Sashe 3
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranta a ɓace ta shiga adaidaita sahu, domin Nura ba ƙaramin bata mata rai yayi ba. Ta fito cikin nishaɗi amma yayi fatafata da nishaɗin nata lokaci ɗaya. Haka lokaci ɗaya bikin da take marmarin xuwansa taji ya fita daga ranta ji take kamar ta juya zuwa gida, idan kuma ta tuna da burin dake ƙasan ranta sai taji kuma tana son ta halarci wannan bikin, dan yadda su Fauzy suka riqa ririta bikin tun ana sauran wata ɗaya, yadda aka riqa tallan bikin a social media tun kafin zuwansa taji tana son taje dan yadda takejin labari kamar angon yaron gwamnan Bauchi ne wanda ya sauka. Tasan kuwa manyan mutane ne zasu halarci bikin shi yasa xataje itama ko zata samu zabin ta acan wanda yayi daidai da ra'ayinta. Ɗan sahu ne ya katse mata tunani yana tambayarta inda zasu je dan tunda ta shiga batayi maganar inda zataje ba. Sai a lokacin ta buɗe baki ta faɗa masa sunan wurin da zataje ɗin suka nufa. Irin kalar motocin da ta hango ana shiga dasu a wurin yasa ta dakatar da ɗan Sahun tun kafin su qarasa wurin.
"Aje ni anan." Ta faɗa masa babu musu yayi parking ta fito ta zuge zip ɗin jakarta, ɗari biyar-biyar ne guda biyu su kaɗai suka rage mata, ɗayar ɗari biyar ta ciro tana miqa masa. Baki ya saki yana kallonta kafin yace.
"Kuɗin ki Naira dubu ne Hajiya."! Wani irin kallo take masa kafin ta ɗora da faɗin.
"Kasan me kake faɗa kuwa? wace irin tafiya ce mukayi zaka wani ce mun dubu ɗaya? Toh ni dari biyar ne dani ka amsa haka Allah yasa masu albarka."
"Gaskiyya dubu ɗaya zaki bani Hajiya." Lokaci ɗaya Tauheeda ta rufe ido daman a cike take ta samu inda zata huce baƙin cikin da Nura ya kunsa mata. Lokaci ɗaya ɗan sahun ya kashe adaidai Sahun tasa ya fito. Cike da izgilanci yace mata ba zai qarbi ɗari biyar ba yana wani irin huci saboda yadda yaga tana masa. Ƙoƙarin karɓe handbag ɗin hannunta yake yi dan ya ɗauki kuɗinsa. A fusace ta dakatar dashi tana faɗin.
"Mekake shirin yi haka Malam? karka taɓani da wannan kazamun hannun naka." Ta faɗa a masifance. Ganin da gaske tara mata mutane zai yi yasa ta ɗakko ɗaya ɗari biyar ɗin ta haɗa ta jefa masa, cike da tsiwa da rashin kunya take fadin.
"Matsiyaci kawai!" Ta faɗa tana jamasa tsaki. Dariya yayi yana faɗin duk mune ƴaƴan gidan malam Shehu." Ya faɗa yana tura mata dariyar haushi. Ɗan Sahunsa yaja yana barin layin tare da yin kwafa dan ji yake da ta yi masa rashin kunya zai nuna mata banbancin rashin kunyar namiji. Kwallar takaici taji tana cika mata idon ta, duk irin wannan kwaliyyar da tayi zai kalleta yana faɗin duk sune ƴaƴan matsiyata? Duk wannan kyawun nata an san ƴar gidan talakkawa ce ita? Cike da wani irin sanyin jiki ta nufi ƙofar shiga event center ɗin. Da sauri yake tahowa waya kare a kunnen sa, kusan karo sukaci da juna, wani irin sanyin kamshi ya doki hancinta wanda bata taɓajin kalarsa ba a rayuwarta sai taji kamshin nata turaren na disashewa a hankali. Wani irin dokawa zuciyoyinsu suka yi lokaci ɗaya. Kuma kusan lokaci ɗaya suka kalli junansu. Ya rigata janye idon nasa saboda yadda zuciyarsa ta cigaba da doka masa. Hannu ya ɗaga mata yana furta kalmar.
