Sashe 17
Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar duk abinda ake a office ɗin mu suna kallo ne live dama mutane wata kalar gagarumar tarba muka samu. Musamman ma ni. Dan mata-matan staffs ɗin nan namu rungumeni suka dinga yi da kwarzanta ƙoƙarina. MD kam bakinsa tamkar zai yage ne. Wannan abin alfaharine a garesa ace mutum kamar Maash ya amsa gayyata da ga gidan tvn sa a gaɓar da kowa ke matuƙar buƙatar hakan. Oho su suke shirmensu ni nawa hankalin ma ba'a kansu yake ba. Maganar kisan can ne yay matuƙar tsaya mun a rai da zuciya. A dalilin sallar la'asar na samu damar zame musu. Dan bamu tsaya munyi acan ba kasancewar an tashi gab da za'a fara kiran salla. Ana idar da salla na MD yace muje gida mu huta. Haka dama nake buƙata. Dan burina kawai na keɓe da Mansoor na ji yaya za'ayi da batun video dake a cikin wayata. Muna barin office ɗin kam zancen dana fara masa kenan. Shima da alama abinda ke cimasa rai kenan. Dan haka muka shiga tattaunawa. Koda ya isa dani ƙofar gida ma ban fita a motar ba. Zancen muka cigaba da yi. Ni dai ina a matsayar mu kaima hukuma video ɗin. Tunda dai duk hanyar da zasu bibiyi batun gawar zai zama mai sauƙi kasancewar ya faɗi inda za'a kaita. Amma sai Mansoor ya ce nadai bashi dama yayi nazari tukunna. Na kuma tura masa video ɗin. Babu musu na tura masa, nima na adana wanda ke wayar tawa da ƙyau duk da babu wanda ke taɓamin waya ma. Daga haka mukai sallama ya wuce ni kuma na shiga gida. Dan Yaya Musaddiq na wajen aiki........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_
........Daga ajiye Samraah gida ya wuce shima. Sama-sama ya amsa gaisuwar maigadin su ya shige ciki. Shi da ɗan uwansa a duk sanda suka dawo gida idan sun fita sukan fara shiga sashen iyayensu ne, musamman ma shi da akance yanada ƙulafucin uwa. Amma yau sai hakan ya gagara garesa. Dan ko motar tasa yau a gab da sashensu ya ajiyeta. A falo ya samu yayansa kwance cikin kujera yana kallo, hannu kawai ya ɗaga masa nan ma yay shigewarsa ɗakin barcinsa. Da kallon mamaki Attahir ya bisa. Dan abune da bai saba gani ba. Amma sai ya ɗan girgiza kai da sake maida kansa ga tvn da yake kallo, zuciyarsa na ayyana masa maybe ya gaji ne. Ya cigaba da kallonsa da tunanin idan yay wanka ai zai fito ya nema abinci, amma shiru kake ji har magrib na neman yi. Tsam ya miƙe ya nufin ɗakin nasa, ya ɗanyi knocking, kafin ma a amsa masa ya tura ya shiga.
A tsaye ya samu Mansoor na faman kai kawo. Yay masa kallon tsaf sannan ya ce, “Kai wai lafiyarka ka kuwa? Ka dawo ma mutane kana ɗacin rai ka kuma shigo ka rufe kanka a ɗaki. Ko har ka fara tunanin auren ne? To bakai kace kana so ba, kama jirani kayi tsalle ka dire kai ba haka ba.....”
Ganin Mansoor bai maida masa murtanin tsokanar ba yasa Attahir yin shiru, gabansa ya ƙarasa tare da dafa kafaɗarsa. Cike da kulawa ya ce, “Baka da lafiya ne Kiddo?”.
Kai Mansoor ya girgiza masa.
“To mike damunka?”.
“Yaya babu komai fa. Kawai bana jin daɗine”.
Jimm Attahir ɗin yay yana kallonsa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Okay shike nan. Shiga bayi kai alwala mu wuce massalaci. Dan kar Dad yay zaman jiranmu”.
Kai kawai Mansoor ɗin ya jinjina masa yana nufar bayi. Attahir ya bisa da kallo har sai da ya shige. Shima kaɗa kansa yay ya fita yana ji a ransa ƙarya Mansoor ɗin ke masa. Duk da shi mutumin ne mara son hayaniya. Amma idan suna tare baka banbance wannan halin nasa na rashin yawan magana. Dan suna rayuwa ne tamkar abokai ba wa da ƙani ba. Sun tashi ne kamar ƴan biyu, komai nasu a tare yake. A halayyane kawai zaka iya banbance su. Dan tabbas sun banbanta tanan ɗin.
Koda suka fito domin tafiya massalacin sun gamu da Dad ɗin su. Shima dai da mamaki yake kallon Mansoor ɗin. Harma ya gagara haƙuri ya ce, “Kai dama ka dawo gidan kabar Mamanku natama mutane shelarka?”.
Kan Mansoor a rissine ya ce, “Dad amin afuwa na dawo ne kaina namun ciwo”.
“Dole kai ciwon kai ai wannan hidima da kuka sha. Ku muje massalaci za'a tada salla”.
