← Book details Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 58

Sashe 18

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

          “Sir dan ALLAH kada ka saka kanka a damuwa. In dai batun yarinyar nan ne dai-dai yake da kaɗawar iska mai wucewa. Ita ta isa ta saka abinda bakayi niyya ba. Waye ubanta a ƙasar nan? Har micece ita a aikin jaridar ma. Yarinya ce fa ƙarama fitik”.
       Idanunsa dake lumshe ya buɗe a hankali. PA ɗin nasa dake magana ya zubama su kusan sakan arba'in. Sai kuma ya sake maidasu ya lumshe a kasalance. Dai-dai nan drivern sa yay sallama a ƙofar katafaren falon. PA ɗinsa ne ya amsa. Sai kuma ya bashi umarnin ya shigo dan yasan kayan boss ɗin nasu ne dake a mota ya kawo. Cike da tsantsar girmamawa yaje Centre table ɗin gabansa kuwa ya ajiye. Sai kuma yay ɗan jimm a duƙe kafin ya ɗago yana nuna wata jaka. “Sir wannan wani mutum ne yanzu nan ya kawo wai a baka. Naso ƙin yin hakan amma kausasan kalamansa suka daƙileni. Dan ya tabbatar min ƙin baka ɗin zai zama kuskuren da bazan yafema kaina ba kaima kuma bazaka yafe min ba. Dan saƙon nada amfanin da idan na wofamtar da shi dai-dai yake da gina harsashin tarwatsaka. Amin afuwa shine ya faɗi hakan”.
       A zabire PA ɗinsa ya furta,  “What! Wane ɗan iska ne haka. Su securitys ɗin gate kuma suna aikin mi ya shigo cikin gidan nan, kai kuma ka zauna sauraren wawancinsa, are you mad?”.
       Shiko gogan ko motsi baiyi ba. Sai idanunsa da ya ɗan buɗe kaɗan a ƙasa-ƙasa yake kallon drivern nashi da su. PA zai sake magana ya masa alamar ya barsa. Hakan yasa driver tashi da sauri ya fita ya bar saƙon da aka nannaɗe a cikin leda mai ƙyalli. Sake maida idanunsa yay ya lumshe kawai. PA da hankalinsa gaba ɗaya ke'a kan saƙon sam ya kasa nutsuwa, ganin ogan nasa baida alamar bashi umarnin ya buɗe suka miye a ciki ya furta, “Sir ya kamata musan minene a ciki. Dan bamu san mi mai saƙon ya taka ba har yake irin waɗan nan kalaman.” shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kaɗa masa kai alamar ya buɗe ɗin. Jikin PA har rawa yake wajen ɗaukar saƙon. Kamar ƙyaftawar ido ya gama buɗesa ledar da aka nannaɗe sa. Sai dai kafin ya ciro abinda ke'a cikin kwalin da aka naɗe ɗin text message ya shigo wayarsa. Kasancewar wayar mai muhimmanci ce dan ta business ce ya ɗauka dan ya duba saboda akwai saƙon da dama suke tsammani. Rubutu ne da bai wuce words ɗari ba. Dan haka ya fara karantowa.
           Sosai jikin Hayatu PA ke rawa yana mai ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Sir tabbas hasashenka ya zama gaskiya. A kwai wanda ya gammu, kuma tabbas shine mai face mask ɗin nan. Dan gashi anan ya turo saƙo?”.
Idanunsa ya ɗan buɗe batare daya tanka ba yay masa alamar miya faru?. Cikin rawar jiki Hayatu ya fara karanto saƙon a fili kamar haka.........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_

........*_Barkan ka madubin wannan ƙarni. Ba sai na cikaka da gaisuwa ba, bari na tafi kai tsaye kawai. Ina buƙatar naira miliyan ɗari biyar daga gareka. Kuma cikin gaggawa. Idan ba hakaba, a daren yau zan rusa duk wani tanadinka da tunƙahonka da videon dake hannuna ta hanyar yaɗashi a social media. Kasan dai kisan kai ba abune mai sauƙi ba. Musamman ga mutum irinka sananne mai tarin magauta da masoya tako ina. Na baka awa arba'in da takwas. Idan kunne ya ji jiki ya tsira._*

         Ya jima bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kwance jikin kujerar kansa a sama kaɗan. Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima ji ko fahimtar abinda PA ɗin nasa ya karanto masa bane ba sam. Yaja kusan minti uku PA nata kai kawo kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau, sai dai a nutsensa yake abin mamaki. Goran ruwa dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa. Sai da ya shanyesa tas sannan ya jefar da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na biyu yana sake nutsar da kansa, sai kuma kamar wanda ya tuna ya dubi PA ɗinsa. “Ina buƙatar duka cctv footage na company a daren nan?”.
      Cak Hayatu ya tsaya da ga kai-kawon da yake, sai kuma jiki a sanyaye ya ce, “Sir ka manta mun duba sanda muka shiga kafin faruwar abun amma basayi duk an kashesu”.
         “Hakane, amma kamar na kunna ukun farkon nan.”
      “Yes yes tabbas kuma hakane fa Sir. Wlhy sai yanzu na tuna. Aiko ko wanene wannan zaici ubansa.” baima jira umarnin ogan nasa ba ya fice da sassarfa tamkar zai kifa ƙasa duk kuwa da dare ne a lokacin. Dan kusan sha ɗaya ma ake nema, saboda bayan an tashi a taron company sun bu sarkine kamar yanda ya buƙa. Bayan sallar magrib suka bar gidan sarki, maimakon gida suka wuce wajen wani abokin harƙallarsa dan haɗuwar ta sirrice, sai goma saura suka nufo gida. Gashi yanzu ana harar sha ɗaya da wasu mintuna.

        Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa.
         Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka...
Chapter 18 · 0% Book details