Sashe 5
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
4
Kamar kullum kananun kayane ajikinsa yana zaune akan mashin ɗinsa roba-roba, tun kafin ta isa wurinsa kamshin turarensa ya ziyarci hamcinta. Duk son turaren Nura da take yi sai yau taji yayi mata wani iri na daban. Tun kafin ta ƙaraso wurinsa tana hango fara'ar dake kwance akan fuskarsa, lokaci ɗaya kuma ya sauko daga kan mashin ɗin yana ƙarasawa wurinta still wearing a big smile kwance akan fuskarsa. Yana son Tauheeda da dukkan zuciya da ruhinsa. Ko ya ya ta ɓata masa rai ba zai ɗauki dogon lokaci ba ɓacin ransa yake cirewa, Tauheeda tayi folding hannunta akan kirjinta fuskar nan tata babu fara'a a cikinta.
"Sannu da karasowa gimbiyar mata."
"Yawwa sannunka kai ma.!!" Ta faɗa da yanayin da yasa jikin Nuran ya ƙara yin sanyi. Ganin yanayin ta yasa Nura ya saukar da murya yana faɗin.
"Wai har yanzu baki huce ba ne? Nafa baki hakuri."
"Waya faɗa maka fushi nake yi? Ni daman bako mai yasa na tura maka saqo ba, akwai abund nake so na faɗa maka ne." Saurin katseta Nura yayi cike da zumuɗi yana faɗin.
"Nima kuwa akwai albishir ɗin da nake so nayi miki kusan guda ukku." Ya faɗa yana kallon yanayin ta. Jin taki cewa komai, yasa ya cigaba da fadin.
"Na farko zan siyarda mashin ɗina zan siyarda gonar da na mallaka ta wurin Baba, zan cika na ƙarasa ginin gidana. Sauran kuma sai na siya mota koda second hand ce saboda naga kina so. Sai maganar auren mu zan kamalla karatuna a wannan shekarar, dan haka za'a yi auran mu bada jimawa ba, shine albishir na ukun." Ya faɗa yana kallon yanayin da yake kwance akan fuskarta sai yaji jikinsa yayi sanyi kamar ba Tauheedar da ya sani ba ce,
da ada ne zai ga fara'a saman fuskarta, amma banda yanzu da yaga baya son yaga wannan yanayin akan fuskarta.
"Kin san Yaya Auwal ya shigo gari jiya kuma ya taho da babban alkhairin da nasan idan kikaji zakiyi farin ciki. Amma kafin na faɗa miki meye tukuicina.??" Ya faɗa da zumuɗi sosai a muryarsa.
"Kawai ka faɗa kai nake jira." Ta faɗa cike da kosawa. Takardar dake hannunsa ya miqa mata. Karɓa tayi tana bin takardar da ido fitilar wayarsa ya haska mata tana bin rubutun takardar daki-daki. Form ɗin scholarship ne na jami'ar Ado Bayero. Ji tayi yana cewa.
"Kin san ɗan majalisar ƙaramar hukumar (Gaya) abokinsa ne da kyar ya bani wannan ɗin ma. Gashi nan sai ki cike na mayar masa kinga burinki ya kusa cika zaki fara karatu a jami'ar Ado Bayero nan bada jimawaba. Kuma duk ƙarshen wata zaku riqa samun alawans acikin asusun bankinku za'a ɗauki nauyin karatunku har ku gama. Tauheedah kuwa duk wannan zubar da Nura keyi bama fahimtar sa takeba ita har ta fara hango kanta a matsayin matar Mr. Galadima, tasan da sanin zai kirata tabbas zai kira kamar yadda ya karɓi number. Tasan akwai uzurin da ya riqesa yanzu tana jin kanta tafi qarfin kowace irin alfarma ta Nura kamar yadda tafi ƙarfin Form ɗin scholarship indai zata zama matar Mr Alkasim Galadima, ita tasan a yanayinsa ko a ƙasar waje take son yin karatu zatayi sa. Meyasa yanzu zata tsaya kula kananun mutane irinsu Nura? sai yanzu take jin haushin kanta na kula shi dan akwai tazara mai yawa tsakaninta da Nuran, bata san meyasa ta fara kulasa tun farko ba. Gashi dan ya raina mata hankali motar ma second hand zai siya ba irin wacce take mafarkin samu ba. Miqa masa Form ɗin tayi tana kallon tsakiyyar idanunsa tana hango yadda fuskarsa take ɗauke da bayayyannen mamaki.
