Sashe 4
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
#Tauheedah
#Love at first sight
#lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/15, 4:44 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
3....
"Kin san shi ne?" Tauheeda ta faɗa tana kallon Fauxy duk da bata hango fuskarshi ba. "Yana ɗaya daga cikin friend's ɗin ango." Fauxy ta faɗa tana buɗewa Tauheeda ƙofar gaban motar. Tauheeda na saka kanta cikin motar wani irin dokawa zuciyarta ta shiga yi da qarfi har Fauzy ta rufe ƙofar motar tana faɗin sai sunyi waya. Ɗaga kai kurum Tauheeda ta iya yi tamkar wacce aka kullewa baki, ga wani irin yanayi da ta tsinci kanta a cikinsa wanda ta kasa tantance yanayin menene. Sanyi Ac da kamshin turaren jikinsa ya haɗe da wani irin kamshin da ya saka ta lumshe idonta. Kamshin ƴan gayu. Ta faɗa can ƙasan makoshinta, tana son kuma ta tuno inda ta taɓa jin wannan kamshin ta kasa. Sanyayyar muryarshi ce ta katseta yana tambayarta unguwar da take. Lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kallesa suka haɗa ido cike da mamaki. "Shine!" Ta faɗa can ƙasan makoshinta, hankalinsa yana kan tukin da yake ya qara maimaita mata tambayar a karo na biyu ba tare da ya kalleta ba. Cike da wani irin sanyi jiki da nauyin baki ta faɗa masa, har lokacin bata daina jin bugun zuciyarta ba har cikin kunnuwanta. Bawai ya san Kano sosai bane danna wayarsa ya shiga yi kafin ya makala mata wani abu dake jikin motar, sai taga sun ɗauki titin unguwarsu. Bata gama shan mamaki ba sai da suka shiga cikin unguwar ya ɗan kalleta yana faɗin. "Wane layi ne??"
Wani irin takaici taji ya mamayeta tamkar ta fashe da kuka. Yanzu duk wannan kyan nata acikin wannan unguwar take rayuwa? shi kansa haka zai yi tunanin. Kuma ai ita bazata so yaga ƙofar gidansu ba. Ji tayi makoshinta ya bushe tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle take faɗin. "Kawai ka ajeni a nan nagode." Ɗan kallonta yayi yana ɗauke kansa ba ya son yayi ta maimaita magana, mamakin kansa ma yaje yi da har ya ishesa da ya tsaya yana biye mata. "Inane layin gidanku?" Wannan karon ya faɗa da wani irin yanayi a muryarsa wanda ya nuna mata da gaske har ƙofar gidansu zai ajeta. Ɗan tura baki tayi kamar yadda yara suke yi, aranta take faɗin. "Wannan karfin hali har ina?" Bai san lokacin da murmhshi ya kwace masa ba, da hannu take nuna masa layin, yana jin yadda motar tayi wani irin ƙasa har duwatsu na gogarta. Ai kuwa har ƙofar gidan nasu ya kaita yana mamaki yana qarawa ganin wani irin gini da ta kira da nan ne gidan su. Ga unguwar da wani irin cinkoso. Tun kafin ta kai hannunta kan marfin ƙofar yayi saurin dora mata wayarsa kan cinyar ta. Kallonsa ta tsaya tana yi da alamar tambaya a yanayin ta. "Lambarki zaki saka mun." Ya faɗa kamar ana matse masa bakinsa, ko a mafarki idan yace zai roqi lambar macce zai ƙaryata mafarkin da yake yi. Amma gashi yau shine da karɓar lambar macce? daman tamkar jira take ta ɗauki wayar ta shafa wayar dan ta yi mata kyau sosai. Wata zuciyar tana faɗin. "Tayi sauri ta saka mishi karta yadda damar ta wuce mata. irin waɗannan mazan ba abun yaddawa bane,ta lura yana da wani irin aji da miskilanci
Kar ya canja shawara. Da sauri ta saka lambar ta miqa masa tana jin yadda bugun zuciyarta ke karuwa da sauri.
"Sunan da zan saka?"