Binsa sukai gwanin sha'awa suka fita har maigadi. Koda aka idar da sallar ma basu fito a massalacin ba har akai isha'i. A tare yanzu ma suka dawo gidan, kai tsaye ainahin sashen gidan suka nufa su duka. Sashene babba kuma mai ƙyau, dan komai yaji na ababen more rayuwa. Lallai gidan su Mansoor suna da kuɗi suma ba laifi. Dan idan wani ne ma zai iya cewa yafi ƙarfin aikin da yake yanzu, duk da kuwa yana a babbar kujera ne. Amma kuma aikin jarida hubby ɗinsa ne tun yana yaronsa. Sannan mahaifinsa nada babbar alaƙa ma da wajen aikin nasu, dan yanada hannun jari mai ƙarfi a cikin companyn. Shigowarsu dai-dai da fitowar ƴammata biyu masu kama da su Mansoor ɗin sosai daga wani ɗaki. Cike da murnarsu suka nufo Mansoor ɗin suna masa sannu, sai jera masa tambaya suke akan Maash. Amma a mamakin kowa ko a yaƙi ya furta, sai ma zagayesu yay ya wuce saman kujera ya zauna yana faɗin, “Malami kun isheni da surutu”.
Babbar ce ta ɓata fuska tana kallon Dad ɗin su. Ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar sunfi kusa. Sake ɓata fuska tai sosai. Ta ce, “Dad kallafa yanda yake basar da mu. Shi dama Yaya Man idan baiso abu ba ya iyama mutane wulakanci”.
“To yayi fitinanniya.”
Wata mata dattijuwa ta faɗa tana fitowa a hanyar dake tabbatar da kitchen ne, itama dai kama take sosai da su Mansoor ɗin. Hararar yarinyar tai da nuna musu hanyar data fito. “Ku wuce kuzo ku fiddo abinci. An gaya muku kowama irinku ne da shegen surutu. Yaro yaje aiki ya gaji kun wani sashi gaba dolene sai ya baku labarin abinda ya farun? Idan son gani kuke miya hanaku zuwa”.
“To an taɓa ɗan lelen Mamy”.
Cewar Attahir na ƴar dariya. Murmushi Dad shima yayi, yayinda Mansoor ya miƙe ya nufeta yana harar Yayan nasa. Yana zuwa gab da ita ya bata side hug, tare da kamo hannunta ya sumbata. A marairaice ya ce, “Mamy barsu kada ma kanki yay ciwo”.
Kansa ta shafa fuskarta da murmushi. Kafin cikin kulawa ta ce, “Yaushe ka dawo?”.
“Tun ɗazun ya dawo yau baya yayinki ne kawai Mamy”.
Attahir ne ya faɗa yana kaiwa zaune a kujerar dining dan su Islam sun kammala jera abincin. Hararsa Mansoor yayi, tare da faɗin, “Mamy ƙyalesa so yake kawai ya haɗamu. Kaina fa ke ciwo amma nasha magani”. Yay saurin faɗar haka ne dan yasan yanzu zata iya ruɗewa. A hakanma tuni fuskarta ta nuna damuwa. Dan sai tattaɓa kan nasa take, daga ƙarshe dai ta ja hannunsa suka koma saman dining ɗin tana jera masa sannu, abincin ma a baki ta bashi dan kowa yasan ɗan gatan ta ne a gidan. Daurewa yay kawai ya ɗan ci abincin dan karta damu, amma gaba ɗaya hankalinsa na'a kan Samraah, babu abinda zuciyarsa ke hango masa sai yanda take a firgice har sanda ya ajiyeta a gida.....
Bayan sun kammala cin abinci duk yanda Mamy taso suyi hira Mansoor bai cewa komai, zata nuna damuwa Dad ya dakatar da ita akan ta barsa yaje ya huta dole akwai gajiya. Mansoor yaji daɗin samun wannan damar, dan haka ya miƙe ya wuce sashensu. Yana shiga bedroom ɗinsa wayar Samraah yay ƙoƙarin kira. Cikin sa'a kuwa bugu uku ta ɗaga. Sai dai a yanda yaji muryarta na fita a shaƙe ya tabbatar har yanzu tana a cikin damuwa. Daɗaɗan kalamai ya shiga jera mata da lallashi akan ta kwantar da hankalinta. Ba shi yace mata zasuyi wani abu ba. Bafa itace ta aikata laifin nan ba da har zata takurama ranta haka suma dake tare da ita ta sakasu a damuwa. Sosai lallashin nasa yay mata tasiri, dan haka ya yanke kiran yana cewa bari yay shirin barci zai kirata video call. Yana yanke wayar Attahir na shigowa ɗakin, yanda ya kafesa da ido ya sashi duƙar da kansa, fatansa dai ALLAH yasa baiji wayar da sukai da Samraah ɗin ba.
“Mike damunka Mansoor?”.
“Yaya nace maka babu komai”.
“Ƙarya kake yi. Idan kuma zakama kowa wannan ƙaryar ni kasan bazaka mun ba. Dan nasanka fiye da yunwar cikina. Koka sanar min, ko yanzun nan naje na kira maka Mamy da Dad maybe su ka sanar musu”. Ya ƙare maganar da juyawa kamar zai fita. Da sauri Mansoor ya riƙosa yana girgiza kansa. “Please basai ka kirasu ba. Ba wata damuwa bace mai yawa fa”.
“Kasan dai bama ɓoyema juna damuwarmu. Karka fara daga yau to”.
Numfashi mai nauyi Mansoor ya sauke tare da ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana harhaɗo ƙaryar dazai sanar masa dan bazai taɓa faɗa masa gaskiyar zancen ba tunda yayima Samraah alƙawarin haka.....
★💫★💫★💫★💫