← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bata jima ba ta siyo datar ta dawo daman tun a hanya ta kunna datar kafin takarasa gida messages ɗin data tara sun fara shigowa. Whatsapp ta shiga tana duba group ɗinsu na secondary school wanda suka buɗe tun bayan kammala candy. Kusan su goma ne a cikinsa wanda mafiya yawancin su ƴaƴan talakawa ne kamar ta, duk da wasu sun ma fisu rufin asiri sosai. Sosai suke zumunci da junansu idan hidimar mutum ta tashi ana yi masa qara a tafi ko idan mutum ya tashi aure ana bawa mutum wata ƴar gudunmuwa. Duka hirar samari ce suke yi, ta zauna tana karanta yadda samari suka yi tsada a wannan zamanin, kawai sai hirar ta tuna mata da Alkasim. Fitowa tayi daga group ɗin tamkar ance ta kalli sunan Alkasim Galadima da tayi saving tun ranar, kawai taga ya turo mata saqo, zuciyarta ta shiga bugawa tana tsalle da sauri ta duba saqon inda ya turo mata.
"Salam, Ya kike? Kwana biyu."
Ajiyar zuciya ta shiga saukewa a hankali tana qara dora idonta akan rubutun da yayi.
"Da gaske shine!!!" Ta faɗa murmushi na kwace mata. Har zata bashi amsa  wata zuciyar tace tun yanxu taja masa aji. Kashe datar tayi wani irin farin ciki taji na lulluɓe ta. Ranar cikin farin ciki ta yini duk yadda takeso ta kunna datar ko zata qara cin karo da saqon Alkasim ta kasa tana son taji ya qara yi mata magana kafin ta amsa shi duka. Da magariba tana kwance akan katifarsu dake gefen ɗakin, tunda tayi sallar magrib take kwance a wajen, ƙaramar autarsu wato Zaheeda ta shigo ɗakin tana faɗa mata Maman su na kira. Tunda ta shiga ɗakin zuciyarta ke bugawa ganin irin kallon tuhumar da Maman ke binta dashi. Zama tayi kan ledar dake shimfide a ɗakin tana jiran taji abinda Mama zata faɗa.
"Lafiya wayar Nura a kashe? Inata kiransa tunda nadawo daga gidan kawunku har yanzu bai kira ba."
"Nifa Mama mun rabu da Nura tuntuni na faɗa masa ya canja wata bana iyawa da rigingimunsa." Wannan karon zuciyar Mama bugawa take yi. Da tsananin mamaki take ƙarewa Tauheedar kallo.
"Ohhh dama kenan laifinkine ke kika korasa ko?" Maman ta faɗa a hasale kamar zata ɗauke Tauheedar da mari. Ɗan jada baya tayi tana turo baki ta ke faɗin.
"Ni bai mun bane. Kawai Allah ya haɗa kowa da rabonsa." Wannan karon kasa daurewa Mama tayi. Wata roba dake gefenta ta ɗauka tana jefawa a saitin Tauheeda ɗin tana cewa.
"Tashi kibar gabana." Maman ta faɗa a hasale tana jin kamar tayi ta dukan ta. Babu musu Tauheedah ta miqe tsaye ta nufi ƙofar barin ɗakin, dafe kai kawai Maman tayi tana jera. "Innalillah wainnah ilaihir raji'un! Me yasa Tauheedah zata yi musu hakan? Shin da wane ido ma zata kalli wannan yaron?"

Kaduna state...

