Sashe 57
Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna.
Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas...” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya........✍️
_🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_
.......Har muka iso kuka nake sosai, haka dai aka fita dani kaina a lulluɓe. Ina jin mutane nata yaba gidan. Hakan baisa naji wani abu daban ba saboda nasan gidan Mansoor kam tabbas yayi ƙyau da tsari. Sannan babu laifi babbane. Da addu'a na shiga kamar yadda Gwaggo ta bani umarni. Dan motar da aka ɗakkoni ce kawai dama ta shigo har cikin gidan. Sauran duk a waje suka tsaya. A falo aka ajiyeni kamar yanda Inna Magajiya tace. Mutane suka ɗan shishshiga kitchen da inda ba'a rasa ba. Bedrooms dai a rufe suke duka biyu dake a gidan kamar yanda naji suna faɗa. A karan farko na ɗan ji mamaki, dan nasan bedrooms huɗu ne a gidan Mansoor. Amma dai banda tacewa, bayan mutane sun gama zazzagawa suka fita dan dare ya farayi za'a maidasu gida. Sai da kowa ya fita sannan Gwaggo ta kama hannuna ta kaini bedroom da naji tana faɗa bayan ta buɗe da makulli, anan ne na gane ashe keys ɗin na hannunta sune dai suka hana mutane shiga wai dan kar a ɓata tunda dare yayi babu damar zama a gyara min. A bakin gado ta zaunar dani, tana sake jaddada min kalmar haƙuri, haƙuri dai da duk abinda zan gani, dan shi aure ibada ne bawai wasan yara ko nanaye kamar yanda mu yaran yanzu muke tunani ba. Ni dai kuka kawai nake zabga mata. Tadai samu ta zame jikinta ta gudu ta barni. Kuka na sake fashewa da shi irin mai cin rai da zuciya ɗin nan, harna zame na kwanta a gadon batare dana sani ba na cigaba da kukana.
Tun ina darzar kuka da tunanin Mansoor zai iya shigowa har al'amarin ya fara bani tsoro. Dan gari yay wani irin shiru sai kukan karnuna amma babu Mansoor babu labarinsa. Kai komai ya fara canja min daga yanda nake tunani da hasashensa. Dan daga jiya zuwa yau komai da nake gani ba irin tsare-tsaren Mansoor ɗina bane. Komai yana zuwa min a banbancin abinda muka tsara. Mi hakan ke nufi, Mansoor ne ya canja komai a yanda na sanshi ko yaya al'amarin yake ne?. Banda mai bani amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyi na. Dan haka na cigaba da kwanciya a wajen ga ciwon kai mai tsanani na ratsani, kafin ma wani dogon lokaci na fara rawar sanyi. Ina jin yanda wata iskar hadari ke tasowa da ƙarfin tsiya amma na kasa ko motsi. Haka na cigaba da kasancewa a wajen na tsawon lokacin da ban san adadi ba har barci yay awon gaba dani batare dana farga ba....