Sashe 36
Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_
.......Da faɗa ya faramin tare da turkeni kan saina faɗa masa dalilina na jifan Mansoor ɗin da waɗan nan kalaman. Da farko naso dojewa. Amma ganin yanda ya birkicemin a yanayin da bai taɓa ba bamma san na saki layi ba na zayyane masa komai. Tashin hankali na gani sosai a tattare da shi. Ya sake balbaleni da faɗa cikin ruɗani.
“Amma Samraah baki da hankali. Yanzu wannan abin na faruwa da ke tsahon sati biyu amma kika ja bakinki kikai shiru sai yanzune kike faɗa. Shima badan kunyi haka da Mansoor ɗin ba da bamu kamo bakin zaren ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Samraah baki da wayo, wlhy sam baki da wayo. Dan tabbas bana raba ɗayan biyu mutumin nan ne yasa ake bibiyarki. Dolene ma ya gano kin ɗauki videon nan. Wannan abin shi nake gudu tun farko daman, shiyyasa kullum nake cikin tunanin mafita ashe nima nayi sakaci...”
“Yaya ban gane ba. Wai kana nufin wancan mutumin mai ɗaure gashi Maashi yake komi ma oho masa”.
“Idan bashi ba wanene Samraah. Tabbas dole shine zaisa a iya miki irin wannan bibiyar. Samraah kodai kinyi wani yunƙurine a kansa batare dana sani ba, dan na sanki da shegiyar wautar tsiya”.
“Wlhy Yaya ni babu abinda nayi, kaima kasan kuma bazanyi komai ba sai da saninka. Ka tambayi Mansoor ALLAH ne shaidata shima shaidatane. Daga office bana zuwa ko'ina sai gidan nan. Weekend kuwa islamiyya ce kawai ko Malam Umaru zai tabbatar maka da hakan shima. Toni wanema yunƙuri zanyi tunda kunce nabar komai a hannunku. Wlhy ko video ɗin tunda na adanashi ban sake waiwayarsa ba balle ma na kalla har wani yaji ko ya gani. Hatta da Mansoor ranar yake cemin ALLAH ya kiyaye yana rage abubuwa ya goge video ɗin nan, da ace banda shi a wayata da an samu matsala. Amma dan ALLAH na sake adanashi kada nayi sakaci tunda na sanshi shi da goge-goge a waya na tsiya.”
“Nasan baza'a samu matsala daga gareki ba Samraah. Amma dole mutumin nan yanada cctv camara ai, idan kuma mai yawan bibiyar abubuwane to tabbas anan ya gano shine yasa ake bibiyarki. Ko kuma wani ya ganki. Ina dai zuwa bari na kira Mansoor yazo ya same mu”.
Ban iya cewa da shi komai ba. Sai faɗawa duniyar tunani kawai da nayi. Harya kammala wayar bamma sani ba. Cigaba yay da kai kawonsa alamar haɗa lissafin abubuwa. Cikin abinda baifi mintuna talatin ba sai ga Mansoor yazo. Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi suka tafi massalaci. Sai da aka idar suka dawo ina ɗakin Yaya ɗin dai har sannan. Mansoor na gaida daga haka suka shiga tattaunawa danni gaba ɗaya zuciyata bata tare da gangar jikina. Sai da Mansoor yaymin tambayar ni da waye muka je restroom ɗin a ranar? Dan tambayace da ya kamata ma ace sun min tun a waccan ranar amma basu yi ba. Saida na sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci sannan na sanar musu ɗaya daga cikin securitys ɗin da suka bada tsaro a ranar ce. Na sake maimaita musu yanda mukayi. Sun sake tambayata bayan ita ban haɗu da kowa ba? Sannan itama ɗin sanda ta tafi yin wayar bata dawo bane nemana?.
“Eh gaskiya ni dai banga ta dawo ba, kasancewar ma hankalina ya tafi akan abinda ya faru ban sake bi takanta ba. Dan haka ban san miya hanata sake komawa ba. Kuma ni gaskiya bana jin nama sake ganinta har aka tashi”.
