Sashe 8
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ni wallahi mami dama zaki yi magana Ikram nada hankali sosai." Zahra ta faɗa cikin karya kai. "Ki rufamin asiri ku kuna mata ba ayi muku auren dole ba sai shi?." Suka yi murmushi suna cewa ai shi za'a iya yi masa tunda bai kawo wacce zai aura ɗin ba. Sai da aka yi sallar magrib bai jima a masallacin ba ya dawo cikin gidan saboda yayun nasa. Ganin su biyu ne kawai a falon banda mahaifiyarsa yasa ya sauke numfashin da yake riqe dashi. Duka su biyun kallonsa suke da alamar shi suke jira ya fara faɗin wani abu. "Wallahi idan da kaga yadda kazama kayi dogon wuya da baka fara lakawa kanka wannan damuwar ba. Shin meke damun ka ne?" Wannan karon Yaah Hajja ta faɗa tana zuba masa idanun ta. Kwantar da kansa yayi cikin kujerar da yake akai zuciyarsa na bugawa hoton fuskar Tauheeda na wulga masa. Shin me zai ce musu? shi kansa ya gaji ko yayane yana son ya raba damuwarsa dasu.
"Matar aure na samu!" Wannan karon kamar an fisgo maganar daga bakinsa ne, dan shi kansa ji yayi ta taho gabaki ɗaya. Dariyar da Zahra Galadima ta fashe da shine yasa ya dawo hayacinsa. Wani irin murmushi Yaah Hajja ta saki tana cewa,
"Finally our little prince ɗin mu zai angwance." Hannu yasa cikin sumar kansa yana hargitsa ta. Girarsa ɗaya ya ɗage, kafin ya girgiza kai yana faɗin. "Yar Kano ce!" Ya faɗa ba tare da ya jira sun tambaye shi ba.
"Toh Allah dai yasa tana da kyau, tana da class kamar yadda kaima kake tsara matar aurenka a kullum. Mu dai Allah yasa ba mummunan bace ba. Matan da ka riƙa zalunta Alkasim Allah bazai barka ba." Ɗan murmushi ya saki yana faɗin. "Ni babu wacce na zalunta." "Toh munji, yanzu dai a faɗawa mami ta yiwa Abba magana?" Cikin sauri ya kallesu, mamaki yana kama zuciyarsa, daga gaya musu zasu wani fara yayatawa? Cikin yatsina fuska yake cewa. "Nifa ko magana ban taɓa yi da yarinyyar ba, ban taɓa faɗa mata ba ma." Zahra ce ta wara ido tana faɗin. "Toh mekeke jira sai wani ya riga ka? Ji yayi zuciyarsa tayi wani irin dokawa da karfi jin cewar wani zai rigasa samun Tauheedah. Ai ko acikin mafarki baya kawo hakan zata kasance. "Ina taso na kirata na faɗa mata nakasa ne Yaah Zahra, ban san ya zanyi ba, ban kuma san ta ina zan fara ba." Daria Zahra ta fashe dashi tana nuna Alkasim din da yatsan ta tana cewa. "Kai dai wannan ego ɗin naka ka ajesa a gefe wallahi idan baso kake karasata ba. Zan aje maka account details ɗina ta Whatsapp zan tura maka kalaman da zaka faɗa mata copyn and paste kawai zakayi, kaji na rantse maka Alkasim Galadima bazata wuce tayinka ba." Kamar wani ƙaramin yaro ya ɗan cune fuska yana cewa. "Ke dai bazaki yiwa mutum abu dan Allah ba sai an biya ki." Juya ido kurum Zahra tayi tana jin wani nishaɗi a ranta. Yaah Hajja ce tayi gyaran murya tana faɗin. "Idan da gaske kake wannan karon dan Allah kawai ka tunkari yarinyyar nan Alkasim, ni bazamu yi maganar da mami ba har sai kun daidaita kanku da yarinyar kasan halinta da saka abu a rai. Kawai mu bari ku fara daidaitawa da ita yarinyar sai muga abinda za'a yi next." Gyada kai yayi alamar gamsuwa da maganar yayar tashi. Sunata hira har kusan qarfe 9 kafin kowace ta yiwa mahaifiyarsu sallama suka nufi nasu gidan. Kuma duka cikinsu babu wacce ta yiwa mamin magana kawai sun bar sa akan Alkasim ɗin ya fara zuwa ya samu daidaitawa da yarinyar. Kusan qarfe goma na dare har yayi wanka ya saka kayan bacci a jikinsa, ya kunna data messages ne da yawa suna shigowa. Kai tsaye yaje ya lalubo lambar Zahra yayi mata sallama na kusan minti biyu babu reply, kasa jurewa yayi kawai ya sauka ya kirata har sau biyu bata kira ba, sai da aka ci mintuna biyar ta kirasa daman wayar na hannunsa. Da sauri ya ɗaga wayar yana mata qorafin ya kira bata ɗauka ba dan shi ko kaɗan baya son jira.
