Sashe 11
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kusan qarfe goma ya shigo sashen mami, ƴan aiki nata aikace-aikacen su. Bai sameta a falo ba kai tsaye bedroom ɗinta ya nufa sai da yayi sallama aka bashi izinin shiga sa'anan ya shiga ɗauke da wata sallamar bakinsa. Koda ya shiga mamin na zaune gefen gado tana waya. Zama yayi akan soofa yana jiran ta kammala. Ya kai minti biyar kafin ya samu ta gama wayar da wanda take wayar, ta ɗaga kai tana kallonsa.
"Harka shirya kenan?" Ta faɗa ɗauke da murmushi a fuskarta.
"Na shirya mami."
"To Allah ya tsare hanya ga wannan sai ka kaiwa surukar tawa ka gaisheta." Karɓa yayi murmushi ɗauke a kyakkyawar fuskarsa yana yiwa mamin godiya ceke da farin cikin yadda mamin takeson Tauheedarsa. Tun jiya ya sanar da mamin zaije Kano da yake Yaa Hajja ta mata bayanin komai, itama mamin ba karamar murna tayi ba ganin Alkasim ɗin wannan karon da gaske auren zai yi babu shiririta acikin lamarin, dan ko jiya Zahra da Hajja da suka zo gidan da daddare suna sanar da ita Alkasim yana son ayi maganar aurensa da Tauheedah. Mamin tayi murnar da basu taɓa hasasowa ba.
"Ni mami na ɗauka sai sun qara fahimtar junansu kafin ayi maganar aure kin san Alkasim da gaggawa komai baya tsayawa ayisa cikin natsuwa."
"Wane irin jira za'ayi tunda ya samu matar aure kuma ya yaba da hankalinta da dabi'unta? ai kawai zan samu Abbanku nayi masa maganar ko ban samu naje ba ko a waya zan kirasa na gaya masa." Watau Yayan mahaifinsu mai rasuwa. Zahra zata buɗe baki ta kara magana Yaa Hajja tayi saurin kifta mata ido tana ɗan girgiza kai alamar karta ce koma. Sai da zasu wuce gida Zahra Galadima ta kalli Yaa Hajja tana faɗin.
"Kinga mami ta wani biye masa ko. Komai a hankali fa ake tafiyar dashi, Yaa Hajja maganar aure ba abun wasa bane..."
"Kedai kiyi masa addu'a Allah ya sanya Alkhairi." Da haka kowace ta shige motarta ta nufi gidan aurenta.
"Mami bari naje da drivern ki jirgin karfe 11 ɗaya zan bi." Kyakkyawar addu'a mami tayi masa irinta uwa suka yi sallama ya fito.
KANO STATE
Karfe goma ta fito cikin shirin fita sai cika take tana batsewa tunda akwai kudi a account ɗinta batada damuwa sunyi waya da Alkasim jirgin karfe goma sha ɗaya zai shigo. A ɗaki ta samu mahaifiyarta ta faɗa mata zataje gidansu Fauxy ta karɓo saqo. Mama kam banda Allah ya kiyaye hanya babu abunda tace mata, ta daina saka damuwar Tauheedah aranta a kullum addu'ar shiriya take mata. Ɗan sahu ta tare ta faɗa masa unguwar da zataje tana cewa.
"Dan Allah ka ɗan ƙara gudu malam inada uzuri." Bai kulata ba saboda yasan shi iya gudun da zai iya yi kenan. Inda ta nuna masa nan ya tsaya, ta zaro wayarta tana karawa a kunne,
"Gani a ƙofar gidanku dan Allah karki daɗe ina tare da ɗan sahu ki fito mun da canji na bashi." Ba'a yi minti biyar ba Fauxyn ta fito da wani figaggen mayafi akanta sai riga da wandon baccin dake jikinta masu kauri. Nan ta biya mai adaidaita suka shiga cikin gidan.
A falo Tauheedah ta tarar da mahaifiyar su Fauzyn macce wayayyiya da fara'a ta tarbi Tauheedah, yayinda Tauheedah ta duka har ƙasa ta gaishe ta. Kafin su wuce dakin Fauxyn.
"Baki da kirki Tauheedah sai da kika lalatamun bacci hankalinki ya kwanta."
"Uhmm ke bacci ne ma a gabanki ko? Toh albishirinki Hajiyata."
"Sai kin faɗa nasan dai wannan fara'a tayi yawa karki ce mun malam Nura ya siya miki iphone bani nasha." Fauxy ta ƙarasa maganar tana fashewa da dariya. Tsaki Tauheeda taja cike da takaicin Fauzyn take faɗin.
"Ko ɗan ƙaramin gidansu zai siyar bazai isa ya siya mun iphone ba. Muyi magana mai muhimmanci malama. Kawata yau Alkasim Galadima zaizo." Ware ido Fauxyn tayi cike da mamaki
"Dan Allah da gaske kike?"
"Kin taɓa ganin nayi miki kalar wannan wasan? Ai tuni nakama zuciyar wannan gayen xauna nan."
"Uhm.. inji masu ciwon baki, kawata kinyi nisa na yadda ke manyya ce."
