← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari.
Mama bayan tagama duk ayyukan da zatayi a gidan kusan qarfe goma ta shigo ɗakinsu Tauheedah bacci ta samu ta nayi, girgiza kai tayi cike da takaicin yartata haka zatayi aure tana wannan barcin hasara babu aikin fari barantana na baki. Tashinta ta shigayi dakyar Tauheedah ta buɗe ido ganin mahaifiyarta yasa ta ɗan tura baki alamar an katse mata dukkan jin daɗin ta.
"Ki tashi ki ɗora girkin rana kafinsu Waheeda su dawo daga makaranta ni zanje na sanar da kawunku magabatan Nura zasu zo neman aurenki, nayi ta kiran wayarsa tun jiya amma a kashe kila yayi halin nasa ya siyar tunda bai iya riqe waya a hannunsa, sai kin tsince shinkafar tana nan a roba na aje miki a kitchen, idan kin gama ki soya manja dama Waheeda ta daka yaji tun jiya. Dan Allah karki tsaya sanyin jiki har su dawo baki gama ba. Tauheedah abincin kawai zaki yi Waheeda tayi shara Zaheeda kuma tayi wanke-wanke." Daga haka mahaifiyartata ta fice daga ɗakin, ita ba takaicin zuwa gidan kawu bane ya dame ta tasan Nura idan shi ɗan halak ne yabarta har abada kenan. Ita yanzu takaicinta sanwar da aka sakata ɗorawa dan ita can bason shiga kitchen takeba, ta tsani koda ɗora ruwan zafi ne. Ga babban abun takaici tsintar shinkafa ta tsani tsintar shinkafa, gashi kullum mahaifiyarsu cikin auno musu shinkafar Hausa takeyi sai kace wasu mayu kanaci kana tauna tsakuwa. Gabaki ɗaya ranta a ɓace yake, idan tayi nasarar shiga cikin rayuwar Alkasim Galadima tasan sunyi bankwana da talauci har abada. Dan da gaske tagaji da kalar wannan rayuwar da ake yi a gidan su....

#Tauheeda
#Nura
#Love/Betrayed..
#lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/16, 3:11 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*

*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu

5...

Yaa Meri ta kalli Nura da yayi wata irin zabgewa cikin dare ɗaya, idanunsa sunyi wani irin zuru-zuru, tun a jiyan babu yadda Inna bata yi dashi ba akan suje asibiti yace yaji sauqi. Yaya Auwal ya kira yazo masa da maganin zazzaɓi, haka suka kwana yau da safe ma dakyar ya kurɓi kokon da Inna ta dama masa ta kawo masa har ɗaki. Ganin halin da yaron nata yake ciki ya qara ɗaga hankalin Innar, dakyar yasha kunun kaɗan ya aje yace ya qoshi. Ita dai Inna sai binsa take da kallo, haka tace Auwal ya lallaɓa shi koshi zai yadda ya kaisa asibiti da kansa.
"Inna wai shi yaro ne? wane irin lallabawa ne ba'a yi masa ba tun jiya? Kibarsa idan yaji ajikinsa zai faɗa ne. Hmmm ni fa na san ciwon nan nasa duk akan wannan yarinyyar ne, daman da wuya ki gansa a kwance sai tasu ta haɗo su. Ni kam na rasa jaraba irin wannan yarinya ƙarama ta zauna tayi ta juyasa kamar wani waina.!" Auwal ya faɗa sounding so very pissed up. Ko form ɗin da ya bashi ya kai mata dakyar ya yadda ya basa. Nan nuran ya fice daga gidan ya tafi harkokinsa, sai ga Yaa Meri itama tazo dan Inna ce ta kirata a waya. Inna tayi ficewarta cikin gida tana hada-hadar ɗora girkin rana kafin autarta ta dawo, daman kuma Yaah Merin kamar jera take ta Inna ta fita, ta kalli Nura ta saukar da murya tana faɗin.
"Wai meke damun ka ne?" Tambayar yaji tayi masa wani irin girma, ta ina zai fara yace Tauheeda ta fasa aurensa. Idan sukaji ai dariya zasu yi masa dan daman ba wani sonta suke yi ba, dukkan su cewa suke yi yarinyyar bata kwanta masu ba ta fiye rawar kai, musamman yadda Nuran ke rawar jiki da ita ya ɗauki wata irin soyayya ya ɗora mata.
"Allah ya kyauta toh, idan tayi wari maji." Yaa Meri ta faɗa tana kallon yanayin kanin nata, kafin ta ɗora da faɗin.
"Wai bama yau ne za'a kai kuɗin gaisuwa gidansu ƴar gwal ɗinka ba ne? Dan Nima Inna ke faɗa mun a waya." Nura jin tambayar yayi kamar an ɗauki mashi an soka masa a ƙahon zuciya. Bai ce komai ba saboda shi komai ya sake jagule masa. Bayan fitar Yaa Meri daga ɗakin nasa ya koma ya kwanta kan katifarsa yana jin wasu irin warm tears na sauka a fuskarsa. A hankali kuma yake jan shessheka kamar wani little boy yana faɗin.
"Meyasa zaki yi mun haka Tauheedah?" Ya faɗa da wata irin raunanniyar murya. Jin zuciyarsa yake tamkar ana gasata da wuta. A hankali ya ɗauki wayarsa yayi dialling lambar Tauheedan. Wannan karon layin busy aka riqa danna masa da alamar tayi blocking ɗinsa.