Tunda ya shigo Zahra ke kallon sa, kana ganin shigar jikinsa kasan daga office yake ko gida bai isa ba. "Taso muje kaci abinci kafin muyi magana." Girgiza kai yayi yana faɗin. "No, na tura mata sako naga ta duba har yanzu bata yi magana ba." Ya faɗa da wani kasalallen yanayi a muryarsa. Zahra tayi dariyar zuci da tasan idan tayi dariya a bayyane hasala zai yi. Ita kam tana mamaki tana qarawa wai yau Alkasim Galadima ne ke bin wata mace ta kulasa. Tana son taga wannan Tauheedar da ta ciri tuta a cikin ƴan mata.
"Maybe tana da wani uzurin ne yasa bata yi maka reply ba." A hasale yake fadin.
"Wane irin uzuri ne zaisa ta kalli saqona takasa magana? Shin batasan ya nake ji a rai na bane? Look nifa natsani jira wallahi." Tab, Lallai ma kuwa. Toh aikuwa jira yanzu kafara mace ce fa Alkasim dole taja aji...." Kalaman Yayar tasa yaji suna qara ɓata masa rai, ace kamar matsayinsa ne zai zauna ya saka damuwar macce har haka ransa yana zafi? Ya faɗa can qasan makoshi. Lokaci ɗaya Zahra taja kumatunsa kafin taja hannunsa zuwa cikin dining area. A hankali take faɗin. "Komai zai zama daidai bro karka wani damu, Tauheeda zata zama taka duka me kake yiwa sauri? Wata kila dai tana da wani uzuri da yasa bata kula saƙon ba, mujirata mugani." Haka ta kwantar masa da hankali ta saka sa yaci abinci sosai shi kansa yayi mamakin abincin da yaci, daga nan gida ya wuce, sai dai tunda yabar gidan Zahra ya kunna datarsa yabarta a buɗe saqon Tauheeda kawai yake son ji ko sallama ce so yake ta amsa masa ko zaiji sanyi domin rashin ganin amsarta yana ƙokarin kwantar dashi. Yau duk meeting ɗin da yayi a kamfaninsa kasa fahimtar komai yayi haka ya riqa bin kowa da ido har aka watse bai gama fahimtar komai ba, sai da PA ɗinsa ya tsaya ya karasa sauraran abubuwa..

Kano state.

A yinin ranar Mama ta riqa daurewa Tauheeda fuska duk inda ta wurga harara ce take binta dashi, shi yasa Tauheeda tayi zamanta a ɗaki, duk da tana son taje gidansu Fauzy. Sai da tazo kwanciya sannan ta buɗe datar ta. Kasa daurewa tayi a wannan karon ganin jan ajinta zai kaita ya baro ta. Turawa Alkasim sallama tayi, tamkar yana jiran hakan tuntuni sai taga ya soma typing. Ɗan murmushi tayi tana wani juya ido. "Sai yanzu kika ga daman amsani? Toh nayi fushi." Ya faɗa da dukkan gaskiyyarsa tamkar wani qaramin yaro. Hakuri tabasa kafin ta ɗora da faɗin. "Uzururukane suka yi mata yawa, kuma datar ce kawai a buɗe. Daga nan kuma suka soma hira sosai tamkar sun san juna. Sai kusan sha ɗaya na dare suka aje wayoyin cike da wani irin nishaɗi a zuciyoyinsu tamkar sun jima da sanin junan su. Tunda ya shigo Ammi ke kallonsa tana kallon yadda walwala ke yawo akan fuskarsa. Zama yayi akan bedside drower yana shafa dogon wuyan sa. Yafi minti ashirin zaune a wurin kafin mamin ta idar da azkar ɗin da take yi, ita kanta tayi mamakin dawowarsa daga masallaci da wuri haka, dan yana kai karfe bakwai a masallaci kafin ya shigo gida. Sauka yayi daga kan bedside drower ɗin ya ɗora kansa akan kafafun mahaifiyarsa lokaci ɗaya ya lumshe idonsa masu cike dajin bacci. shafa kansa da tayi yasa ya ɗan buɗe idon da suka fara canja kala. Hamma yayi yana ɗorawa da faɗin. "Sabahul khair mami." Cigaba da shafa kan nasa tayi tana faɗin. "Sabahul noor Habeebin mami, meya hanaka bacci jiya da wuri bayan da wurin ka kwanta?" Ɗan matse idonsa yayi kafin ya buɗe su akan mahaifiyarsa, ɗan murmushi yaji ya kwace masa tuna irin hirar da sukayi da Tauheedah a daren jiyan. Miqewa yayi tsaye yana shafa sumar kansa still wearing a big smile akan fuskarsa. Kallonsa kurum mamin tayi jin yaki magana, girgiza kai tayi ya nufi ƙofa yana faɗin. "Mami bara naje na ɗan kwanta zuwa 9 zan fita office akwai kayan da za'a kawo yau." Da haka ya nufi ƙofa ya fice daga dakin yana rufo mata ƙofar. Numfashi ta sauke kamar kullum tana roqarwa Alkasim ɗin nata macce tagari.

Kano state.
Chapter 9 · 0% Book details