Sashe 26
Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
.......“Da kika gudo kika barni yanzu ban kawo kaina ba?”. Mansoor ya faɗa dai-dai suna ƙarasowa inda nake shi da Yaya Musaddiq. Baki na ɗan murguɗa ta cikin mask ɗina, a zahiri kam nai ƙasa da kaina sai dai bance komai ba. Sai Yaya Musaddiq ne ke dariya. Ni dai bance komai ba, sai da Mansoor ya sake faɗin, “Bazaki ban haƙuri ba?”.
Bakin na sake turawa. Sannan na ce, “To kayi haƙuri”.
Murmushi Mansoor yay yana kaiwa zaune. “Ai dole ma na haƙura dan bana iya dogon fushi da ke. Ga yaya Musaddiq nan ma shaida ne”.
Murmushi Yaya Musaddiq ya sake saki, ni kuma na ɗan harari Mansoor ɗin. Shima murmushin yay a lokacin, tare da ɗan taɓe bakinsa ya ɗauke kansa gefe. Sai kuma ya sake juyowa gareni. “Mi MD yace dake?”.
Mask ɗin na cire ina kumbura fuska kamar MD ɗinne har yanzu a gabana. Labarin komai na basu, shi kuma ya faɗama Yaya Musaddiq komai tun daga farko. Sosai naga farin cikin abinda nai ɗin a fuskar Yaya Musaddiq, har takai ya kasa haƙuri ya dafa kaina da faɗin, “ALLAH yay miki albarka Kandalata. Abinda kikayi shine dai-dai, dan nima anan banga wani dalilin da za'a baki ƙyauta harta mota ba ki amsa. Ki cigaba da haka, dan gaskiya itace RUHIN dukan MUSULMI na ƙwarai. Sannan ita mace tana bine ta kowacce hanya domin kare mutuncinta da kimarta a al'adance da kuma addinance.”
“Nagode Yaya”.
Na faɗa cikin zumuɗi da jin daɗi. Dan kalamansa sun ƙaramin ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske. Ganin Mansoor bai tanka ba na ɗan juyo na kallesa. Murmushi ya sakar min, nima sai na mayar masa da murtani. Kaina tsaye na ce, “Amma kaima zaka maida musu?”.
“In sha ALLAHU”.
Ya bani amsa cikin tabbatarwa. Nan ma nayi farin ciki, daga haka na mance da dukkan damuwata muka koma hira mai daɗi. Harga ALLAH ina matuƙar son waɗan nan mazajen biyu, dan sunada matuƙar muhimmanci a rayuwata. Sun kuma taka rawa mai ƙarfin gaske da in har zan nuna kaina sai na haɗa da koda inuwarsu ce. Ko kaɗan bamuyi maganar videon nan a wajen ba saboda tsaro, sai da muka koma motar Mansoor sannan muka ƙarasa. Yaya ya bada shawarar mu binciki ɗan sanda mai gaskiya da zamu iya damƙama video ɗin kawai batare da sunanmu ba, kokuma mu haƙura a gogeshi mubar zancen, ko bajima ko ba daɗe idan har halin mutumin nan ne hakkin rai bazai barsa ba. Amma maganar yin fito-na-fito da shi bama ta taso ba a garemu.
Harga ALLAH maganar Yaya Musaddiq bata mun daɗi ba, taya kawai dan mutum nada kuɗi a dinga nuna tsoronsa haka bayan akwai hujja mai ƙarfi a tare da mu. Amma sai na danne yanayina nace mu sakesa a media kawai, dan a wannan zamanin banga wani ɗan sandan da suke hasashen samu ba. Su duka basu goya da bayana ba. Shima Mansoor yana bayan shawarar Yaya Musaddiq ɗin ne. Dole nima nabi ra'ayinsu, duk da tun farko dama ni na fara kawo shawarar kaiwa ƴan sandan, banbancin shawarar tasu da tawa ƙalilance. Bayan mun kammala tattaunawar munbar Yaya anan ni kuma Mansoor ya wuce kaini gida. Muna tafiya muna hirarmu mai daɗi, duk da yaso mu tsaya muci abinci naƙi yarda da hakan. Koda mukaje gidan ma sai da muka ɗan ƙara taɓa hira, duk da dai hirar tamu ma dai akan bikinmu ne, dan iyayensa zasu sake zuwa a satin sama domin saka rana. Ya kuma tabbatar min da bawani lokaci mai tsayi za'a saka ba. Dan shi ya gama kammala komai amarya kawai yake jira. Naji kunyar furucin nashi sosai, dan haka na ɓalle murfin motar na fita abina. Ina jiyo sautin dariyarsa ban kulashi ba, sai da zan shige gida gaba ɗaya ne na juyo. Ido ɗaya ya kashe min, aiko nai wuff na afka ciki..
A falo na samu duka mutanen gidan tsaye carko-carko har Abbas yau yana gida. Ga kayana a barbaje an musu filla-filla. “Yauwa ga ɓarau-ɓarau ɗin nan ta dawo”. Furucin Bibaa ya dawo da hankalina kansu. Kafin nai wata magana kawai naji saukar mari. Duk da azabarsa ta matuƙar ratsani banyi ko gezau ba. Sai wanda ya marenin na zubama ido kawai, ba kuma kowa bane face Abbas. Nunani yay da ɗan yatsa tamkar zai tsokale min ido ya ce, “K dan uwarki kawo sarƙar Mom da kika sata, shegiya ɓarauniya mai kama da aljanun daren salla”.
