Sashe 7
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mami ta kalli plate ɗin yaron nata ganin kawai abincin da yaci kuma yana ƙoƙarin mekewa tsaye tayi saurin dakatar dashi da idanun nata yake karantar fuskarta kamar tana son magana dashi. Babu shiri ya koma ya zauna ya wani shagwaɓe fuska kamar yaro ɗan shekara biyu, yasan zancen da zata yi masa tun daga ranar da ya dawo daga Bauchi ta fahimci yana ɗauke da damuwa amma zurfin cikinsa ya hana ya faɗa mata. Dama tun farko da take tambayar sa, ce mata yayi babu komai aiki ne kawai yayi masa yawa a office ta san duk wani motsi na Alkasim ya canja tun daga ranar da ya dawo Bauchi yake ɗauke da damuwa, ya dai kasa fitowa ya faɗa mata ne. Duk soyayyar Alkasim da son abincin ta lura a kwanan nan baya wani cin abinci ya qoshi sai dai ya tsakura yace ya qoshi.
"Sau nawa zan tambayeka matsalar ka? Meke damunka.??" Ta faɗa on a serious tone.
"Mami mana.!!!" Ya faɗa yana riqo hannunta duka biyu yana murzawa cikin nashi hannun
"Kar kayi mun karya nasani akwai abunda kake ɓoyewa. Ko sai na tara maka ƴan uwanka duka zaka dawo hankalina?" Da sauri ya girgiza kai, me yasa zata tara ƴan uwansa akan wannan maganar? yasan ma idan ya yadda sukaji wannan sirrin dariya zasu yi masa, akan wata macce ta sace zuciyar Alkasim Galadima. Da yake duka ƴan uwansa mata ne, Yayunsa biyu mata ma duka suna gidan mazajen su sai ƙanwar sa dake Egypt tana karatu. Idan sukaji ai ya bani da tsokana dole ya dakatar da mami akan wannan tunanin nata.
"Mami bafa wani abu bane ba."
"Owk naji menene faɗa ina jinka." Zuciyarsa rawa take, shi kunya ma yakeji ya faɗawa mahaifiyarsa he's in love.!!! Ganin yadda take kallonsa alamar shi ta ke saurare yaji zuciyarsa ta buga, ya buɗe baki zai yi magana wayarsa ta fara ringing numfashi yaja yana saukewa dan kuwa ko wanene ya cecesa. PA ɗinsa ya gani yana kiran, miqewa yayi tsaye yana faɗin.
"Mami zamu yi magana zuwa dare i promise Muktar yana jirana a office." Ya faɗa yana sumbatar hannunta. Murmhshi tayi tana masa fatan sauka lafiya. Bayan ficewarsa da ƴan mintuna ta saka mai aikinta ta dauko mata wayoyinta dake ɗakin ta a up stairs ita dai har yanzu zuciyarta taki yadda babu abunda ke damunsa gara ta tattaro ƴan uwansa su tsare matashi har sai ya buɗe baki ya faɗi damuwar sa. Babu jimawa mai aikin ta sakko da waya har biyu a hannunta ta miqa mata. Aje ɗayar tayi ta rike ɗayar tana lalubar lambar babbar ƴarta. Tana fara ring aka dauka.
"Kinyi kewata ne mami nazo?" Hajja ta faɗa cike da barkwanci. Yadda suka mayar da mamin tamkar wata kakar su.
"Kuzo gida narasa meke damun Alkasim."Mami ta faɗa a hankali kana jin wani irin rauni tattare da muryar ta. Jikin Hajja yayi sanyi ta ɗora da faɗin.
"Toh shi meke damunsa mami?"
"Ina na sani tunda bai faɗa mun ba, ko abincinfa bayaci sosai ina kula dashi." Murmushi Hajja tayi tana jinjina irin kaunar da mahaifiyar tasu ke yiwa Alkasim, a duk cikinsu tafi nunawa Alkasim soyayya ko Najma dake auta Ammi bata yi mata wannan kalar son.
"Zuwa anjima zan shigo, daman kuma baban Ahmad baya ƙasar zan kira Zahra a waya sai mu haɗu a gidan." Sauke ajiyar zuciya mami tayi kafin ta tambayeta jikokinta ta faɗa mata kowa yana lafiya. Daga haka sukayi sallama...
#Tauheeda
#Nura
#Alkaseem Galadima
#Lovestory2025
#Love/Betrayed
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/20, 8:56 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
6..
