← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 16

Sashe 12

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwalliya ta xauna ta tsarawa fuskarta tamkar mai shirin xuwa gasar sarauniyyar kyau ta duniya. Daman tun can dama ita Tauheedah mai yawan son adoce da kwaliyya, duk kuɗin da take samu wurin samari saita haɗa su ta shiga wurin koyon kwaliyyar zamani, haka ta qara tara wasu kuɗin ta siya kayan kwaliyya ƴan unguwarsu har wurinta suke zuwa tayi musu suna bata 1500 ko 2k babu laifi kuma ta kware sosai a kwaliyyar. Akwai wani lokacin da kawarta Fauxy ke faɗa mata me zai hana ta riqa yiwa mutane bama ƴan unguwa ba sai su sameta har gida tayi musu tunda ta iya sosai ba ƙaramin morar kuɗin zatayi ba. A wancan qaron da Fauzy tayi mata maganar baki buɗe  ta saki  tana kallonta. "A wane gida zan tara yaran ƴan gayu nayi musu makeup Fauzy? A cikin wannan gidan namu kike so na tara su? Hmmm Fauzy kice dai kawai dan idan suka xo bazasu qara marmarin dawowa ba, ni wallahi sai kisa ma su rainani. Ke dai ki taya ni da addu'a In sha Allahu ƙawata babban shagon makeup mijin da xan aura zai buɗe mun. Ke bama makeup kaɗai ba harda su gyaran jiki da saloon." A lokacin haka ta faɗa, kuma har yanzu tana da wannan burin cikin zuciyarta. Bata shiga wanka ba sai da tabbatar ta share ko'ina na gidansu ta saka turaren tsinke, aranta tana ta tsaki ganin yadda duka simintin gidansu ya farfashe, idan Allah yaso sunyi aure da Alkasim ai unguwar duka zasu bari ta siyawa Maman su wani gidan. Duk yadda ta share ɗakin Maman su ta kauda duk wani tarkace gefe sai taga bai yi mata ba, gani take idan Alkasim ya shigo cikin gidansu komai karewa kallo zai yi. Ita dai Mama banda kallon Tauheedah babu abunda ta keyi, addu'a kawai take mata Allah yasa Alkasim ɗin alkhairi ne a tare da Tauheedah dan tasan Tauheedah bata taɓa tsayawa tama roki Allah miji nagari ba, ita dai kawai mai kuɗi. Tana cikin fesa turare ta ji muryar Waheeda na kwala mata kira, da sauri ta aje turaren ta fito daga ɗakin har kusan cin karo sukayi da juna. Waheeda sai kallonta take ganin irin kyan da Yayar ta ta tayi.
"Wani na sallama dake a waje." Waheeda ta faɗa tana ganin yadda fara'ar Tauheedah ɗin ta karu sosai wanda ta qaramata kyau da kwaliyyar da tayi.
"Yawwa Wahee zan fita yanzu na shigo dashi zai gaisa da Mama, kafin nan zanyi masa shimfiɗa a (soro) kulolin can a gefe na haɗa komai da komai ɗauka kawai zaki yi ki kai masa. Amma kafin nan ki fara shiga kiyi wanka ki canja kaya masu haske ki shafa turarena."
"Ikon Allah Yaya Tauheeda ina kika samu wa'annan kulolin na ƴan gayu da tsada??"
"Kinga nidai bana son tambaya kiyi sauri zan fita na shigo dashi." Da sauri ta fita ta leqa ɗakin Mama ta faɗa mata cewa bakon ya iso. Ita dai Mama binta kurum take da kallo tun daga suturar dake jikin ƴarta ta har kwaliyyar da ta tsarawa fuskarta. Xuciyar Mama sai da tayi wani irin bugawa ganin irin kyan da Tauheedar tayi, tasan wannan kayan dake jikinta banata bane arosu tayi. Ganin Maman ba tace komai ba Tauheedah ta juya da saurinta tabar cikin ɗakin. Dakatawa tayi acikin zauren gidansu tana jin yadda zuciyarta ta canja sautin bugawar da take. Tafi minti biyu tsaye a wuri ɗaya kafin ta ɗaga ƙafa ta fita a ƙofar gida. Jingine ta samesa jikin mota ya harde hannayensa a kan kirjinsa yana bin unguwar da kallo da mutanen dake kai kawo a cikin ta. Tsayawa tayi tana kallonsa yayi mata kyau sosai. Shima ɗin kallonta yake ,xuciyarsa dokawa take da soyayyarta. Cikin bin umurnin  zuciya da gangar jiki ya nufeta baifi taku biyu ba a tsakaninsu ya tsaya yana kallonta da idanunsa masu sheqi. Kallon da yake mata ba ƙaramin narkar mata da zuciya yake yi ba. Duk tabi ta ruɗe. Langabar da kanta tayi da wani sanyayyen murmushinta take ce masa sannu da zuwa. Girarsa ɗaya ya ɗage yana faɗin.
"Da gaske kece? kinyi kyau." Wani daɗi ya qara cika mata zuciya tasan tana da kyau daman.
"Mu shiga ciki akwai rana anan." Ta faɗa cikin sanyin muryarta mai fisgarsa. Haka suka jera suka shiga cikin gidan nasu banda bugawa babu abunda zuciyarta keyi. Tunani ta ke idan kuma yaga gidansu ya kasa karbarta matsayin abokiyar rayuwa fa? Ɗan dukawa yayi ganin yafi ƙofar tsayi nesa bakusa ba, sai bin ɗan karamin tsakar gidan nasu yake da kallo yana mamaki yana qarawa daman akwai masu rayuwa a irin wannan wurin?
"Mu shiga ka gaisa da Mama." Ta faɗa muryarta na ɗan rawa ganin yadda yake bin ɗan ƙaramin tsakar gidan nasu da kallo. Bakinsa ɗauke da sallama yayi sallama ƙofar ɗakin Mama. Daga ciki aka amsa masa sallamar Mama Hadiza ta ɗaga kai ta kalle sa. Cikakken matashi mai cike kamala da natsuwa. Har kasa ya saka gwiwoyinsa ya saukar da kansa yana gaishe da Maman. Cike da kunya Mama ta amsa cike da kulawa tana masa bangajiya da kuma yadda ya baro gida. Lokaci ɗaya ya amsa da cewa
"Alhmdulillahi!!" Shiru ya ratsa a tsakaninsu har na tsawon minti biyu, duka Alkasim ɗin ya rude ya rasa ta ina zai fara, dan Maman su Tauheedah tayi masa wani irin kwarjini. Dama yasan ba su da mahaifi sai dai mahaifiya Tauheedah ta faɗa masa wannan. Sai dai ya dace ya yiwa Mama bayani yazo ne kai tsaye da niyyar auren Tauheedah ba wai wasa yazo ya yi musu ba. Samu yayi ya tattaro natsuwarsa ya shiga yiwa Mama bayanin kansa, asalinsa da komai, qarshe ya faɗa mata ya shigo cikin rayuwar Tauheedah gabaki ɗaya dan su zama abu ɗaya ya zaɓe ta ne a matsayin abokiyar rayuwa. Mama tayi farin ciki da bayanin da Alkasim ɗin yayi mata haka ta yaba da natsuwarsa da duka kalamansa.
"Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta faɗa masa kafin ta ɗora da faɗin.
"Tunda har da gaske kake, ina addu'a a cikin lamarin, kuma tauheedah nada kanin mahaifi yana nan a raye idan ka shirya sai kaje can ka same sa kuyi magana." Alkasim ya ɗaga kai alamar gamsuwa da bayanin Maman yana ɗorawa da faɗin. In sha Allahu xuwan da xai yi na biyu tareda magabatansa zai zo ayi maganar aure.

