Sashe 14
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Buɗe ƙatuwar kular dafadukar wake da shinkafa tayi wacce taji alayayyahu da kayan ciki tayi kyau sosai a ido ga wani ƙamshi dake tashi a cikin ta, tabbas ta ɓangaren sarrafa girki tana jinjinawa Maman su domin ba dai a ci ace babu daɗi ba. Shiru Tauheedah tayi tana ta kallon abincin da kular da aka zuba abincin aciki. Ita kam tayi da ta sanin kai kularsu Fauxy da wuri, tunda gashi yanzu ranar fita kunya tazo kuma duk bata dashi. Gashi dama abincin ba wai ya kwantawa Tauheedah bane, dan tana ganin dafadukar wake da shinkafa ai Mama raini zata janyo mata a wurin surukkanta. Tamkar zata yi kuka ta nufi ɗakin Mama tana wani haɗe rai. Tsaye tayi a bakin ƙofa suka haɗa ido da Aunty Hauwa wacce suke uba ɗaya da Maman su kuma itace mahaifiyarta ta riqe Mama Hadiza. "Yanzu saboda Allah Aunty Hauwa, shin Mama ta kyauta kenan? Dafadukar wake da shinkafa za'a basu??" Ta faɗa cikin rawar murya. Baki buɗe Aunty Hauwan ke kallon Tauheedah tana mamakin ta.
"Ohh shi ba abincin bane ba marar kunya? Ko duk yadda baiwar Allah ɗin nan t ta dage tayi miki abinda za'a bawa bakin ki, shine yanzu kike wani cewa wai ke dan me? Ina zaki kai rayuwa Tauheedah? Ba a haka ya ganki ba ya kuma ce yana sonki? Ki guji rayuwar nan wallahi. Kuma shi aka ga damar yi ɗin kiyi duk abinda zakiyi." Cike da turo baki da takaici take faɗin.
"Aunty Hauwa suna da kuɗi fa sosai ba kowa ne irin abinci suke ci ba. Kuma dan Allah ji kular da aka zuba musu abinci wannan ai sai su raina mu." Ta faɗa a fusace tana barin ƙofar ɗakin kamar zata kifa ƙasa. Sai da Mama tayi mata rantsuwa da jan ido akan babu abincin da za'a siyo a waje a gida za'a girka a basu, idan sunga dana suci. Idan sunga dama kuma su barshi. Lemu kawai ta aminta a karɓo musu, shima dan basu da abun da zasu basu mai ɗan sanyi sanyi ne.
"Iskancin Tauheedah yawa ne dashi. Toh karya takeso muyi musu dan uban ta?." Aunty Hauwa ta faɗa sounding so very fed up.." Wani irin dogon tsaki taja tana cigaba da faɗa daman kuma faɗa aunty Hauwan gareta sosai, ba kamar mahaifiyarsu Tauheedah ba mai sanyin hali.
######
Wata irin tarba wakilan Alkasim suka samu a wurin Kawu kaya na mutunci ya saka harda babbar riga shi da amininsa malam Sallau. Yadda Kawu ya natsu zakuyi tunanin wani babban shehin malami ne. A nan yayan mahaifin Alkasim Galadima watau Alh Ibrahim Galadima ya gabatar da kansa a matsayin uban Alkasim kuma waliyinsa shi da abokinsa. A nan suka nemarwa Alkasim auren Tauheedah cikin dattaku. Haka suka ce a yanka musu sadaki zasu biya. Kawu ya gyaɗa kai yanata yaba nagarta irin ta waɗannan mutanen. Ko daga ganin shigar jikinsu kai kasan kuɗi sun zauna ta kowane ɓangaren. Shi kam kawu kakarsa ce ta yanke saqa yana ganin xai yi kwana biyu yana cefane a gidansa. Cikin rashin damuwa domin shima so yake ya samu. Dan haka yace.