Kusan qarfe biyar na yamma yayi horn a bakin gate ɗin gidan su. Da sauri maigadi yazo yaja gate ɗin ya buɗe shi. Kai tsaye ya danno hancin motarsa yana kallon yadda Baba maigadin yake ɗago masa hannu alamar gaisuwa. Shima ɗaga masa hannun yayi ko magana baya son yi kansa ciwo yake masa. Da kyar ya samu ya kashe motar. zamansa yayi acikin motar yana jinginar da bayansa jikin seat ɗin motar. Runtse ido yayi yana sauke wani irin numfashi mai ɗumi, ko'ina ya motsa tunaninta ne manne a zuciyarsa, duk inda zai ɗora idonsa ita yake gani baisan meke faruwa da rayuwarsa ba. Tambayar da yake yiwa kansa kusan sati guda kenan. "Meyasa ya kasa mantata? meyasa zata manne da zuciyarsa da bugun numfashiaa a kowane motsinsa da zai yi sai ta faɗo masa arai?" Da kyar ya fito daga motar, tun daga kan laptop da briefcase ɗinsa da tarkacensa na office bai ɗauka ba haka ya barsu a motar gami da rufe ta. A haka ya taka zuwa entrance ɗin shiga gidan kansa tsaye. Tsaye yayi a bakin ƙofar yana danna door bell, ba ayi sakan goma ba ƙofar ta buɗe, idanunsa cikin na Zahra Galadima dake ɗauke da ƙaramar babyn da take goyo. Kallo ɗaya zaka yi mata kasan suna kama da Alkasim ɗin, tun daga kan doguwar fuskarsa zuwa kalar fatarsu. Ɗan ware idonta tayi akan ƙanin nata. "Sannu da zuwa Baban mu."! Ta faɗa cike da tsokana a muryarta dan wata rana haka suke cewa shine babansu a yanzu. Hannu yasa ya karɓi Yasmin yana faɗin. "Kin cika yawo yaya zahra wai ke kullum sai kin fita ne? wannan mijin naki kin rainasa da yawa." Dariya Kawai Zahra tayi tana faɗin. "Bazan ce komai ba matar taka na zuwa zamu gani idan ita kulle zakayi mata." Tare suka ƙarasa cikin falon mami, sai lokacin ya lura da Yaa Hajja da ta ke zaune ita da mami suna magana. Zama yayi a gefen mami ya gaisheta kafin ya gaisa da Yaa Hajjan.
Murmhshi Yaa Hajja tayi tana hango irin ramar da Alkasim ɗin yayi, da gaske ya rame har cikin idonsa. Mami yaron nan ya rame ciwo yayi ba mu sani ba." Yaa Hajja ta faɗa tana mayar da kallonta kan mahaifiyar su. Itama mamin kallon Alkasim tayi sai kuma ta girgiza kai tana faɗin. "Shi yasa nace ku taho ku tsare munshi muji meke damunsa." Da sauri Alkasim ya buɗe ido yana kallon mahaifiyar sa. Sai yanzu ya tuna maganar da suka yi da safe da mahaifiyar sa har yaji tana cewa zata sanarwa ƴan uwansa, ya zata ta manta ashe tana sane. Hannu ya saka cikin lallausar sumar kansa wacce tasha taza sai wani kyalli take. Wargaza sumar kansa ya shiga yi bai ce komai ba.
"Kayi magana Alkasim baka da gaskiya wallahi akwai abunda ke damunka ko?" Zahra ta faɗa tana tsaresa da ido. Tun kafin ya buɗe baki yayi magana Yaa Hajja tayi saurin dakatar dashi tana faɗin. "Mu ƙarasa cikin dinning area muyi lunch sai mu tattauna kaga Zahra ta dafo maka favourite abincinka." Saboda yana son dambun shinkafa sosai, baya gajiya da cinsa, dan haka Zahra ta tsaya tayi masa shi tunda ance baya iya cin abinci. Suna kaunar junan su gabaki ɗaya babu wanda keso wani abu ya taɓa ɗan uwan sa. Tun suna yara mahaifiyar su ta koya musu kaunar junan su. Nan da nan Zahra tayi sarving ɗinsu a plate ɗaya ta shimfida musu ƙaton carpet daga can gefen dining area. Duk yadda Alkasim baya jin daɗin cin abinci a kwanan nan haka ya zage yaci abincin tare dasu. Dambun yayi masa daɗi sosai, haka sukaci dambun cikin raha da barkwanci. Ya rigasu barin wurin ya faɗa musu zaije yayi wanka ya dawo kafin ayi sallar magrib. Bayan wucewarsa ne Zahra ta kalli Yaa Hajja kafin ta ɗora da faɗin. "Da gaske ya rame." "Yes wallahi." Cewar Ya Hajja. "Ku yadda fa akwai abundake damunsa, nidai komai zai faru karku bar gidan nan sai kun tsare minshi anji damuwarsa." Daria Zahra tayi tana faɗin. "Mami kinsan halinsa fa, Allah yasa ya faɗa." Hirarsu suka cigaba dayi a tsakanin su, Zahra nabasu labarin ƙanwar mijinta wacce ke masifar son Alkasim ɗin wacce ke zaune gidan na zahra saboda shi. Bai taɓa ba ta fuska ba ko sun haɗu gaisuwace kawai a tsakaninsu.