← Book details Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........Ina zama office ɗinmu daya kasance mu biyar ne a ciki Asiya data kasance duk tare muke anan ta shigo da sallama. Ganin takardu a hannunta ya tabbatar min da ba yanzu ne ta shigo ba. Gaisawa mukai farko, kafin ta ɗora da faɗin, “Samraah MD na kiranki kuwa. Ya ce ki maza kuma dan zaiyi baƙi”.
       Kaina na jinjina mata batare da nayi magana ba na miƙe ina sake gyara zaman facemask ɗina daya ɗan zamo ta saman hanci. A cikin takuna na nutsuwa da yanga da mutane da yawa ke fassarawa na fito. Duk wanda na gamu da shi nakan ɗaga masa hannu da cewa good morning, wasu sukan ɗan tsokaneni. Sai dai iyakata murmushi kawai dan nifa idan ba kayi dogon zama dani ba bazaka taɓa tunanin inada surutu ba sam. Ban cika yawan magana a ko ina ba sai in nice naga damar hakan. Shiyyasa da yawan mutane ke ɗaukata mai shiru-shiru. Har wasu kan dangantani da hakan da iya yardarsu. Basu sani ba idan aka taɓoni banda ragi banda ragowa sam. Na isa office ɗin MD, bayan nayi knocking sai da nai tsaiwar kusan minti ɗaya kafin ya bani izinin shiga ciki. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, dan mutum ne shi mai shegen son kallon mutane kamar zai cinyesu. Cikin son kawar da idanunsa dake yawo a kaina ya ce, “Zauna”.
      Zaman nayi a ɗarare nace da shi, “Good morning sir”.
       A taƙaice ya amsani da, “How are you?”. Batare da ya jira amsawata ba ya cigaba da maganarsa yana turomin wata ƙyaƙyƙyawar mujalla da wani envelope mai kama da invetion card. Bana ganin fuskar mutumin daya mamaye bangon farko na mujallar gaba ɗaya. Sai jikinsa dake sanye cikin wasu shegun suit sky blue zuwa ƙafarsa dake cikin cover shoes dake wani shining duk da kuwa a hoto ne. Zaune yake a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya, hakan ya bani ɗan damar ganin hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen farata dake riƙe da glass cup da guntun drink ke ciki. Sai zobe guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsarsa...
         Duk da baifi a sakanni goma na ƙarema hoton irin wannan kallon ba a ɗan kamar fusace naji gyaran muryar MD a kaina. Saurin gyara yanayina nayi na maida hankalina gareshi, fuskarsa a ɗan ɗaure yana famar yamutsa fuska ya ce, “Ɗauka ki duba”. Ɗaukar nayi, sai dai ban kallaba yanzu na maida hankali garesa da nuna alamar shi nake saurare. Shima sai naga ya ɗan sassauta yanayinsa. Ya nuna ni da faɗin, “Samraah na zaɓoki ne saboda nasan zaki iya. Wannan mujalla ce ta TAURARINMU A YAU data fita jiya. A gaba ɗaya abinda ke cikinta ya ta'allaka ne akan matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ke amsa kuwa a ƙasashenmu na Africa dama duniya a ɗan tsakanin nan. Wato *_AWWAB  EL-MU'AZZ._* sai dai kowa yafi saninsa da *_MAASH_* ne. Maash ɗan arewa ne haifaffen garin Kano sai dai mazaunin jihar Lagos. Yana da tarin cibiyoyin kasuwanci a kudancin ƙasar nan dama wasu ƙasashen Africa. Hakama a ƙasashen turawan da larabawa yana da rassan kasuwanci. Amma abin mamaki bai taɓa kafa wani abunsa a arewacin nan namu ba. Hakan yasa mutanenmu sukai masa ca, suke kuma sukarsa akan hakan, har takai suna ƙalubalantar dukiyar tasa musamman idan akai dubi da ƙarancin shekarunsa. Duk da kuwa an san mahaifinsa nada kuɗi, hakama Kakansa sanannen mutum ne, sai dai ko kwatar abinda shi MAASH ɗin ke da a yanzu mahaifinsa bai mallaka ba. Kace nace ya sake yawaita a kansa ne a watanni uku da suka gabata, dalilin bayyanar Companyn sa na jirage dake jigilar mutane daga Nigeria zuwa ƙasashen ƙetare. Domin a farko jirage goma ne ciff suka fara aiki. Sosai manyan gidajen jaridu sun so tattaunawa da shi amma Maash yaƙi bada kowacce irin dama. A duk lokacin da hakan ta taso sai dai a tattauna da P.A ɗinsa. To nadai taƙaice miki zance a yanzu haka bayan ka-ce-na-ce da aka sha yimasa akan gudun arewa da ƙaruwa Mujallar nan ta fitar da bayanan buɗe ɓoyayyen katafaren company da kusan wata uku kenan ana aikinsa batare da mutane sun san na wanene ba a cikin Kanon nan. Company ne na ƙera motoci da babura da abubuwa masu yawa da suka shafi ababen hawa. Irinsa shine na farko a Africa, a duniya