"Mun yanka sadakin ƴar mu naira dubu ɗari biyu." Kawu ya faɗa yana jin irin girman kuɗin da ya zabtaro sai addu'a yake yana raba ido Allah yasa su bayar karsu nemi ragi. Murmushi Alh Ibrahim Galadima yayi ya miqe tsaye yana faɗin yana zuwa. Wannan karon banda dokawa babu abunda kirjin Kawu keyi, yana mamakin ina kuma Alhajin zaije? kardai kuɗin da ya faɗa sunyi masa nauyi? Idan haka ne kuwa wannan Alhajin ya cika matsolo. Yo ko motar da su ka zo da ita ai abun kallo ce sunfi karfin million ma bare wata two hundred thousand. Duk Kawu ya rasa natsuwar zuciyarsa saboda zillimi. Koda Alh. Ibrahim ya fita ƙofar gida driver ya yiwa umurni ya fito da duka kayan dake cikin booth ɗin motar. Haka kuwa driver ya shiga fiddo manya-manyan kwalayen lemukka da biscuits da sweet tamkar za'a buɗe shago dan yawan su. Haka ya saka yara suka rinqa shiga da kwalayen cikin zauren su Tauheedah. Da sauri Kawu ya miqe tsaye. Haka aka rika lodasu wuri ɗaya. Ganin wurin bai isa ba gashi basu qare ba Kawu ya yiwa yara umurnin su shiga da sauran cikin tsakar gida. Kaya ne masu yawan gaske haka yaran suka gama lodasu. Da sauri Kawu ya saka hannunsa cikin aljihun babbar rigarsa yana laluben canji dan ya baiwa yaran, har ya taɓo canji sai yaga Alh Ibrahim Galadima ya fito da ƴan dubu-dubu sababbi dal ya miqawa kowane yaro ɗaya-ɗaya, haka yaran suka tafi suna murna. Bayan yaran sun fita su Alh Ibrahim ya zauna ya miqawa Kawu wani babban envelope. Da sauri Kawu ya amsa.
"Kuɗin sadakin ƴar mune naira miliyan ɗaya. Allah yasa ayi damu." Sai ya qara fiddo da wani envelope ɗin a karo na biyu yana faɗin.
"Wannan Naira dubu ɗari biyar ne kuɗin saka rana." Nan fa duk Kawu ya sake gigicewa, a ruɗe yake jiki na rawa ya amsa. Baffa Ibrahim ya saukar da murya yana faɗin.
"Sauran saka rana Alhaji ina jin ku ya dace ku faɗi lokacin auren." Da sauri Kawu yace.
"Duk ranar da kuka saka ai mu a shirye muke Alhaji, ko ba haka ba malam Sallau?" Kawu ya juya gun amininsa yana tambayar sa. Da sauri malam Sallau ya ɗaga kai dan shima tunda aka faɗi kuɗin sadaki shock ya kamasa. Baffa Ibrahim yayi murmushinsu na manya da dattako yana faɗin.
"Mu dai a bangaren mu mun saka nan da wata biyu, bamu sani ba ko hakan yayi muku idan kuna da shirin da zakuyi sai a ƙara." Da sauri Kawu yace.
"Ba wani shiri, hakan ma yayi Alhaji Allah ya tabbatar mana da qlkhairi."
"Amin." Baffa Ibrahim ya faɗa kafin suyi haramar tafiya.
"Alhaji ga abinci an kawo ko taɓawa bakuyi ba."
"Mungode wallahi a koshe muke." Suka faɗa suna barin wurin. Har mota Kawu ya rakasu yana musu fatan sauka lafiya. Sai da motar ta ɓace masa ya koma cikin gidan ya dubi amininsa da sauri jikinsa na rawa yake faɗin.
"Sallau kodai banji daidai bane kuɗin sadakin nan duk na ruɗe fa." Kawu ya faɗa yana ciro envelope ɗin ɗaga cikin aljihun babbar rigarsa. Zama yayi suka buɗe kuɗin shi da malam Sallau. Zuciyarsu wani irin motsawa tayi kakaf rayuwarsu basu taɓa ganin kuɗi irin haka ba a fili sai a cikin tv. Banda zaro ido babu abunda kawu keyi. Cikin rawar murya yake faɗin.
"Sallau kuɗi..! wallahi kuɗi ne!!" Da sauri Kawu ya mayar da kuɗin ya sassauta murya yana faɗin.