Waheeda tayi duk yadda Tauheedah ta tsara mata, sai bin Alkasim take da kallo ta gefen ido tana mamakin inda kuma Tauheedah ta jajibo irin wannan saurayin na liqawa a goshi domin irin su ne ake kira mazan Novel. Wato dai komai sun haɗa. Duk yadda Tauheedah taso yaci abinci kasaci yayi sai faman kallonta kurum yake tamkar ya sace ta su gudu dan so.
"Nifa a koshe nake me yasa zaki wahalar da kanki wurin yi mun girki?"
"Haba tun daga Kaduna kazo shine zakace me yasa na wahalar da kaina? Nidai kaci dan Allah ko kaɗan ne." Ta faɗa cikin shagwaɓa. Murmushi yayi yana faɗin ta zuba masa amman kaɗan. Kamar yadda yace kaɗan ɗin ta zuba masa ta ɗora masa naman kaza a sama. Ko yadda yake cin abincin cikin burgewa irin na ƴan gayu kasa ɗauke idonta tayi akansa wearing a big smile kwance akan fuskarta. Yana ɗagowa suka haɗa ido, tayi saurin ɗauke idonta. Ba ƙaramin kunya taji ba. Murmushi yayi yana ɗage mata girarsa ɗaya.
"Abincin nan yayi min daɗi waya girka? kin san ina son abinci sosai, kuma da alama Allah ya dubeni da rahamarsa ya bani maccen data iya girki." Kalamansa na karshe ba ƙaramin buga mata zuciya sukayi ba, ita a ɓangaren girki ai tasan batada wannan jarumta, ita shiga kitchen ma mugun wahala yake bata, ko dafuwar dafaduka Mama ta sakata sai ta cabe. Farar shinkafa kawai ce zata dafa tayi daidai sai wake da shinkafa, ita rashin iya girkinta bai wani dameta ba. Ta riga ta ɗorawa kanta burin auren mai kuɗin da tasan order kawai zasu saka kullum bazata shiga kitchen ba rayuwar hutu da jin daɗi kawai. Ko yanzu bata ɗauki kalaman Alkasim ɗin da muhimmanci ba. Murmushi kurum tayi masa dan babu amsa da zata iya bashi. Sai da ya canye wanda ta zuba masa, haka ta ɗora masa samosa da meatpie akai shima yaci babu laifi yanata yaba girkin. Alkasim ya daɗe sosai a wurin Tauheedah sunata tsara yadda rayuwarsu zata kasance. Sai wuraren qarfe 4 yace mata zai tafi. Komawa cikin gidan yayi ya yiwa Mama sallama gami da ajewa Maman 100k a gaban ta. Mama ta riqa faɗa tana faɗin ya ɗauki kudinsa sunyi yawa. Amma fir Alkasim yaki saurarenta Haka ma ya baiwa Waheeda da Autar Mama 50k. Har cikin mota Tauheeda ta rakasa tana jin kanta ya mata gingiringim ganin yadda yan unguwa ke kallon Alkasim. Wata babbar leda ya dauko a back seat ya miqa mata yana ɗorawa da faɗin.
"Inji mami." Amsa Tauheedah tayi cike da murna watau har mahaifiyar Alkasim ta santa. Godiya ta riqa yiwa Alkasim tamkar zata duka masa. A bakin motar ma sun daɗe tamkar kar ya tafi yake ji. Shi kansa yana mamakin kalar son da yake yiwa Tauheedah Baffa. Dakyar ya iya tafiya ya faɗa mata wani satin zai shigo. Daga nan suka yi sallama ta shiga ciki shi kuma yaja motar sa ya bar unguwar.
Chapter 12 · 0% Book details