"Nidai naji, lokaci na tafiya kaya nazo na ara. Ki tashi ki buɗe mun wadrobe ɗinki na zabi kalar da zan yiwa sahibi na kwaliyya." Da yake kusan jikinsu ɗaya da Fauzyn bata sha wahalar zabar kayan da zata saka dan fita kunya ba. Can idonta ya hango mata sallaya shimfide mai tsadar gaske kalar maroon tana da ɗan girma. Da sauri ta isa ta ɗauki carpet ɗin tana cewa.
"Dole zan haɗa da wannan carpet ɗin na shimfida masa. Kai Allah ya rabamu da talauci
In sha Allahu kakarmu ta kusa yanke sa'a." Suna cikin magana akayi Knocking ƙofar, sai da Fauzyn ta bada izini aka shigo. Ƴar aikinsu ce ɗauke da kayan breakfast, tayi sallama ta aje a tsakiyar ɗakin. Wani kamshin girki mai daɗi na ƴan gayu ya daki hancin Tauheedah. Ita kam shi yasa takeson zuwa gidansu Fauzyn ko dan ta cika cikinta da kalolin girki masu daɗi na ƴan gayu.
"Ki zauna muyi breakfast." Fauxy ta faɗa tana kallon Tauheedah. Tauheedah tuni ta zauna tana faɗin.
"Ai ko bakice ba din wallahi yunwa nakeji banyi breakfast ba na fito." Tare suka karya kumallo agurguje Tauheedah tayi shirin tafiya ganin lokaci na tafiya.
"Kiyi mun alfarma Fauzyn dan Allah." Wannan karon Tauheedah ta faɗa cikin sanyin murya.
"Ina jinki kawata."
"Dan Allah ko zaki aramun kula idan na siyo abincin sai na juye aciki zuwa jibi sai na maido miki da ita."
"Kedai baki da kirki, yanzu akan aron kula kike make murya tamkar wata mutuniyyar kirki? Allah ya shirye ki. Kinga kinzo a sa'a kuwa bari naje store na binciko miki wasu kulolin da Mumy ta siyo a Dubai." Tauheedah tamkar zata goya Fauzyn dan daɗi dan haka takeson Fauzyn, tasu tafi zuwa ɗaya ko cikin kawayensu. Haka duk abunda zata tambayi Fauxyn aro bata kyashin ara mata komai girmansa. Fauzy bata jima ba ta dawo da manyan kuloli har guda biyu a cikin kwalin su. "Kinga Mumy batama yi amfani dasu ba, yanzu haka kika bincika ta manta dasu, kawai ki tafi dasu Allah yace ke zaki fara amfani dasu." Nan da nan Tauheedah ta yiwa Mumynsu Fauxy sallama harda 2k ta bata ta shiga mota. Kai tsaye Tauheeda eatry tace akaita kudinta dubu goma na a jakarta da ta ciro wurin mai pos wanda ko kuɗin cirewar bata basa ba tace sai ta dawo dan bataso ta taɓa su taje ta tarar da ba haka ba.
List aka aje mata na abubuwan da take bukata, jikinta yayi mugun sanyi. Shinkafa plate ɗaya da naman kaza a sama 5k bazasu ma isa ta haɗa da snacks ba da lemun da tace zata siya na kwali. Plate ɗaya ai bazai cika manyan kololin da ta aro gidansu Fauxy ba. Kiran Fauzyn tayi a waya tana faɗa mata ko zata ƙara mata 10k ne? dakyar Fauxyn ta yadda ta tura dan a ɓangaren kuɗi kam Fauzy ba sauki. Plate biyu tayi masa na friderice sai ta siya snacks da 5k da haka ta koma gida
da kaya niki-niki ta shige ɗakin su dasu. Sa'ar ta ɗaya su Waheedah na makaranta da idon da zata saka mata ba'a magana, taji daɗin haka kuma. Koda ta shigo da kayan Mama bata tsakar gida. Fita tayi ta karɓo lemun kwali da ruwan roba masu sanyi. A hanya sai tsaki take tasan koda Alkasim zaizo ruwan da lemun sun huce. Allah dai ya tsinewa talauci dan beyi mata rana ba. Koda ta dawo Alkasim ya kirata kusan kira biyu da yake tabar wayar a gida. Zaro ido tayi da sauri ta ɗauki wayar tayi daillig. Katsewa yayi ya kirata. Sallama yayi mata cikin sanyayyar muryarsa ta amsa cike da jan aji a tata muryar.
"Ya hanya?"
"Alhmdulillahi mun sauka tun dazu."
"Okay Alhmdulillahi." Ta faɗa cikin sanyi murya kafin shiru ya ratsa a tsakaninsu na ƴan sakanni.
"Nan da awa ɗaya zan shigo."
"Allah ya kawo mun kai lafiya." Tana jin sautin murmushinsa kafin ya ɗora da cewa.
"Amin." Da haka suka aje wayoyinsu....
#Tauheeda
#hotlove/Romantic
#Tauheeda Baffa
#Alkasim Galadima
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/22, 7:13 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
9....