← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 16

Sashe 13

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da rawar jiki ta shiga cikin gidan su tana kwalawa Maman su kira. Kai tsaye faɗawa tayi cikin ɗakin tamkar zata faɗi ta karasa a gaban Mama ta sauke ledar ƙasa ta zauna dabas a ƙasa ta cire mayafin kanta da ɗaurin da tayi tana cewa.
"Mama kinga ikon Allah koh??" Me nake faɗa miki tuntuni. Hmmm Mama ai wani jinkiri alkhairi ne wallahi." Tasa hannu tana fito da manyyan atamfofin dake cikin ledar da kuma turarruka masu tsadar gaske. Ɗaga atamfofin ta shiga yi tana cewa.
"Kin gani ko Mama. Mahaifiyarsa ce tasa ya kawo mun." Turarrukan ta ɗauka ta shiga juyasu tana misalta irin tsadar da xasuyi. Sai kuma rafar 1k har rafa biyu. Wani irin ihu Tauheedah ta saka tana kankame kuɗin a cikin ƙirji. Tamkar wata zararra take fadin.
"Mama me na faɗa miki? Na gaya miki suna da kuɗi sosai. Mama naira dubu ɗari biyu fa." Ta faɗa sounding so very happy. Ita dai Mama har lokacin kallon Tauheedah take wacce tabi duk ta rude.
"Sai kiyi addu'a kiyi istikhra ki nemi zabin Allah idan alkhairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba alkhairi bane Allah ya musaya miki da mafi alkhairi." Da sauri Tauheedah ta katse Mama tana faɗin,
"Mama Alkasim alkhairi ne ma a wuri na ki daina faɗar shi ba alkhairi bane dan Allah." Ta miqawa Mama rafa ɗaya ta kuɗin da Alkasim ɗin ya bata
"Mama ga wannan dubu dari ɗin a siya mana kayan abinci masu kyau na ƴan gayu muci musha mu more. Mama nasan abincin yau harda kaza da lemu. Wannan kuma dubu dari ɗin zan cire bashin da ake bina na cire kuɗin ɗinkin wannan atamfofin na miqa next zuwan da za yayi yaga na ɗin ka su zaiji dadi." Daga haka ta kwashi kayan ta nufi ɗakin su sai juya manyyan atamfofin take. Tabbas da yamma bata yi ba ai gidansu Fauxy zata wuce. Abincin da Alkasim ya rage shi taci ta samma kannenta sauran. Sai bayan magrib ta ƙara kiran Alkasim, tunda ta kira wayarsa bata shiga sai takasa samun natsuwa. Wannan karon wayar ta shiga sai dai har tagama ringing bai ɗauka ba. Saqo ya tura mata akan yana tare mami idan ya gama zai kirata. Sai wuraren qarfe 9:00pm Alkasim ya kirata ta tambayesa ya sauka lafiya? Ya amsa da alhmdulillahi. Ta tambayesa mami fa? ya faɗa mata tana lafiya. A nan ta tambayesa lambarta yace zai tura mata idan sun gama waya. Wayarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, dakyar ta samu ta lallaɓashi sukayi sallama tace ya kwanta ya huta shida yayi tafiya. Suna gama wayar ta kunna data ta shige Ig neman styles ɗin da zai dace da atamfofin da mahaifiyar Alkasim ta ɓata. Acan ta gantale tana ta kallon ƴan gayu yadda suke gudanar da rayuwarsu suke daukar pics. Itama harta fara hango kanta haka gidan Alkasim. Ita kaɗai ta riqa sakin murmushi. WhatsApp ta koma ta turawa Fauxy atamfofin da aka bata da turarruka. Taci sa'a Fauxy na online nan take ta tura mata v.note tana faɗa mata tsadar atamfofin. Wani irin juya ido Tauheedah ta shiga yi tana jin kanta na ƙara girmama, haka ta riqa baiwa Fauxy labarin yadda Alkasim ya karɓi ƴan gidansu ba kyama babu komai, ta faɗa mata gobe zata shigo idan ta kai ɗinkunanta wurin telan dake mata ɗinki.

Washe gari...

Tea da bread aka sha a gidan da wainar kwai sanin halin Tauheedah yasa Mama tasa Waheeda taje bakin titi ta karɓo bread da kwai, amma duk da haka bazata biyewa Tauheeeda ba adana kuɗin zata yi, idan anzo maganar aurenta me suke dashi da xasuyi mata kayan daki? tasan dai Kawu shima takansa yake ko tabarma bata da tabbacin da zai siyawa Tauheedah. Sauqinta ɗaya tana adashi da ƴar sana'ar da take. Suna gama karin kumallo daman Tauheeda ce da wanke-wanke ranar, almajiri ta samo yayi mata wanke-wanken tunda tana cikin kuɗi dari biyu ta basa. Mama ta yiwa sallama tace zataje ta kai ɗinki har ta juya sai kuma ta dawo ta kalli Maman tana tambayar me za'a dafa?
"Duk abunda ya samu." Maman tabata amsa. "Mama ko za'ayi taliya da wake da kifi ina marmarinta. Dan Allah Mama ayi da wuri zan dawo." Da haka ta fice daga gidan cike da nishaɗi.....