"Mu fara cin abincin tukuna malam Sallau sai mu shiga ciki na nunawa Hadiza kuɗin, idan ya kamata nabarsu a hannuna sai na barsu." Kular abincin da aka kawowa su Abba Ibrahim suka buɗe suka hau cin abinci kamar Allah ya aiko su. Sai da sukaci suka koshi sa'anan kawu yace malam sallau ya jirasa. Ko kaɗan malam Sallau baiso hakan ba shi so yayi ayi komai agabansa abasa hakkinsa na ganin ido dan yasan halin kawu gameda son kuɗi. Kawu yayi sallama cikin gidan. A tsakar gida ya tsaya, da sauri Mama ta fito tana masa sannu da zuwa, Aunty Hauwa ta ɗakko tabarma ta shimfida masa. A nan Kawu ya shiga yi musu bayanin komai da ya faru. A karshe ya fitar da kuɗin ya aje gabansa yana nunawa Mama. Mama da Aunty Hauwa suka yi Allah ya sanya alkairi. Daga karshe kawu ya buɗe baki yana faɗin.
"Zanje da kuɗin na aje su a hannuna, abunda aka kara haɗawa sai a haɗa a siya mata kayan ɗaki. Daga Mama har Aunty Hauwa binsa suke da kallo musamman Maman da tasan halinsa, gaba ɗaya ma zancen aje kuɗi hannun Kawu baima taso ba. Aunty Hauwa tayi wuf ta kwashe kuɗin cikin sauri tana girgiza kai take fadin.
"Gaskiya malam Mamman ba za'a yi haka ba. Kuɗi wurin Uwar yarinyar nan za'a aje su. Watau sai yanzu kasan yaran suna da muhimmanci a wurinka kenan ko?" Wani irin kikifta ido Kawu ya shiga yi yana kallon Mama yaga ko zata yi magana amma sai yaji tayi shiru. A fusace yake faɗin.
"Hadiza ki shiga tsakani na da kanwarki, ina ruwanta da abunda ƴaƴan ƴan uwa zasu samu? suna da wanda zai daura musu aure bayanni kanin uban su ne? Keee! Hauwa kike ko wa? Toh bari kiji ko ma wacce ce ke tun muna ganin juna da sauran mutunci ki mai domin da kuɗin auren ƴata kafin aji kan mu."
"Ai wallahi kuɗin nan sunzo hannu malam Mamman, kawai kaja tsumman rayuwarka kayi gaba sai kuma ranar ɗaurin Aure." A fusace ya juya kan Mama yana faɗin.
"Hadiza kina gani ƙanwarki ke ci mun mutunci."
"Yadda ta faɗa haka za'ayi malam mamman zan adana kuɗin. Zan haɗa dana wajena dan na yiwa Tauheeda kayan ɗaki." Ɗaga kai Kawu ya shiga yi tamkar kadangare mamakin Mama Hadiza da kanwarta bakaramun kashesa yayi ba shi bai dauka xasuyi haka ba , da sallama kawai zaiyi masu bazai ma shigoba sai idan yaje gida yagama lissafi. Ya kirata a waya ya sanar mata Bakaramun sakawa kudaden nan rai yayi ba harso yayi ya qara aure cikinsu.sai gashi Hadiza da kanwarta sun cucesa sun ruguza komai yasan duk Masifar da xaiyi bazasu yadda su damka dukiyar auren yarsu a hannunsa ba. sauran lemukka da kayan makulashe Aunty Hauwa ta fitarwa yarinyar nata ta fitarwa Mama Hadiza da dangin ta. Sauran kuma aka miqawa Kawu. Nan ma Kawun rainawa ya yi yana jin kamar ransa zai fito. Mama Hadiza ta bashi 5k tace suyi na mota. A rai ne ya karɓi kuɗin yana tsinewa Mama Hadiza da Aunty Hauwa aransa. Dole ma ya samu lambar mijin Tauheedah dan yaga alamar Mama Hadiza ba zata bari yaci arziki ta ɓangaren ba. Haka kawu yaja talkaminsa yayi waje...
#Tauheeda2025
#Love/Romance
#Asmy b Aliyu
#08086207764
[6/24, 6:21 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
11...