← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda ta tashi daga baccin safen  mahaifiyarta bata gidan da alamar yau ko kokon safen da suke siyarwa ba'a yi ba, su Waheeda suna makaranta Ita kaɗai ce a gidan. Tauheedah ta kalli tulun wanke-wanken dake jiran ta, daman kuma ita ke da wanke-wanke a yau. Kafa ta saka ta riqa harba su tana addu'a Allah ya turo Alkasim a kwanan nan ayi maganar aurensu ta fara hutawa da aikin da mahaifiyarsu ke tula musu tamkar xaya kashesu. Tana jin yadda hanjin cikinta ke wani kullewa saboda yunwa. Bokitin kunun da ta hango ne yasa ta nufesa kai tsaye ta buɗe. Ragowa ne kawai aciki tasan  nata ne. Wani irin matsewa zuciyarta tayi cike da takaicin kokon da ta gani. Ta buɗe langa ragowar kosan rogone da bai wuce kwara shidda ba. Zama tayi a ƙofar kitchen ɗin tana jin hawayen bakin ciki na cika idanun ta. Yanzu ɗan wannan abun ne zai isheta tayi kari? me yasa talauci zai zabi gefen su? me yasa talauci zai zabi ɓangaren ta har biyu? me yasa bazai ɗauki ɗaya yabar ɗaya ba? Daga Mama har Abbansu babu mai arziki a cikinsu. Jin irin karar da cikinta keyi yasa ta saka kokon agabanta tafara sha. Tunda mahaifiyar Nura ta buɗe baki tana korawa Hadiza bayani jikin Hadiza yayi wani irin mugun sanyi da mamakin Tauheeda da ya kusa kasheta a zaune. Wani irin kunyar mahaifiyar Nuran yazo ya lullube Mama lokaci ɗaya. "Karki damu Maman Tauheeda haka Allah ya tsara daman Allah yayi can ba matarsa bace." Inna ta faɗa da sanyi murya. Kasa zama Hadiza tayi karkashin innuwa ɗaya da Innar Nura, ji tayi wani nauyin matar na danne mata kirji. Sallama tayi mata kawai tabar gidan. Koda ta koma gida ko kallon inda Tauheeda ta ke ba tayi ba. Sai kusan sha biyu suna da garin kwaki da kuli-kuli shi ta jiqa ta kwadawa su Waheedah suka ci. Bayan su Waheeda sun dawo daga makaranta data kalli yanayin Mamar tasu, sai da ta tambayeta wani abu ya faru ko batada lafiya? Numfashi ta sauke daman jira take ta raba wannan damuwar da waninta. Nan ta fadawa Waheeda aika aikar da Tauheedah ta yiwa Nura. "Kuma Mama kika kyaleta.?" Waheeda ta faɗa da wani irin rawar murya, tausayin Nura na mamayar zuciyarta. "Yaya Tauheedah taci amana Allah bazai barta ba Mama." Mana tace, "Ki kyaleta kawai kowa yayi nagari dan kansa." Tana idar da sallar la'asar daman ta nufi ɗakin Maman su ta lura yadda mamar ke wani shasshareta haka ma kanwarta Waheeda. "Wai wani abu ya faru ne Mama?" Tauheeda ta faɗa tana kallon Maman dake tsintar wake." Jin shiru Maman taki magana yasa Tauheedah ta dawo gaban mahaifiyar ta. "Wai meya faru ne Mama?" wannan karon ta faɗa da sanyi murya, duk rawar kanta ba ta son ganin ɓacin ran Maman su. Wata irin harara Maman ke aika mata, kafin ta ɗora da faɗin. "Harma tambaya kike mai ya faru?" Turo baki Tauheedah tayi, yanxu tasan zancen, watau akan Nura Maman ke wani shareta. "Ni dai na faɗa miki kawai mu hakura da Nuran nan addu'a kawai zaki yi mun Allah ya bani wanda yafi shi." Tauheeda ta faɗa tana karɓar waken da Maman ke gyarawa ta cigaba da tsincewa....

#Tauheeda Baffa
#Alkasim Galadima
#Lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/22, 1:43 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
PAID BOOK

Asmy b Aliyu

8...

"Ni wallahi nagaji!!" Ya faɗa yana kallon Zahra Galadima dake binsa da ido. Gyada kai ta shiga yi tamkar wata kadangaruwa. "Sati biyu ne fa duka-duka da haduwarku, kana ganin bai yi kusa ba manya su shiga maganar nan? ya kamata ku ƙara sanin junanku Kasim ban san saurin me kakeyi ba."
"Ta faɗa mun komai nata Yaa Zahra, Kuma nima tasan wani abun ta wurina. To jiran me zamu yi? Nidai kawai ki faɗawa Yaa Hajja suyi magana da mami kwanan nan zanje Kano gidansu mu sake gaisawa." Shiru Zahra tayi masa tana danna wayar hannunta, ita har tsoron soyayyar da Kasim ɗin yake yiwa Tauheedah take yi. "Kinyi shiru kina danna waya." Kasim ya faɗa cike da ƙosawa. Shifa baiki ace gobe Tauheedah Baffa ta zama mallakinsa ba dukanta. Shi yana ɗaya daga cikin mutanen da basa son jira ko kaɗan,
Idan yana son abu zai yi sauri ya mallaki abunsa ne babu ɓata lokaci. To me yasa Yayarsa ke faɗin ya jira? Jiran me Zai yi? Kullum fa suna tareda Tauheedah a waya, duk wani motsi da zatayi a waya yana jinsa har kasan zuciyarsa. Yayi ƙoƙari sosai wurin karantar halayyarta cikin hirar su.
Miqewa yayi tsaye hannayensa duka biyun zube cikin aljihun wandon shaddar dake jikinsa.
"Ki kirata dan Allah kar ya wuce yau Yaa Zahra." Ya faɗa yana ɗan shagwaɓe mata fuska. Murmushi tayi tana ɗan juya ido alamar ta ji. Daga haka ya mata sallama ya fice daga gidan. Bayan fitarsa ta kira Yaa Hajja har sau biyu bata ɗauka ba, sai ta hakura dan tasan tana wata hidimar ne idan tagama zata kirata.