"Sorry!!" Cikin wani irin jan aji da kamewa. Anan wajan ya barta da kamshinsa da ya gama cika hancin ta. Sai lokacin ta dawo hankalinta, ji tayi numfashinta na sarqewa. Taja numfashi tana jin zuciyarta na mata wani iri.
"Tauheeda!" Yi numfashi Zuciyarta ta faɗa mata. Numfashi takeja tana saukewa cikin bin umurnin zuciyarta kafin ta dawo hankalinta Haushin kanta ya cika ta. Duk talaucinta tana da wani irin aji na ban mamaki, amma yau ita Tauheeda ce ta kure da namiji da ido har haka? Itace da fita hayacinta har haka akan namiji? Yamutse fuska tayi fuskarsa na gilma mata cikin idanuwan ta. Da wani irin nauyin ƙafa ta shige cikin event center ɗin sai dai ba ƙaramin raina shigar jikinta tayi ba domin Ƴaƴan manyya ne a wurin suna ta gilmawa cike da nishaɗi. Wani irin sanyi jikinta yayi musamman yadda taga ana bin shigar jikinta da kallo, tana jin yadda wayarta ƙirar (TECNO) ke ta faman ringing a cikin jakarta. Kasa fiddo ta tayi ji tayi ta wani irin wulakanta ganin yadda manyan ƴan mata ke fitar da manyyan wayoyi wasu na picking call wasu na selfie wasu kuma suna riƙe da ita a hannu. Gefe ta koma ta ciro wayar tana mayar da ita silent. Fauzy ce mai kiran. Kiranta tayi babu ɓata lokaci Fauzyn ta ɗauka tana faɗin.
"Baki shigo ba ne Tauheeda har munzo wurin fa." Haushin Fauziyyan taji ya cika mata zuciya, meyasa batayi mata bayani ba sosai
Akan tsarin bikin su? sai yau ta raina kanta, ashe koda kanada kyau kana ƙarawa da gyara da kaya masu tsada sai kyan naka ya fito sosai. Da kyar ta faɗa mata inda take. Cike da ɗoki Fauxyn ke faɗin tana zuwa. Mintunan da basu wuce biyar ba sai ga Fauxyn ta bayyana sai dai irin danƙareren leshin da taga Fauxyn ta saka da kanwarta tasha mamaki. Wato Fauxy tace basuyi anko ba, kowa zai saka nashi shine ashe sunyi anko da ƴan gidan su? Toh meta ɗauketa bata da arzikin siyan irin suturar dasu Fauzyn ɗin ke sakawa ko me? A ɓangaren Fauxyn kuwa taso ta nunawa Tauheeda ɗin, dan tasan zata nemu kuɗi tayi ɗin ko wurin samarin ta ne, sai Yayunta sukayi mata caa suna faɗin karma ta fara Iya su kaɗai ƴan gidansu zasu yi karta wani saka musu kawarta. Lokacin rigima aka yi sosai har Maman su ta shiga maganar. Sai dai irin kallon da Tauheeda keyi mata sai taji kamar bata kyauta ba. Zuwa tayi ta rungume Tauheedan tana mata sannu da zuwa, dole Tauheeda ta saki fuska ganin yadda ake kallonsu, Ko babu komai Fauzyn ta karammata cikin mutanen da keyi mata wani irin kallo. Hannunta Fauxy taja tana faɗin.
"Mu ƙarasa wurin ango da amarya." Haka taja hannunta suna dosar cikin hall ɗin. Wurin zama Fauxyn ta bata tana faɗin ta jirata tana zuwa Aunty Hafsat ta aike ta taje tazo da baki a waje. Bayan tafiyar Fauzyn Tauheedan ta mayar da hankalinta kan ango da amarya da sukayi mata kyau sosai. Gyara zamanta ta ƙara yi irin bikin da takeso kenan, nan da nan fara mafarkin tayi dama itace a matsayin amarya. Sosai ta tattara hankalinta kan ango da amaryar dake wani irin nishaɗi, amman sai dai me? tana ɗaga idonta ta hangosa. Wani irin dokawa zuciyarta ta shiga yi da sauri da sauri yana zaune kansa a ƙasa yana danna wayar hannunsu cike da kwarewa, sam bata san tayi nisa ba sai da taji ya ɗago kansa caraf suka haɗa ido ai kuwa tayi saurin ɗauke kanta. Kura mata ido yayi yadda zuciyarsa ke harbawa yasa ya ɗauke kansa lokaci ɗaya, gaba ɗaya yanayinsa ya canja.