Kallon juna Yaya da Mansoor sukai. Cikin ƙarfin hali da nuna tashin hankali Yaya Musaddiq ya ce, “Anya kuwa security ɗin nan bata koma ba a lokacin. Idan lissafina yayi dai-dai, ta koma domin su fito tare kamar yanda ta mata alƙawari, maybe bata sameta ba ta shiga nemanta, ko kuma ta sameta a lokacin da take bude-buɗen ƙofar ko ma ɗaukar video ɗin. Dan inba haka ba babu yanda za'ai tai ɓatan dabo gareta. Hasashe na biyu lokacin da take faɗa maka ko wani ya jiku. Cikin biyun nan dole ɗaya ya tabbata, kuma duk inda zancen ya fito to tabbas an samu Maash an fargar da shi komai shiyyasa yasa ake bibiyarta.”
Cikin jinjina kai Mansoor ya ce, “Tabbas hasashen ka zai iya zama gaskiya Yaya. Amma ni a wannan gaɓar ma sai hankalina yaso rabuwa biyu akan wasu dalilai. Maash bawai ƙaramin mutum bane. Kana ganin ya aikata wannan kisan ya kuma san ya aikata har wata ace ta ɗaukesa a hoto mai motsi ya sani kuma ya zauna sakaci. Duk da yanda muke tunani abinda masu hannu da shuni ɗin nan suka tsana a rayuwarsu shine su binne wani laifinsu amma ya zama yana a hannun waninsu ko waninsu ya sani. Zakaga suna gaggawa wajen ganin sun daƙile komai. Idan lissafina yayi dai-dai wata fa kusan ɗaya kenan da faruwar komai. Kana ganin zai zaman ɓata lokacine akan wani bibiyar Samraah bayan yana da hanyoyi masu yawa dama zai karɓi video ɗin a hannunta batare da wata gargada ba. Karfa ka manta har hira yazo anyi da shi kuma itace tai da shi, randa aka saki hirar kuma ƙura ta tashi sosai da kace nace ɗin mutane harda masu cewa akwai alaƙa tsakaninta da shi, nasan dai kasan komai ba sai na sake maka bayani ba. Na kawo wannan hujjojin ne saboda bana son mu shagala da yawa a kan shine wanda kuma ke son ƙulla tsiyar na gefe. Kuyi haƙuri MD kansa na cikin zargina. Dan na jima da fahimtar yana son Samraah na hauka, randa kuma ta kai musu kayan saka bikin mu ya tabbatar ma da kowa hakan. Sai ƴar uwarku Baby. Tana sona matuƙa, wasu dalilai ne suke dakufeta, naji a majiya kai ƙarfi cewar tai alƙawarin sai tabi tako wace hanya domin ganin auren nan namu bai yiwu ba, dan tana da babban plan akan haka akwai kuma mai bata ƙwarin gwiwa ta bayan fage. Saboda yima kanta alwashin indai itama bazata sameni ba sai dai su rasa su duka. Da farko na ɗauki zancen shirme kawai irin nata na ƴan shaye-shaye, sai dai wannan abin na yanzu ya fara haskomin da gaske zata iya komai fa. Dan haka musa hankalinmu jikinmu domin tabbatar da ko wanene”
“Shaye-shaye kuma? Wai babyn ce ke shaye-shaye ko wa?” na faɗa ina kafe Mansoor da idanu. Murmushi kawai ya mun da faɗin, “Hum Samraah kenan, ke dai ALLAH ya shirya mana zuri'a kawai”.
Yaya na kalla a firgice, sai naga shi babu alamar mamakin zancen akan fuskarsa. Kasa haƙuri nayi sai da na ce, “Yaya kenan kaima kasan tana Shaye-shayen?”.
Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya furta, “Na sani Samraah. Na kumayi iya yina na ganin ta daina amma hakan ya gagara. Na lurar da Abba amma ya nuna sharri nake mata. Tun daga nan na tattarasu na watsar”.
