Sashe 2
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Karfe huɗu da rabi ta fito daga ɗakinsu babu kowa a tsakar gida kannenta sun tafi islamiya, itama daga yin candy ta jingine islamiyyar gefe sai yawo gidan ƙawaye da zuwa taron biki, dan kusan duka ƙawayen Tauheeda ɗin masu kuɗi ne babu laifi ita kaɗaice tallaka a cikinsu. A wanni fannin kuma ko bakayi niyar abokantaka da Tauheedar ba sai kayi tana da saurin shiga rai kuma tana da wani irin kyau wanda ba maza ne kawai yake fisga ba harda mata ƴan uwanta. Haka kuma babu wacce ta haɗu da ita a makaranta sai a gidan kitso, lalle da kuma saloon. Kuma duka samarinta sun tsaya mata itama, lokacin da ta fara kula samari ta kuma daina kitso acikin unguwarsu da yawan zuwa lalle da gyaran kai da take yawan yi a gurare masu tsada yasa ta haɗu da ƴaƴan masu kuɗi. Buɗe kular abincinsu tayi wacce aka ajiye a kitchen saboda duk wanda ya tashi ya ɗiba yadda yake so. Tun kafin ta buɗe kular ta fara addu'a Allah yasa ba fara da mai bace dan ta tsani fara da mai saboda kusan kullum ita ake dafawa a gidan su. Kuma ita gani take sunfi kowa talauci idan ana yi. Wani irin dokawa zuciyarta tayi cin karo da abincin kular, yamutse fuska ta soma yi tana jin ranta yana zafi. Da sauri ta rufe tana jin ai gara fara da mai da wannan danwaken da ta hango, kuma danwaken ma na dawa.
"Allah ya tsinewa talauci." Ta faɗa Kusan rai a ɓace ta fito daga cikin kitchen ɗin, komawarta tayi ɗaki, kayan jikinta ta rage ta jawo wata ƴar ƙaramar jaka dake sargafe a bangon ɗakin an buga kusa ajikin bango. Zuge zip ɗin jakar ta yi sabulun wanka ta fitar (Dudu osun) da kuma soson wankanta dan ita kusan komai nata daban ne a gidan bata cika sharing abubuwa da kannenta da mahaifiyar su keyi ba, dan ko basu da sabulu Waheeda idan ta ɗauka tayi wanka kwana zatayi tana mita data daukar mata abu ƙara ta bata ta siyo wani daban. Mintuna talatin suka ɗauketa tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar material kalar pulple wanda kalar tayi mata kyau ɗinkin kuma ya zauna sosai a jikinta. Ta saka turarrukkan da take amfani dasu a jikinta masu daɗin ƙamshin. Shigar da tayi yayi matuqar yi mata wani irin sanyayyan kyau tamkar ɗiyar wani kusan gomnati. Ta ɗauki talkami da jaka wanda zasu ƙara fito da shigarta ta saka. Wayartace tayi ƙara ganin mai kiran yasa tayi murmushi tana cewa. "Hello Fauzy kun isa wurin ne? Okay nima ganinan fitowa. Owk tom idan nazo zan kiraki." Ta faɗa tana sauke wayar zuciyarta shar. Wata ƙawarta ce ake bikin cousin ɗinta, suma suna da kuɗi sosai shi yasa aka gayyaci Tauheeda ɗin dan Fuzyn ta santa da kaunar zuwa biki a rayuwarta. Tasan kuma idan bata faɗawa Tauheedan ba zata sha qorafi da mita wanda za'a shekara bata daina ba.
Daga labulen Maman su tayi tana zaune a tsakar ɗaki tana lissafin kuɗi wanda ƴan goma-goma sunfi yawa a cikinsu, kasancewar mahaifiyar tasu tana ƴan sana'o'inta haka tana sai da koko da safe sosai take ciniki. Dariya Tauheeda tayi tana tsaye daga bakin kofa take faɗin. "Mama irin wannan dakune kuɗi haka kina ta wani dakuna su kamar wacce take riƙe da dubu ashirin a hannunta? ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kuɗin nan bazasu wuce dubu biyu ba." Harara Maman ta bita dashi. Dariya Tauheeda ta sake yi tana faɗin. "Yi hakuri Mamana in sha Allahu wahalarki ta kusa zuwa karshe dan mai kuɗi zan aura, dan ni gaskiya bazanyi auren talauci ba kamar yadda kikayi." Girgiza kai kurum Maman tayi ta rasa me zata cewa Tauheedan, dan tamkar wata Kaka haka Tauheedan ta mayar da ita.