kuma na uku. Kuma Maash da kansa zai zo Kano bikin buɗesa. Hakan yasa tunda naga mujallar nan na shiga na fita sai da na samo mana invetion card ɗin shiga wajen, dan hatta ƴan jaridar da zasu halarci wajen a ƙa'ide suke. Dan haka na kwana nazari a daren jiya, na kuma hanga na hango a kaf gidan nan kece nake ganin zaki iya mana wannan aikin, fatanmu kiyi duk yanda zakiyi kisa Maash ya magantu a gaban ƴan jarida karo na farko dan ALLAH. Hakan zai zama ba ƙaramar nasara ba a garemu da ma wannan gidan namu baki ɗaya. Sannan ke a karan kamki ma wata sabuwar ɗaukakace da nike da tabbacin zata zamewa rayuwarki alkairi in ALLAH ya yarda.”
        Wani irin nauyi naji kaina yamun, dan haka da ƙyar na iya fisgo kalma ɗaya akan harshena na furta. “Amma Sir kaifa kace bai taɓa yarda yayi hira da ƴan jarida ba. Taya kake tunanin ni zan iya samo wannan nasarar? Yaushe ma na fara aiki, wane matsayi na taka a cikinsa? Ni wacece da zanyi abinda manyan ƴan jarida gogaggu suka gagara yi cikin sauƙi haka?”.
       “Ba cikin sauƙi bane Samraah. Sannan al'amarin ba iyawa bace ko kaiwa wani matsayi. Sa'a ce kawai kuma kowa da irin tasa a rayuwa. Nima ba ina ji bane wai lallai sai hakan ta kasance ba. Fata dai nake yi da jin yaƙinin zaki iya in sha ALLAHU”.
    Shiru kamar bazance komai ba, kafin kuma na sauke nannauyar ajiyar zuciya. Na ce, “Shike nan Sir zan gwada na gani, ai da gwaji jirgin sama ya tashi sama daga bisa ƙasa. Amma dai bani kaɗai ce zanje wajen ba?”.
      Ƴar dariya yayi a karo na farko, cikin tsokana ya ce, “Kada kice min ke ɗin matsoraciya ce mana. Bayan kuma kallon jaruma nake miki. Kallabi a tsakanin rawuna”.
    “Humm Sir bazaka gane ba. Irin waɗan nan mutanen da suke jin tamkar ma duniyar su suke mata alfarma ba itace ke musu na basu fili a cikinta ba suna kallon mutane ne tamkar wasu dodannin tsaffi a rayuwa. Dan a kullu yaumin zaka gansu ne zagaye da masu tsaro a kowacce kusurwa ta rayuwarsu. Ni gaskiya bana son ƙasƙanci koda a wajen wanda ya fini ne”.
         “Wannan itace ɗabi'a ta cikakken mutum ai Samraah. Duk wanda yasan darajar kansa haka ake so kuma ya kasance. Kada ki damu bake kaɗai zaki je ba. Hasalima ke aikin ki shine gabatar da shirin kawai. Akwai Davido da Mansoor da Khulsoom a tare dake. Yanzu sai kije ki tsara tambayoyin da zaki masa ki kawo min, ki nutsu sosai wajen tsarasun daga nan har zuwa Monday, kinga kinada kwanaki kusan huɗu kenan tunda yau muna alhamis. Kije da wannan mujallar domin duba abinda suka rubuta a kansa. Za kuma ki iya wani binciken a kansa ɗin dai koda ta hanyar yanar gizo ne ko wasu mutane. Hakan da zakiyi ne zai baki damar tsara abinda ya dace a kansa ɗin, dan ina fatan mu zama mune taurarin mako mai zuwa”. Ya ƙare maganar yana murmushi.
    Nima dai murmushin nayi, dan ya ba ni dariya. “In sha ALLAHU zanje nayi nazarin Sir. Maybe ma kafin Monday ɗin kaga na tura maka duk abinda na tsara ɗin koda ta WhatsApp ne”.
         “Masha ALLAH, ALLAH ya bada ikon hakan. Amma dai baki da matsala kibi komai a sannu tunda nunada kusan kwana goma kafin ranar”.
     “To nagode Sir”.
  Na faɗa ina miƙewa hannuna ɗauke da Mujallar. Harna fice a office ɗin ina jin idanunsa a kaina. A raina nace (Maye kawai sai dai kaci kanka kasha baƙin ruwa).......✍️

_Tofa masu karatu yaya kuke tunani akan wannan aiki da MD ya damƙama Samraah. Shin zata samu damar haɗuwa da wannan matashi mai wahalar sha'ani mai suna *Maash* ko kuwa?_.

_Idan ma ta haɗu da shi ɗin taya zata iya abinda wanda suka fita faɗa aji da gogewa akan irin aikinta suka kasa?_.

_Shin wai wanene ma *Maash* ɗin nan ne? Minene dalilinsa na gudun yarda ya bayyana asalinsa ga ƴan jarida. Miyyasa yake ɓoye kansa? Minene baya son a sani game da shi ɗin?_

_Duka wannan amsoshin suna a kundin littafin TSUTSAR NAMA... masu iya magana sunce wai ITAMA ƊIN NAMA ce. Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da abubuwa masu ban mamaki, al'ajabi, makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban-daban._

*_In sha ALLAHU sayen nagari maida kuɗi gida😊😉😉😘😘🫡🫡._*

______________

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙_
Chapter 5 · 0% Book details