"Tauheedah Baffa!" Gyada kai yayi alamar gamsuwa, yana ɗorawa da faɗin nasa sunan.
"Alkasim Galadima!" Sunan yayi mata daɗi irin sunan masu kuɗi. Sai da safe tayi masa tana ɗorawa da yi masa godiya. Akan idonta yaja motar yana ɓacewa daga unguwar. Wani numfashi take saukewa da alamar ta daɗe riƙe dashi. Tana ƙoƙarin shiga gidan su taga ansha gabanta. Ɗaga kai tayi tana kallon Nura da mamaki ganin yadda ransa yake a ɓace. Wani kallo ta shiga watsa masa tana jin wani irin takaici.
"Waye shi??"
"Saurayi na ne!!" Kalmar ta dakesa sosai.
"Meyasa zaki shiga motar sa? Ki faɗa min menene ba na yi maki.? kin san ina da kishi bazan iya jure ganinki tare da wani ƙato ba." Wannan karon baki ta saki ta ware hannayenta tana wani tafa su ta ke cewa. "Toh
haka ka koma? sannu Baba Nura. Kai waye da zaka hanani kula wani? sau nawa zanyi maka wannan kashedin? ka daina kure haƙuri na fa Nura karka qara ɓata mun rai, idan har kana so na daina kula kowa. Kazama kamar sa fiyeda mashi nakeso na ganka!" Taja wani irin tsaki akan idonsa ta shige gidansu gamida bugu ƙofar kamar ƙofar ce tayi mata laifi. A tsakar gida ta samu ƙannenta da Maman su, Waheeda na Assignment ɗin makaranta Autarsu Zaheeda kuma tana haska
mata da ƙaramar fitilar hannu. Ganin yadda ranta yake a ɓace yasa mahaifiyarta ta kalleta tana tambayar ita dawaye? Sannan dawa kuma tayi faɗa.??
"Kema kin sani da Nura mai shegen nacin nan ne, ni ban taɓa ganin natacce marar zuciya irinsa ba, sai na zauna shi kaɗai zan riqa kulawa ga shegen kishi? Ni wallahi tallahi nagaji Mama, nagaji da halinsa gobe ki kirasa ki faɗa masa kawai ya kyaleni Allah ya haɗa kowa da rabonsa." Da sauri Maman ta shiga girgiza kai tana faɗin. "Idan muka yiwa Nura haka ba mu yi masa adalci ba Tauheeda, haba, kiduba kiga yadda yake ɗawainiya damu, ji yadda yake kula da karatun kannenki taya za'a kore shi?." Daman ni nasan haka zakice ai idan kuma nasamu wanda yafi shifa??"
"Idan kika cuci Yaya Nura Allah bazai barki ba Yah Tauheedah!" Waheeda ta faɗa da rashin jin daɗi a muryar ta. Wata irin harara take aikawa ta saitin Waheeda ɗin kafin ta ɗora da faɗin. "Nabar miki shi." Da haka ta tashi tayi shigewarta ɗaki sunan Alkasim Galadima yana zauna mata cikin kanta. Wani irin nishaɗi ta tsinci kanta acikinsa har kusan karfe goma tana riqe da wayarta sunan shi da yanayinsa na samun wurin zama acikin zuciyarta. Haka ta kwanta riqe da waya da mafarkin Alkasim ɗin zai kirata.
"Daman hotel ɗin kadawo? Anata kiranka a waya ɗan iskanci ba zaka ɗauka ba?" Mb ya faɗa so pissed up a muryarsa. Da ido Alkasim ya bisa yana ƙara gyara kwanciyarsa gamida manna filo a kirjinsa yana cewa. Gobe zasu bar Kano daman dalili ya kawosa Kano ba garin zuwansa bane. Wani irin nauyi yaji kirjinsa yayi masa tun lokacin da ya ɗora idonsa akanta yake jin wannan nauyin a tare dashi. Fuskarta ta kasa ɓace masa, "Ga ɗan iska yana magana ko?" MB ya faɗa cike da takaicin sa. Khalil dake rage kayan jikinsa ya wani kwabe baki yana faɗin. "In dai Alkasim ne sai kayi ciwon kai." Da haka suka fice daga room ɗin yana jin mitar da MB ɗin keyi. Wayarsa na riqe a hannunsa har lokacin yana kurawa sunanta da yayi saving da ido tamkar mai son gano wani abu a cikin sunan.