Kuma duk cikin yaranta itace mafi soyuwa a wurin ta. "Mama zan fita zanje bikin ƴar uwarsu Fauzy kiyi min addu'a Allah ya haɗani da rabona." Bakici abinci ba zaki fita?" Mamar ta faɗa tana kallon yadda Tauheeda ta wani kwaɓe fuska cikin shagwaɓa ta ke faɗin. "Ɗanwake ne fa Mama kuma ɗanwaken ma na dawa, bazan iyaci ba gaskiya, idan na fita zan samu wani abun naci." "Allah ya kiyaye." Maman ta faɗa mata hakan. Langabe kai Tauheeda tayi tana faɗin. "Baki yi mun addu'ar na samo babban goro ba fa." Girgiza kai Maman tayi tana faɗin. "Allah ya haɗaki da nagari." Sakin labulen Tauheeda tayi tana barin ƙofar ɗakin ba tare da ta amsawa mahaifiyarta ba, tana jin takaicin me yasa Mamanta ba zatayi mata addu'ar samun mai kuɗin ba. Sai dai wai nagari kawai. Ficewa tayi daga gidan tana ƙoƙarin nemo lambar Nura saurayinta shima yana mata hidima sosai ɗan boko ne kuma yanada rufin asiri a( BUK) yake haɗa digree ɗinsa har mashin yake dashi (Roba-Roba) Tun ana sauran sati ɗaya bikin take damunsa za'ayi bikin ƙawarta tasan yana da abokai masu mota. Ta faɗa masa ya aro ya kaita ko bai daukota ba. Ya amsa mata da toh dan Nura irin samarin nan ne da basa taɓa hangen abun wani ballantana su ara, hakan yasan Tauheeda da hangen na wani da kuma wani irin rikicin da shi kasansa tsoron rikicinta yakeji yasan indai ya buɗe baki yace mata
Bazai iya ba tana ma iya rashin kara kulasa har abada. Shi kuma yana yi mata wani irin son da baya yiwa kansa. Sau biyu ya buɗe baki da nufin ya tambayi abokinsa aron mota sai yaji harshensa yayi masa nauyi ya kasa faɗa Tauheeda ta sakasa abunda yasan bazai taɓa iyawa ba. Shi yana mamakin mugun qarfin halinta bata da gashin wance tace lallai dole sai tayi irin kitson, tun cikin satin bikin yake fargaba karta tambayesa ya aro motar, lokacin da yaga kiranta kuma kurawa wayar ido yayi ya kasa ɗauka, dan baisan mai zai ce mata ba. Yana gani har kiran ya katse wani ya qara shigowa shima bai yi yunkurin ɗauka ba. Wayar take kallo tana mamaki tana qarawa meya hana Nura ɗaukar wayarta? Tasan yau bashi da lecture dan kusan ta haddace ranakkun shiga makarantar sa. Samun kanta tayi da tura masa guntun saqo.
"Nura ina ka shigane dan Allah?
Ka ɗaga wayar muyi magana, Allah yasa dai ka samu motar?."
Samun kanta tayi da addu'ar Allah yasa ya samu dan duk cikin samarinta kaf Nuran yafi su ɗan maiko-maiƙo, suma kawai karyace irin tata suke yi mata suna kashe mata kuɗin. Wannan karon Nuran ya kira numfashi taja tana fitarwa, babu bata lokaci ta ɗaga tana cewa.
"Ina ka shiga haka?" Bana kusa da wayar."
"Owk ka samu motar kuwa.?"
"Tauheeda ko dai nazo da mashin na kaiki Baash ɗin da zan karɓi motar sa baya gari." Wani mummunan ɓacin rai taji yana cika zuciyarta cike da masifa da karfin halinta take faɗin.
"Meyasa sai yau zaka faɗamun kasa na saka rai? Tsayama me naji kana cewa? Kazo da mashin? kana ganin nayi maka kalar wacce take hawan mashin ne? karka fara gwada hak'uri na da yamman nan Nura sai anjima." Ta faɗa tana jan wani irin tsakin da ya shiga ta cikin kunnen Nura ta kashe kiran zuciyarta na wani irin tafasa.... Wato ma ta hau mashin.?lallai ma Nura samun wuri. Kalmar nan ba ƙaramin takaici tabata ba.
#Tauheeda
#Nura
#Lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/15, 4:33 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
2..