← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kawu na fitowa yara yasa mu a waje yace su shiga cikin gidan, tare dashi suka shiga, yana nuna musu kwalayen da iyayen Alkasim suka kawo na neman aure, nan suka shiga kwaso mashi alawa da katon-katon ɗin lemukka. Gefe kuma Malam Sallau ne sai faman gyaran babbar riga yake yi ganin yadda ake fitowa da kwalaye wanda yasan sai ya kwana biyu yana cin abinci da lemu a cikin turakarsa zai boye ko matarsa Tasallah bazata san da zamansu ba. Cikin adaidaita sahu malam Sallau ya kasa daurewa ganin yanayin da Kawun yake ciki wato duk ya canja ba kamar yadda aka karɓi neman auran da aka zo aka yi ba.
"Wai me ya ke faruwa ne malam Mamman ?"
"Uhmm." Kawai Kawu ya iya cewa. har qofar gida mai adaidai sahu ya saukesu, nan ma sai da sukayi da ɗan sahun dan sai da Kawu ya kafe yace bazai ba ɗan sahun kuɗi har naira dubu biyu ba shi dubu ɗaya zai bayar. Nan ɗan sahu ya kashe mashin ɗinsa ya fito cike da tsantsar masifa akan fuskarsa. Mutane suka taru akansu dakyar Kawu ya bada 2k ɗin nan yana ta jawa ɗan sahun Allah ya isa yana mai yi masa bakaken addu'o'i akan Allah yasa ya samu wanda zai fisge abun hawan yaga ƙarshen rashin kunya. Gabaki ɗaya Kawu  duk ya haɗa zufa saboda bala'i. Yara ya samu suka shigar masa da kayan cikin gida, sai katon ɗin lemu ɗaya da ya warewa malam Sallau a matsayin nasa.
"Me kake nufi da hakan mamman??" Malam Sallau ya faɗa cikin fushi.
"Duk wannan kayan kana nufin wannan kawai zan samu?" Da mamaki Kawu ke faɗin.
"Auhhh daman kana tunanin rabawa za'ayi dai-dai? Toh me muka haɗa da kai banda makwabtaka? kaga malam Sallau raina a ɓace yake daman, kawai kabani wuri karka qara ɓata mun zuciya." Wannan karon baki buɗe malam Sallau ke kallon Kawu . A fusace yake faɗin.
"Abinda zaka faɗa mun ma kenan ko? toh shikenan kuɗin fa?" Wannan karon wani kallon ƴan iska Kawu ya riqa jefawa ta saitin Malam Sallau yana cewa.
"Ohh wai dama ka saka ranka a wannan kuɗin ne? toh tun wuri kama cire dan masu iko da yarinyar sun qarbe kudaden sun ce kayan ɗaki za'a yi mata dasu. Hmmm kama godewa Allah mun samu sun bamu na dawowa." Ai tuni Malam Sallau ya dire gaban Kawu Isa yana wani huce yake faɗin.
"Ni zaka yiwa wayau mamman?"
"Toh ai sai ka cajeni duka tunda baka yadda dani ba." Juyawa Kawu  yayi yana haɗa babbar rigarsa da nufin shiga cikin gida A'i kuwa rai a ɓace malam Sallau ya kamo masa riga ya kankance ido yana faɗin.
"Ka bani kuɗina na tafiya dama ara nayi a gunta Tasallah kuma kasan ba mutunci ne ya isheta ba, yanzu nan sai makwafta duka sun jimu daman ara nayi na ɗauka zamu samu wasu kuɗin ne idan munje."
"Lallai ma, kai daman kasan bakada kuɗi ka kwashi jiki kabini? aiko ni nan da kake gani ko sisi bazaka samu ba wallahi. Kawai idan kaje ka haɗata da gorar lemu ɗaya, nasan tuni zata manta da wata ɗari biyar ɗinta musamman idan taga na banza ne. Kuma kaga an daɗe ba'a haɗu ba." Da haka Kawu ya baza babbar rigarsa ya shige cikin gidansa. A tsakar gida ya tarar da matansa suna duba kayan tamkar za'a buɗe sabon shago. Qara tamke fuska yayi ya kirga kayan yaga suna nan yadda ya saka aka shigo dasu. Ya zura ɗayan hannunsa cikin aljihun wandonsa ya fito da wani tsohon mukullin da ya gama zama baki saboda tsufa da yawan taɓawa, ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga ya cire babbar rigarsa yabarta anan kan gadonsa na karfe ya koma tsakar gidan ya riqa kwasar kayan yana sakawa cikin ɗakinsa. Sai da ya kwashe kayan nan tass matarsa ta farko mai suna Baraka ta kasa durewa ta kallesa tana faɗin.
"Malam wai duk wannan uban kayan na neman auran ƴar wajen Hadiza ne?."
"Ehhhh." Kawai yace kamar mai ciwon baki ya shiga ɗakin nasa ya fasa katon ɗin lemu ɗaya ya ɗauki guda shida ya fita tsakar gida yaba matansa ko wace guda uku-uku ita da Ƴaƴanta.
"Malam duk wannan uban kayan wannan kawai zaka bamu?" Cewar Tsahare amaryar sa.
"Idan bakwa so ku kawo tunda ku kaɗai keda bakin sha bamu da dangi." Ya faɗa rai a haɗe ya juya ya shige ɗaki. Nan ya fitar da lemu katan ukku a gefe, ruwan sha ma haka sai biscuits da ya ciri kwali biyu zai riqa sha a ɗakinsa ya rage zafi. Sauran kuma duka siyarwa zai yi ya samu ƴan canji babu dangin da za'a rabawa tunda ba uban wani ke cida yaran ƴan uwan na saba ko acikin dangin. Shi yanzu kawai jira yake a yi magrib duhu yayi wurin Isuhu mai provision zaije su sasanta.

####
Chapter 15 · 0% Book details