KANO STATE.

Tunda tayi sallar asuba takasa komawa baccin datake na safe, ta kasa yadda Alkasim ne zai zo gidansu dan ya ganta. Har kuma lokacin takasa sanar da Mama cewa Alkasim ɗin zai zo tun daga Kaduna dan su gaisa gashi bata da kuɗi a hannunta, gidansu ba kalar cimar ƴan gayu aka sabaci ba, shinkafa da mai da yaji ne dai ɗan kullum. Yanzu dai zata samu ta yiwa Mama daɗin baki ƴan kudaden dake hannunta ta bata taje wani eatry ta samar masa abincin ƴan gayu ko zata fita kunyarsa. Da wannan tunanin ta miqe tsaye ta nufi tsakar gidan dan har Mama ta fito tana hadadar ɗora ruwan kokon da take na siyarwa. Gaishe da Maman tayi Maman ta amsa fuska babu walwala dan tun abunda ya faru na Nura bata ƙara sakarwa Tauheedah fuska ba. Cigaba da aikinta tayi ta shareta tamkar batasan tana tsaye a wurin ba. Gabaki ɗaya jikin Tauheedah yayi sanyi gashi Alkasim yace mata da wuri zai zo ya ganta su sha hira, ya faɗa mata kuma a jirgi zai zo saboda ya iso da wuri. Hijab ɗin da take sanye dashi ta shiga wasa da ƙasansa gabaki ɗaya ta ruɗe ta rasa ta inda zata fara. Cikin rawar murya take faɗin.
"Daman Mama sabon sauryina ne zai zo yau, kuma a Kaduna yake da zama shi da iyayensa."
"Allah ya kawosa lafiya." Maman ta faɗa ta cigaba da hidimarta.
"Toh Mama me za'a haɗa masa na tarbarsa?" Wani irin kallo mahaifiyarta ke bin ta dashi kafin ta girgiza kai ta ɗora da faɗin.
"Idan anyi ɗan wake da rana sai kizuba masa a kula a aje masa." Cikin rawar murya da rawar baki Tauheedah take fadin.
"Mama ɗan wake fa? masu kuɗi ne fa gidan su wallahi bakiga motar da yake hawa ba. Yanzu haka jirgi zai biyo yazo waje na." Tauheedah ta faɗa tamkar zata fashewa Maman da kuka. Baki buɗe mahaifiyarta ke kallon ta tace,
"Auhh Allah? Ashema suna da kuɗi ko? masu kuɗi basacin ɗan wake ne? to idan bixaici ba ki hakura idan yazo kibasa ruwa kawai....." Fashewa da kuka Tauheedah tayi kamar wacce zata tsage taba cewa.
"Mama ki dubi girman Allah ki haɗa mun cinakin kokonki naje restaurant na samar masa wani abun. Allah nayi alkawarin zan ninka miki kuɗinki, nasan idan yazo zai bani."
"Bani dashi anjima dashi zan siyo gero a kasuwa. Tunda Allah ya ɗora miki wahalar karya ai sai kiyi ta yi." Juyawa Tauheedah tayi ta koma ɗakin su. Sosai hawaye ke rolling akan fuskarta. Taya zata baiwa babban mutum kamar Alkasim ɗan wake? itama ai dan ya zamar mata dole ne ta ke ci, idan ta kai masa wannan bakin abun ai kunya zatayi. Gefen katifa ta koma ta zauna ta ɗauki wayarta tana neman layin Fauxy ƙawarta. Bata jima ba tana ringing ba ta ɗauka cikin muryar bacci tayi sallama.
"Dan Allah ki tashi daga wannan barcin muyi magana yadda xaki fahimce ni."
"Kibarni Tauheedah nayi baccina idan na tashi zamuyi magana." Da sauri Tauheedah ke faɗin.
"A'a dan Allah karki kashe. Please daman dubu goma zaki aramun dan Allah xuwa gobe zan baki."
"Kin san dai munyi hidima account ɗina yayi ƙasa."
"Haba mana Fauxy ni ce fa ƙawarki Tauheedah ki taimakamun."
"Naji idan na tashi zan tura maki."
"No please kiyi hakuri yanzu dan Allah ina matuqar bukatarsu kusa." Tsaki Fauxy taja tana faɗin
"Kedai wallahi manyya ce!" Ɗan juya ido tayi tamkar tana ganinta take faɗin.
"Na dai ji." Da haka suka sauke wayar ba'a yi minti biyar ba Fauxyn ta tura mata da kuɗin daman kuma tana da account ɗinta.

KADUNA STATE
Chapter 10 · 0% Book details