Zancen ya matuƙar girgizani gaskiya. Kamar yanda sosai maganar Mansoor tayi tasiri garemu ita game da MD da Baby da zasu iya sakawa a bibiyeni. Dan duk abinda ya faɗa gaskiya ne. Ni komai ma sai naji ya sake susuce min. Amma duk da haka Yaya yace bazamuyi sakaci da duka ɓangarorin uku ba. Zamu saka ido za kuma ku ɗauki matakin daya dace da kowanne. Dan haka zamu kai report wa yan sanda akan ana bibiyata, amma bazamuyi batun video ba fa, zamu bar ƴan sanda suyi aikinsu, idan ma Maash ɗinne da ga baya idan fito da videon ta kama sai muyi hakan. Nanma mun gamsu, kun kuma bashi goyen baya, duk da ni dai naso ace tun yanzu muka fidda video ma wa yan sanda. Amma ban san dalilinsu na son a ɓoye video ɗin nan kamar wani suna tsoronsa.
Kwana biyu dayin haka aka kawo lefena da ga gidan su Mansoor. Akwatina har goma sha biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Baby ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Gwaggo Gudidi. Abu kamar wasa dai sai da aka kwashi rigima. Dan ƴaƴan Gwaggo Gudidi duk sun zo suna gidan. Rikici akai sosai na gaske. Lokacin Yaya Musaddiq shi baya gida. Yana wajen aiki, kamar dai wancan karon ya damƙa komai hannun matar ogansa aima baƙi abincin tarba da kayan maƙulashe. A wajen aikin ma ba zama yay ba shi da Mansoor suka fita police station wajen batun ƴan sanda. Sun shigar da report tare da bada lambobin mota har uku dana basu.. Suna can har aka gama rikin nan kowa ya kama gabansa dan su Gwaggo ma sun ɗauke lefen nawa daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Gwaggo yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri. Wannan yasa suka huce kaina sanda na dawo. Dan bana gidan ma ni ina gidan wata ƙawata ta islamiyya. Duk yanda naso daurewa na kasa. Ranar sai da nai kuka sosai da jin kewar iyayenmu. Daga ƙarshe nai alwala nayi nafilfilina tare da miƙama UBANGIJI kukana. Wannan ɓacin ran dana kwana da shi yasa banyi aikin komaiba a gidan. Sai ma shiri da nai tunda farar safiya domin wucewa gidan su Joy ko zan rage damuwa, amma zan ɗan fara zuwa office saboda saƙon da MD ya turamin jiya da dare kusan 12 kan dan ALLAH yana son ganina a office yau idan babu damuwa. Jin yace abu mai muhimmanci ne yasa na amince zanje ɗin, kuma bana ma son yinin gidanmu a yau ɗin sam. Na fito na leƙa ɗakin Yaya sai na samu ya fita. Nayi mamakin fitar tasa ta sassafe yau. Amma sai nai wucewata akan zan kirashi awaya. Zuwa da rana sai na samesa a garejin dan ina son mu ɗan tattauna wani abu.
Napep na samu na shiga. Mun fara tafiya inata ƙoƙarin kiran numbern Yaya sai naji an kira sunana. Da mamaki na ɗago ina kallon wanda ke kusa da ni dana samu a napep ɗin, ganin babu wata alama data nuna shine yay kiran sunan nawa na kalla mai napep shima. Shima kuma babu alamar shi ɗin ne. Cikin takaici da jin haushi na sake ƙoƙarin maida kaina ina mamaki. Sai kuma aka sake faɗin, “Samraah!”. A fusace na ɗago yanzun kam. Kafin na samu damar cewa komai naji abu a fuskata. Yuuuu naji kaina ya fara mun. Cikin zabura nai yunƙurin dira daga napep ɗin sai dai na kasa hakan. Dan cikin ƙanƙanin lokaci jikina yay wani masifar nauyi na silale jikin kujera idanuna na lumshewa. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba kuma......✍️