"Ki bani sakon da kikace ta Whatsapp!"
"Kaifa bakada hakuri wani lokacin, ni na ɗauka sai gobe zamu tsara komai." Da sauri ya katseta yana faɗin.
"Me zai hana yau? Ba kiga yadda nake wahala bane? Mufara yau dan Allah ko zan samu sauqin abunda nake ji." Zahra ta yi murmushi.
"Okay toh ka fara tura mun kudin."
"Zan tura maki yanzun nan." Tace,
"Yauwa bro daga 100k zuwa sama zaka bayar dan kalamai ne masu shegen tsada Mr. Alkasim Galadima." Cikin zakuwa da son ganin ta turo mai yace.
"Ni dai naji." Yana sauke wayar ya mata transfer kuɗi Naira dubu ɗari, aikuwa ba'a yi mintuna goma cikakku ba Zahra galadima ta tura masa messages ɗin nuna soyayya. Ya daɗe yana karanta kalaman. Kasa daurewa yayi ya kirata yana cewa.
"Duk su zan tura mata?" Ya faɗa da wani yanayi cikin muryarsa.
"Yes su zaka tura ko ba su yi bane?"
"No kawai dai sunyi yawa!" Ya faɗa muryarsa na fitowa sarari.
"Auhhh Allah? daman kalaman Soyayya na yawa ne? Dole fa wannan ego ɗin naka kasaukesa Alkasim, soyayya ba'a mata haka, kana sonta dole kabi hanyar da zaka sameta. Ni dai sai da safe." Tana faɗa ta kashe wayar. Alkasim kuwa ya daɗe yana juya wayar a hannunsa ya rasa ya zai yi. Whatsapp ya koma yana bin kalaman da Zahra ta tura yana haddarsu. Tab, wannan wane irin shirme ne? wannan ai ɓata lokaci ne ya tsaya yana irin wannan maganganun. Lambar Tauheedah yaje ya lalubo a cikin WhatsApp ɗin yaga last seen ɗinta tun karfe tara na safe. Sallama ya tura mata kawai ya sauka. Koda zai yi bacci ya kunna data yafi a kirga har zuwa lokacin Tauheeda bata online. Ji yayi zuciyarsa na katsewa, yana son ta hau suyi magana da gaske yana son jin motsinta. Har bacci ya ɗauke sa.
Wani irin kunci takejin kanta a cikinsa, yau tunda tayi sallar asuba bata koma ba, tun jiya bata da kuɗin data, lokacin da suna tare da Nura da yanxu ya tura mata ga account ɗinta ko sisi bata da shi, dan haka yau da safe ta dage ta taya Mama kunun kokon da suke da safe tasan zata samu ƴan canjin siyan data. Haka kuma ta kasance ɗin bayan angama siyar da kunun wurin karfe 9 na safe ta gama wanke-wanke lokacin kannenta sun tafi makarantar boko. Mama na fitar da kuɗin da zata siyo gero a kasuwa tana ware ƴar ribar da ta samu wacce ba tafi ta Naira dubu ɗaya ba. Tauheeda tana zaune gefenta ta wani saukar da murya tana faɗin. "Dan Allah Mama ki bani ɗari shidda ko 2gb ne na saka nayi maneji tun jia bani da data." Girgiza kai Mama tayi tana faɗin. "Dagaske baki da hankali Tauheedah. Toh ribarce nakeso na siyo kuli-kuli da rana muyi gurasa aci tunda akwai sauran fulawa." Wani irin tura baki Tauheeda tayi tana faɗin. "Duk hana idona baccin safen da nayi Mama? Ni to shikenan ina ladan aikina.? A bani na siyo dasu." Mama da dama tasan ba dan Allah aka taya ta aikin ba tace "Ai daman nasan bazaki yi mun aiki haka kawai ba. Ga ɗari biyu ki saka datan." Hannu Tauheedah ta saka ta karɓa kamar zatayi kuka. Tana yi tana tsinewa talauci a ranta. Sai da ta karya ta nufi bakin titi neman datar....
#Tauheeda
#lovestory2025
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/21, 12:28 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
7...