Cikin dakiya irin tawa na ce, “Karka sake zagar min uwa. Sata kuma kanku ya kamata ku bincika, tunda kune ke shiga ɗakin Mom ɗin ai. Ni ba ɓarauniya bace, kuma in sha ALLAHU babu wani tsananin rayuwa da zaisa na aikata ta”.
Daga haka na duƙa domin tattare kayana. Amma sai ji nai an shaƙoni ta baya. Har hijjab ɗina na matsemin maƙoshi. Da sauri nasa hannu naja hijjab ɗin sama. Sannan na miƙe. Baby ce mai riƙon nawa yanzu, itama hannu ta ɗaga zata maran, sai dai kafin ta sauke min ni na sauke mata nawa yatsun biyar akan farar fuskarta. Saurin janye nata hannun tai tare da sakina ta haɗa duka hannuwanta biyu ta riƙe kuncinta. “Karki soma fara wannan wasar dani a gidan nan, shima daya maran ɗin ba ƙyalesa nai ba balle ke shashasha”.
“Toni bari na marekin sai ki haɗa ki rama” Mom ta faɗa tana wani zaburowa kaina. Banyi ko motsi ba harta ƙaraso ta maran ɗin a haggu da dama. Sannan ta shaƙoni. Kakari na fara, amma ko gezau bata da alamar sakina. Sai ma faɗi take, “Dan ubanki ina sarƙata? Ina kikaje kika saida ta? Dan nasan fitar da kukai ke da annamimin mai saki yin komai a gidan nan abinda kuka je saidawa kenan. Kuma wlhy bazan yarda ba, sarƙata ko kuɗinta”.
Zuwa yanzu kwata-kwata bana iya numfashi da ƙyau, hakan yasa Abba da tun ɗazun baice komai ba ya ƙaraso da sassarfa yana ƙoƙarin cire hannun Mom ɗin daga wuyana. “Kinga Jalilah saketa Please. Sakarta ta faɗa inda take kada ki kasheta mana”. Sam bata da alamar sakin nawa kuwa. Dan haka ya tureta da ƙarfinsa har sai da tai taga-taga zata faɗi, ni ma dai zubewa nai a wajen ina sauke wahalallen numfashi a gwagwgwame. Ga tari dake neman sarƙeni. Da sauri auta yazo gabana ya duƙa yana miƙamin ruwa. Banyi musu ba na amsa, dan ina buƙatarsa. Sauri-sauri na fara sha, sai ji nai an kaɓe ruwan ya zube jikina gaba ɗaya. Yayinda Auta ya fasa wani kukan azaba. Da sauri na tashi zaune, dan bata ruwan da aka zubarmin nake ba ta shi nake. Yaron na sona sosai a gidan, kawai dai dan baida yawan magana ne sai idan shi yaso, dan miskili ne na bugawa a jarida. Ba komai akai masa ba, Baby ce data figesa daga kusa dani kawai yake ma ihun kuka, Bibaa kuma na huci alamar itace ta kaɓar da ruwan da ya bani......
✨(☯෴☯)(☯☯)(☯෴☯)✨
Badan Maash yaso ba dole ya shirya suka fita da Baba prof.. zuwa Company, daga can suka tsaya sukaci abinci a wani haɗaɗɗen restaurant. Daga haka suka wuce airport domin masa rakkiya, dan ya rasa jirgin sha biyu sai ya sake bucking na yamma. A hanyarsu ta zuwa airport ɗin ne Baba prof.. ke tsegunta masa yama yarinyar da tai hira da shi ɗazun ƙyauta amma ta dawo masa da shi. Dan haka mamakin yarinyar ya kasa barinsa har yanzun.
Shiru Maash dake saurarensa yay tamkar bai ji ba. Sai dai a ransa faɗin yake (Ai bazata amsa ba. Ita dake harin miliyan ɗari biyar). “Wai baka jini bane?” Baba prof.. ya katse masa tunani. Cikin basarwar tasa da magana ciki-ciki ya ce, “Ban san mi zance bane Grandpa”.
“A komai ai dama kai baka da abin cewa. Ko akan hirar ya kamata ma ka tambayi dalilina nayin hakan, amma ka share abinka. Awwab wai yaushe ne zaka canja? Anya matar da zaka aura zata iya ɗaukar wannan baƙin halin naka kuwa?”.
“Ni nace zanyi aure ne?”.
Ya faɗa a wani yanayi mai kama da jin zafi. Murmushi kawai Baba prof.. yay yana girgiza kansa. Sai kuma ya ce, “Oh haka zakaita zama kenan?”.
Bai tanka masa ba sai ma ɗauke kansa da yay. Shima Baba prof.. ɗin sai bai sake magana ba har suka iso. Sama-sama sukai sallama, batare da yaga tafiyarsu ba ma yace Tijjani ya juya da shi gida.