"TAUHEEDAH..!!!" Ya faɗa a hankali yana jin zuciyarsa na wani irin dokawa da ambatar sunan nata, kusan sau biyar yana gwada kiranta yana fasawa, bai san ma me zai ce mata ba, kuma zuciyarsa na masa nacin ya kirata kawai. Haka ya kusan kai asuba da tunaninta manne aransa. Dakyar ya iya yin sallar Asuba wani irin ciwo kansa ya shiga yi. Qarfe goma suka wuce da amarya garin Bauchi haka ya baza ido yaga ta inda Tauheedan zata fito sai dai ko mai kama da ita bai gani ba, yaga dai Fauzy har sun gaisa kuma ya kasa tambayarta ina take? Haka suka kai amarya yana manne da ita a zuciyarsa, ganin yadda yanayin sa ya canja friend's ɗinsa suka fara tambayarsa lafia.? Mb yayi dariya yana amsawa da faɗin. "Kasan Mama's boy ne maybe yana kewar Ammi ne." Harara kurum Alkasim ya riqa aikawa ta gefen Mb Still yaki yace komai. Kwanansu ɗaya a a Bauchi ya koma Kaduna shi da Mb dama su kaɗai ne ƴan Kaduna Khaleel da ango duka ƴan Bauchi ne.
*******
"Ka rame!!" Wata farar mata ta faɗa wacce yayi matashi da kansa akan kafafunta tana shafa kansa a hankali. Lumshe ido kurum yayi, bacci yakeji sosai ga wata irin gajiya da yakeji tana mamaye jikinsa. Miqewa yayi daga kwance yana faɗin. "Zanje na watsa ruwa mami." Ɗaga kai tayi tana faɗin. "A kawo maka abincinka ko anan zakaci?" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Zan dawo anan zanci mami daga nan muyi hira na baki labarin biki." Murmhshin jin daɗi tayi tana kallonsa tana gyaɗa kai cike da wata irin soyayyar yaron nata. Da sassarfa ya nufi ɓangarensa ya rage kayan jikinsa ya shige toilet dan watsa ruwa.
Wani irin kunci takeji a kwana biyun nan me yasa yasan bazai kira ba ya karɓi lambar ta? me yasa zai saka mata ran zata iya ganin kiransa ako wane lokaci? Da yamma mahaifiyarta ta sameta da maganar data girgiza ta wai Nura ya kirata yana son ya turo magabatansa a kawo kuɗin auren su. Maganar nan ba ƙaramin dukanta tayi ba, a ganinta babu natacce irin Nura zako tayi maganin sa. Saqo ta tura masa akan tana son ganinsa bayan sallar magriba kara ta fito masa a yaren da zaifi ganewa. Kai wannan masifa ita har ta fara mafarkin zata zama matar Alkasim Galadima a nan kusa tana da tabbacin zai kirata a kowane lokaci, shine wannan zai wani ce zai turo. Kawai zata ci gaba da jiran kiran. Ba ƙaramin daɗi Nura yaji ba ganin saqon Tauheeda, daman sun saba irin wannan faɗan bazata daɗe ba zata sauko daman yasan Tauheeda bazata taɓa barinsa ba. Ana gama sallar magriba sai kuwa ga yaro yana kwaɗa sallama. Waheeda ce ta amsa masa ya faɗa mata ana sallama da Tauheeda, tun kafin Waheeda ta buɗe baki ta baiwa yaron amsa Tauheeda ta fito daga ɗakinsu riqe da hijab a hannunta, ta leqa ɗakin Mama tana faɗin ana sallama da ita a waje. Ɗaga kai Maman tayi dan lokacin tana zaune akan sallaya tana azkar.
#Tauheeda
#Nura
#Love /Betrayed
#lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/16, 3:10 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*