← Book details Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 58

Sashe 19

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haɗa jini da babaƙen fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaɗaine a ɗakin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma ƙoƙarin nufar ƙaton mirrorn dake a ɗakin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya ɗan shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen ƙamshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buɗe, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk ƙananu, sai ƴar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin.....

     ●´⌓`●●´⌓`●●´⌓`●

           Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”.
     Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”.
              “Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”.
     Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”.
        “Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”.
       “Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”.
      “A'a”.
   “Miyasa?”.
“Kawai dai”.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”.
       “Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”.
     “Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”.
        “ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.”
     “Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”.
      Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........✍️

_Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za'a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?..... Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴._

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_
Chapter 19 · 0% Book details