#Tauheeda
#Lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/23, 2:08 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*

Asmy b Aliyu

10
Wani irin rashin gudu taga satin yayi mata, Ita kanta batasan meyasa take qirga kwanakin da Alkasim ya ɗibar musu ba akan zai dawo ya nemi auren ta. Gabaki ɗaya gani tayi satin baya gudu kullum cikin kirga kwanaki take amma shiru. A gefe ɗaya kuma kullum suna manne a waya suna zuba wata irin soyayya kamar ɗaya ba zai iya rayuwa idan babu ɗaya ba. Kamar yadda Alkasim yayi mata alkawarin turo mata lambar mami, ya tura kuma ta kirata, mace mai kirki da fara'a da sanin ya kamata. Tun kafin taganta farat ɗaya taji tana qaunar matar. Hakan ne yasa duk bayan kwana biyu sai Tauheedah ta kira sun gaisa. Ana gobe iyayen Alkasim zasu zo ta samu Mama da zance.
"Allah ya kawosu lafiya munyi magana da Kawunku yace zai zo nan shi da amininsa su tarbi su Alkasim ɗin." Bakaramin mamaki Tauheedah tasha ba jin Kawu zai zo gidansu ya tarbi mahaifan Alkasim, lallai idan kanada kudi babu abinda ba za'a iya yi maka ba.
"Toh Mama me za'a tanadar musu wannan qaron? Ina nufin ɗan abun motsa baki haka snacks  da drinks."
"Kedai wallahi baki da kunya." Mama ta faɗa tana aikawa Tauheedah harara ta saitin ta. Tura baki gaba Tauheedah tayi tana cewa.
"Nidai gobe ayi musu order na snacks sai a haɗa da lemu abasu kinsan manyyan mutanen nan sai da iya taku Mama." Gyaɗa kai kurum Mama tayi tana nemarwa Tauheedah fatan shiriya. Da daddare da suna waya da Alkasim ce mata yayi ya kasa bacci ji yake tamkar ya jawo gobe dan kawai ya ganta. Yau sun daɗe sosai suna waya dan raba dare sukayi sai kusan qarfe biyu suka sauke wayoyinsu.

KADUNA STATE

Yaah Hajja sai bin ƙanin nata take da ido yadda yake rawar ƙafa sai kai da kawo yake yi.
"Wai ba zaki yi masa magana ba ya samu ya saka wani abu a cikinsa kafin su tafi? tea kawai yasha fa.? gashi tafiyar mota ce xasuyi." Mami ta faɗa tana kallon Yaah Hajja.
"Kema dai mami da neman zance kike, Alkasim ne fa. Alkasim za'a lallaɓa yaci abinci? Kawai kibarsa zai nema da kansa yaci."
"Nifa bana jin yunwa gabaki ɗaya mami, kuma kinga tea da nasha yanada yawa."
"Zumudi ne yake yi kuma da murnar zai mallaki Tauheedah ina maganar cin abinci!" Zahra Galadima ta faɗa tana ƴar dariya. Shi dai bai kulata ba dan yanzu yasan da ya yi maganta zata  riqa zolayarsa, ko maganar aurensa da yace a saka wata ɗaya ma ya isa, Zahra tayi cikinsa tana faɗin.
"Wata ɗaya yayi musu kaɗan, su suna da shirin da xasuyi." Haka mami ta saka baki abarsa a wata biyun kamar yadda Abba  ya tsara. Ba ƙaramin haushin hakan Alkasim yaji ba saboda ko cikin kwanaki 3 ɗin nan suna iya haɗa lefe kasancewar Zahra Galadima tana da babban shop na siyarda atamfofi da laces da duka kayan mata na ado. Da sun saka baki sun dage Abba zai iya barinsa a wata ɗayan shi baiga jan lokacin da ake ba wata biyun nan kamar shekara goma yake jinsu a kansa. Har mota mami ta rakasa da foodflaks su Zahra sai dariya suke masa. Bayan tafiyar su mami ta dubi duka ƴaƴan nata tana neman shawarar yadda zasu tsara komai, dan bata da kamarsu a duniya, dasu take shawara dasu take komai sun zama manyan aminanta dan mami ko ƙawa bata da sai dai a haɗu ayi zumunci, ƴaƴanta su ne sirrinta su ne komai nata, kasancewar mami ita kaɗai ce mahaifanta suka haifa har suka bar duniya, bata da ɗan uwan da suke ciki ɗaya. Sai dai dangin dake xagaye da ita wanda gasu nan ta ko'ina. mami ta kalli Zahra ta numfasa kafin tace.
"Lefe shine abu na gaba da za'ayi maganar haɗawa yanzu tunda har kuɗin saka rana da sadaki duk yau zasu kai."
"Kamar nawa kike ganin za'a kashe Zahra?"
"Mami ko lefen miliyan ɗaya ina haɗawa a rana ɗaya. Kawai dai abun iya kuɗinka iya shagalinka."
"Haka ne kuma. Toh shikenan zan tura miki 5m a account ɗinki sai a haɗa idan bai isa ba sai a ƙara." Daga nan ta dubi Yaaa Hajja tana faɗin.
"Ko bai yi ba ne Hajja? Meye shawararki?" Da sauri Yaa Hajja ta girgiza kai tana ɗaga hannayenta duka biyu sama tare da cewa.
"Komai yayi sosai mami, Allah ya saka da alkairi. Ni na ɗauki ɓangaren shoes da handbag Zarah kiyi mun list ɗinsu ko wane sha biyu-biyu zaki saka." Cike da murna mami ke faɗawa Yaa Hajja.
"Angode Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi." Mami ta juya kan Zahra tana cewa,
"Ke kuma me zaki yi mana?" Zarah tace,
"Mami zan duba nagani kin san halin yaron naki Allah yasa kar ya raina. Jin dadina ɗaya Najma na ƙasar nan za'a yi wannan bikin yadda ta ɗauki buri akan bikin Alkasim Galadima." Daga nan hirar bikin suka shiga tattaunawa.

KANO STATE
Chapter 13 · 0% Book details