******
"Ai nama ta kiranka a waya a kashe." Kawu Mamman  ya kalli mahaifiyarsu Tauheeda ya wani tsuke fuska yana faɗin.
"Banda waya yanzu!!" Ya faɗa cikin haɗe rai dan Allah Allah yake ta tashi ta tafi karta kawo masa wata lalurar da zai yi mata bauta yana zaman-zamansa dan yasan zuwan Hadiza wajan shi ba alkhairi bane ba kwata-kwata dan Ita dai kullum a ɗauka a bata ta kula da marayunta ta ke ba wai dan ta bayar ba. Kawu Mamman na shirin miqewa yana faman gyara babbar rigarsa ganin taƙi cewa komai. Hadiza tayi saurin tsayar dashi tana faɗin.
"Baban su Huzaifa daman mai neman Tauheeda ne yake son ya turo da magabatansa." Jin haka yasa Kawu  ya nemi wuri ya sake zama dan in dai irin wannan maganar ce yasan zai samu na kashewa dan yasan harda sadaki za'a haɗo. Da sauri yace da ita.
"Ɗan gidan wanene yaron?" Nan Mama Hadiza ta shiga yi masa bayanin shima ba kowa bane maraya ne kamar su Tauheeda karatu ma yake yi har yanzu. Wani irin canja fuska Kawun yayi kafin ya hau sababin faɗa yana cewa.
"Wannan wane irin neman aure ne? Da alamar Hadiza baki da hankali. Ke yanzu duk kyawun Tauheeda ace talaka zata aura kamar su? kenan su a talauci zasu kare?" Kallonsa Mama Hadiza take daman kuma batayi mamakin maganarsa ba, dan kusan kakaf halayensa na rashin mutunci dana kwadayin abun duniya shi Tauheedar ta ɗakko sak kasancewarsa Kawu Mamman kani yake wajan mahaifinsu
Tauheedan. Baffan su Tauheedan ya daɗe bai yi aure ba dan Mamman  ya rigasa aure sai daga baya Baffan yayi auren, sannan ya tsallaka neman kuɗi daga secondary school dukan su suka tsaya da karatunsu na boko ba wani ilimi mai zurfi suka yi ba a karatun. Su biyu kawai mahaifiyarsu ta haifa, daga Baffa sai Kawu Mamman sai kuma tarin ƴan uba da suke zagaye dasu. Asalinsu fulanin Adamawa ne sai dai mahaifinsu mazaunin Kano ne, a Kanon suke rayuwa dukansu. Ita kuwa Hadiza ƴar asalin jihar Kano ce, itama Babanta ba wani mai kuɗi bane ba, babban malami ne wanda ya buɗe makarantar almajirai a wani ɓangare dake cikin gidan sa. Sannan itama Hadiza ita kaɗai take a wajan mahaifiyarta tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu sai riqonta ya koma hannunta kishiyar uwar ta har ta aurar da ita. Miqewa Mama Hadiza tayi tana faɗin.
"Sai sunzo." Tana gyara wuyan hijjab ɗin ta dan ba zata biyewa Kawu ba, tasan halinsa ba kirki ya cika ba. Ita dai fatanta Allah ya taimake ta kar ya nuna zalamarsa a gaban maneman auren yarinyar ta. Ko cikin gidansa bata shiga ba, dan tana shigowa sukaci karo dashi daman kuma ba shiri takeyi da matansa ba, saboda tun can farko ba sonta sukeyi ba.

*****
"Wai Mama waya dafa wannan shinkafar duk ta cabe kanaci kana tauna tsakuwa?" Waheeda ta faɗa da wani yanayi a muryar ta, duk yunwar da ta kwaso a makaranta ace wannan shinkafar zataci wacce ta kusa zama tuwo?
"Kema kin sani wa zai yi wannan aikin idan ba Tauheedah ba? Kawai kiyi hakuri kici hakanan
Allah yasa batada yawa da ta saka anyi hasara. Kiyi hakuri da daddare sai ki karɓo kuli-kuli kiyi mana gurasa akwai sauran fulawa ai." Murmushi Zaheedah tayi cike da jin daɗi za'a yi musu wani abun dan itama dai dakyar take tura wannan abincin da Tauheedah ta dafa. Tauheedah dake kwance a ɗaki tana ta faman chart a wayarta tana jin hirarsu. Kwabe baki tayi aranta take faɗin kwana nawa ya rage tabar masu gidan? tasan a gidan Alkasim Galadima babu ita babu shiga kitchen Oda  kawai zai riqa yi musu daga haɗaɗɗun restaurants na ƴan gayu tana kwance tana hutawa tana shan Ac. babu ita babu yanka albasa, babu daka, ba tankaɗe babu gyaran kayan miya, ballantana idonta suyi ciwo saboda yajin su. Ji tayi murmhshi yana kwace mata. Da sauri ta lalubo numbersa tana shafawa da hannayenta. A hankali take faɗin.
"Ina jira dan Allah!!!" Wani irin yanayi take jin kanta acikinsa tasama ranta burin zai kirata, duk yadda zuciyarta take ingizata akan takirasa taki yadda da hakan saboda tana da wani irin aji. Sai dai zuciyarta da duka gangar jikinta ta ke jin wata irin kewarsa, ji ta ke kamar ta daɗe da saninsa. Ji take a zuciyarta kamar ba a ƴan mintuna ne tayi da saninsa.

Kaduna state.
Chapter 6 · 0% Book details