"Tana da kyau!!" Zuciyarsa ta faɗa masa, saurin kawar da tunanin yayi a ransa yana basarwa. Kwantar da kansa yayi jikin kujerar yana lumshe idonsa tamkar mai jin bacci haka kamar hayaniyar wurin bata damunsa. Muryar MB yaji akansa yana faɗin.
"Ba dai bacci zakayi mana ba dan kai ko kaɗan bacci baya maka wahala." Buɗe lumsassun idanunsa yayi yana kallon gayen da yayi masa maganar.
"Bana jin daɗi ne da za ka bani car key na koma hotel zai fi min daɗi." Girgiza kai MB yayi yana faɗin.
"Kai ma bazaka fara ba domin Sadiq ba zai ji daɗi ba." Wani irin yamutse fuska yayi yana dafe fuskarsa.
"A aurena babu mai yi mun wannan kalar taron." Ya faɗa sounding so very serious. Dariya Mb yayi yana faɗin.
"Kai da baka da budurwa har ka fara hangowa kanka aure yanzu?." Harara ya bi shi da ita yana kwace car key ɗin dake hannunsa dan ƙara yabar wurin nan saboda sosai iskar wurin tayi masa kaɗan yana jin yadda jikinsa ya ɗauki wani kalar ɗumi. Ficewa yayi daga hall ɗin gabaki ɗaya yana jin kamar yayi tsuntsuwa. A kan idonta ya fice sai kuma taji rashinsa a wurin ya rage mata nishaɗi sosai. Ji tayi zuciyarta na yi mata karfin hali, tana ganin karfe 9 tayi babu alamar za'a watse yasa ta matsawa Fauzy akan tazo su fita ta samu wanda zai mayar da ita gida dan duk tsaurin idon ta da buɗewar idonta tana girmama tarbiyyarta.
"Anya kuwa zaki samu abun hawa anan wurin, saboda nayi ta kiran Fahad da ya kawo su Aunty koshi ya mayar dake amma yaki ya ɗaga. Nasan kuma yana can yana yawonsa a gari." Yana zaune acikin mota ya kure Ac sosai gabaki ɗaya yanayinsa ya canja ya rasa meke damun sa. Tamkar ance ya kalli mirror ɗin motar ya hango ta. Wani irin dokawa zuciyarsa ta shiga yi tamkar zata fito daga kirjinsa, haka ya kasa ɗauke kansa daga kallon da yake yi mata har sukazo suka wuce shi ya kasa ɗauke kansa akanta. Ganin sun nufi hanyar fita daga wurin ya samu kansa da yiwa motar key, duk yadda zuciyarsa ke hanasa akan kar yabi bayan su ya kasa. Jin ana danna musu horn yasa suka juya kusan lokaci ɗaya, ganin farar mota ta tsaya a gefen su sosai motar tayi musu kyau. Tauheeda ce ta fara ɗauke idonta ta cigaba da tafiyar ta. Ganin ana sauke glass ɗin motar yasa Fauxy ƙara gyara tsayuwarta da fara'a sosai a fuskatar take fadin.
"Daman Kaine?!" Ta tambaye shi dan tasan shi yana cikin abokan ango sai dai bata riqe sunansa ba. Shima da murmhshin akan fuskarsa har kuma lokacin hankalinsa na kan Tauheedah da taja ta tsaya a can gefe da alamar Fauxy take jira.
"Gida zaku koma ne??" Ya samu kansa da furtawa.
"Kawatace dai zata koma gida." Numfashin da yake riqe dashi ya sauke.
"Idan babu damuwa zan sauketa nima fita zanyi cikin gari." Ya faɗa da muryar da yake mamakin ta sace kuwa? Yau shine da neman alfarmar ragewa wata macce hanya? anya kuwa kansa ɗaya? ya kuwa san me yake yi? Cike da fara'a Fauzy ta shiga yi masa godiyar da bama fahimta yake ba burinsa kawai
Tauheeda ta shiga motar ko zai samu natsuwar zuciyarsa...