.
      Sallamarsa Abba yay yana ƙara jaddada masa. Yana fita Mum tai wuff ta fito alamar dama laɓe tai musu. Zama tai kusa da Abba tana faɗin, “Bana gaya maka ba Abban Abbas. Yanzu ka yarda ko? To ALLAH kaɗai yasan mi yaron nan ya tara yake raina mana wayo ya barmu da nauyin hidimar rawuwarsu. Ana gama hidimar bikin nan ya kamata ka sashi ya bama Abbas jari yabar wannan gantalin rashin aikin, sannan itama Baby ta fito da miji dan nagaji da yawon nan nata haka nan”.
         Babu wani dogon nazari ko tunani a wannan magana Abba ya amsa Mum tare da bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Daga haka suka cigaba da hirarsu cike da soyayya.

   A ɓangaren Musaddiq kam shi al'amarin su Abba kam ya fara bashi tsoro. Dan ya wuce abin mamaki ko al'ajabi. Amma dai a wannan karon zai ari halin Samraah ko kaɗanne ya gani ko zasu fahimci shi ɗin bawai sakarai bane. Yana binsu ne kawai da halayensu saboda wasu dalilai. Yanzu banda rashin adalci bama damuwarsu ɓatar ƴar uwarsa ba kusan sati biyu kenan, shi dama gani yake Mum da Baby kamar farin ciki suke da rashin Samraah a gidan. Ko mi tai musu haka da zafi oho ya kasa fahimta. Yasan Samraah fitinanniya ce, to amma duk abinta saika shiga sabgarta ne, kuma mafi yawan lokaci sune ke fara takalarta ita kuma ta maida murtani.
      Washe gari kamar yanda suka tsara aka fara gudanar da addu'oi. A masallatai da islamiyoyi, aka kuma dafa abinci aka dinga rabawa mutane musamman ƙananun yara da almajirai. Dan har tsangayoyi aka kai abincin ma. Acan gwarzo ma su Kawu Musa abinda sukai ƙoƙarin yi kenan da kuɗin da Musaddiq ya basu. Dan Mansoor ya taimaka musu sosai da yaji shirin nasu. Dan ko abincin nan ma da aka dafa anan shine ya bada aka dafosa da taimakon Mamynsa. 

      Kwana uku anata addu'oi da raba dafaffen abinci. Ga kwanakin biki nata sake matsowa daf. Gefe Musaddiq nata wasan ɓuya tsakaninsa da Abba da Mum. Yayinda su kuma suke zaman jiran a kawo musu kuɗi.....

        ✨★✨★✨★✨

Tabbas duk wanda ya miƙa al'amarinsa ga UBANGIJI babu shi babu taɓewa Bily, naga fa'idar hakan ƙwarai da gaske a wannan gaɓar. Domin kuwa duƙufar da nai wajen gayama UBANGIJI damuwata ya saka min ƙwarin zuciya da jin sabon ƙarfi na dawo Samraah ta tada. A daren da nake lissafin kwanakin aurena da Mansoor saura biyar kacal a bazata naji ana ƙoƙarin buɗe ɗakin da nake. Hakan ya bani matuƙar mamaki dan ba lokaci bane da ake kawo min abinci, kusan ƙarfe goma da wasu mintuna ake yanzu na dare. Hijjabina daya kasance ɗaya jal da nake salla da shi na ɗauka da sauri na saka. Bamma kai ga ƙarasa sakawarba har an riga an shigo. Baki na buɗe cikin ɓacin rai zanyi magana kawai ya jefamin wata muguwar harara. Ba kowa bane face yaronsa ɗin nan mai dogayen kunnuwa uwa na zomaye. Nima hararsa nai da mare baki, a fili na furta, “Daka daina burga dan baka da banbanci da damisar takarda. Kullum kana bayan wani kamar mai gadi”.
A take fuskarsa ta rine zuwa ɓacin rai, ya ɗaga hannu kamar zai ƙwaɗan mari sai kuma miya tuna oho masa ya fasa. Ya dunƙule hannun yana ɗan kaima iska naushi a cikin takaici. Ni dariya ma ya bani, amma sai na dake banyi ba. A cikin zafin rai ya furta “Shigo ki mata”. Ban gama hahimtar mi yake nufi ba likitar ranar data dubani akan matsalar ciwon mara ta shigo. Matar ƴar gayuce sosai. Da gani kuma kasan itama ƴar masu kuɗice. Murmushi tai min cikin tsokana tace ashe dai patient ɗina ta miƙe?”. Watsar da ita nai kamar banji mita faɗa ba, dan haka kawai bata mun ba, nama ɗauke kaina gaba ɗaya. Magana tai yunƙurin sake yi mai kunnen zomaye ya dakatar da ita cikin magana zafi-zafi ya ce, “Doctor kimata kawai”.
Itama amsa masa tai da to tana zaro syringe. Kambu idona idon allura na zabura zan miƙe, sai dai mi jinai kawai an damƙomin hannu an riƙe, kafin na farga ta saka min handcuffs. Ido rufe na buɗe baki zan balbaleta da masifa ta shamaceni kawai sai shigar allura naji a hannuna. Kafin wani dogon motsi ta zareta tana sauke ajiyar zuciya kamar daga jikinta take cirowar. Kaina ne ya fara juyawa na koma ganin ɗakin da su kansu bibbiyu, da ƙyar na iya ɗaga hannu ina nunasu amma na kasa magana. Dan idanuna lumshewa suke kaina na ƙara nauyi, a cikin abinda bai wuce minti ɗaya da wasu sakanni ba komai ya koma min ɗiff. Sai buɗe idanuna nai na ganni a inda banyi zato ko tsammani ba....

      💫💥💫💥💫💥💫
Chapter 48 · 0% Book details