"Nagode da dukkan kulawarka malam Nura, but ina mai kuma baka hakuri ni gaskiyya bazan iya aurenka ba, ni na san kona aureka zan takura ne zan wahala karshe ba zamu taɓa farin ciki ba dagani har kai ba. Kasan burina tun farko bazan yi auren wahala da takura ba kamar yadda na taso a gidan mu cikin talauci. Gaskiya bana son na shiga gidanka mu ɗora daga inda aka tsaya, ƙara tun wuri mu raba hanya da juna kowa yaje can ya samu daidai dashi ina maka fatan alkhairi acikin rayuwarka, Allah ya baka kalar maccen da zata dace dai-dai da rayuwarka. Sannan dan Allah karka ƙara kirana a waya, kawai idan mun haɗu a hanya muyi zumunci shikenan." Maganganunta yaji suna wani irin bugar masa kai wanda yake jin hakan har cikin ƙasan zuciyarsa kafin wani haske ya riqa gifta masa ta cikin idanunsa. Jin wani irin jiri na kwasarsa har kafafunsa na kasa ɗaukarsa yasa ya dafa bango yana jin numfashinsa na wani irin sarqewa. Duk wannan mummunan yanayin da Nura ya shiga lokaci ɗaya ko kaɗan zuciyar Tauheedah bata girgiza ba, daman tana son kanta da yawa, me yasa tausayi zaisa ta kasa cikawa kanta burin ranta? Juyawa tayi tana masa sai da safe bata kula da ya amsa ba ko bai amsa ba tayi shigewarta cikin gidan su tabar Nura da tashin hankalin da tunda yake a rayuwarsa bai taɓa shiga cikin tashin hankalin da yake ciki ba yanzu, Rabonsa da ya shiga wannan mummunan yanayin shekara biyar a baya lokacin mutuwar mahaifin sa. Yafi minti goma, amma ya kasa yadda da abunda Tauheeda tayi masa yanzun nan. Wata zuciyar ce ta faɗa masa ba Tauheeda bace yasan wasa take masa. Lalubar numberta yayi ya shiga kiran ta, sai dai bata ɗauka ba, kira kusan biyar yayi mata amma bata ɗagawa. Samun wuri yayi kan dakalin dake qofar gidan ya dafe kansa da hannu biyu yana jera kalmar innalillah wainnah ilaihir Raji'un. Ji yayi wani zazzabin tashin hankali yana neman ya rufesa lokaci ɗaya akan wannan abun.
Koda ta koma gida babu kowa a tsakar gidan dan haka tayi shigewarta ɗaki jin kanta tayi sakayau, tasan Nura idan yana da zuciya ya hakura da ita kenan har abada. Tauheedah tana ganin kiransa taja wani irin tsaki ta mayar da wayar duka a silent, tarasa kalar zuciya irin ta Nura. A ɓangaren Nura kuwa kafin ya isa gida wani irin zazzaɓi mai qarfi ya rufesa da kyar ya iya tuko mashin ɗin ya dawo gida, ko cikin gida bai ƙarasa ba wurin Innarsa sun gaisa, kawai ya buɗe ɗakinsa dake soron gidan ya faɗa kan katifarsa. Wani irin sanyi yakeji a jikinsa ga wata irin makyarkyata da yake yi .alamar zazzaɓi mai qarfi ya shige sa. Har kusan qarfe tara Inna dake zaune a ƙofar ɗakin ta tana zuba gyangyaɗi tana jiran Nuran ya shigo amma bai shigo ba kuma taji ƙarar mashin ɗinsa tun ɗazu alamar ya dawo kuma taji qarar buɗe dakinsa alamar an shiga. Tayi mamakin da har yanzu bai shigo ya ɗauki abincinsa ba. Ta kalli autarta da tayi nisa wurin rubutun da ya tarar mata na biology da tayi sati biyu bataje makarantar bokon ba saboda ta kwanta ciwo shine yau da taje ta karɓo duka subjects ɗin da aka wuceta tana yi.
"Rabi'ah jeki ki dubo Yayanki Nura lafia naga har yanzu bai shigo ya ɗauki abincin sa ba ga dare yanayi kuma tun ɗazu ya shigo gidan." Rabi'ar ta aje rubutun da takeyi kasancewar babu wutar lantarki ba'a kawo ba yasa ta ɗauki ƴar qaramar fitilar hannun da take rubutu da ita ta nufi soron gidan su. Tsayawa tayi a bakin ƙofar ɗakin tana doka sallama har sau uku. Jin shiru yasa ta fara kiran sunan Yayan nata, amma nan ma shiru taji, wata zuciyar ta faɗa mata kodai yana ƙofar gida? daman idan bai yi nisa ba yana barin ɗakinsa a buɗe. Ɗaga labulen ɗakin tayi, sai dai wani irin duhu take gani dako tafin hannunta bata gani yasa ta fara zaro ido. Nishi taji hakan yasa ta haska fitilar dake hannunta, hango Yayan nata cikin mummunan yanayi yayi matukar ɗaga mata hankalinta. Qarasawa tayi wurinsa tana kiran sunansa da qarfi.
"Yaya meya sameka?" Rabi'a ta faɗa a ruɗe jin Nura yayi shiru sai rawar sanyi da yake yasa Rabi'ah ta ƙara tsorata. Da gudu ta fice daga ɗakin tana ƙwalawa Innar su kira. A gigice Inna ta miqe tsaye tana tambayar Rabi'ar menene? Rabi'ah na sauke numfashi take faɗin.
"Inna Yaya Nura bashi da lafiya gashi can kwance yana rawar sanyi." Rabia'h ta ƙarasa maganar da wata irin raunanniyar murya.
Da ita da Inna suka ƙara komawa ɗakin Nuran, Inna tayi tsaye tana tambayarsa meke da munsa? Nura ya kasa cewa komai wani irin nauyi kirjinsa yayi masa wasu hawaye masu dumi ke zuba akan fuskarsa, addu'a yake Allah yasa mafarki yake yi dan har yanzu ya kasa gasgata duk abunda ya faru tsakaninsa da Tauheedah. Babu kalar tambayar da Inna da Rabi'ah basu yiwa Nura ba sai dai yaki cewa komai, babu shiri inna ta lalubo lambar Yayansa Auwalu daman su huɗu ta haifa Yaya Meri itace babba tana gidan aurenta harta aurar da ƴan mata biyu. Sai Auwalu da ko auren farin bai yi ba, sai Nura dake shekarar karshe a jami'a sai auta Rabi'a dake aji biyar a secondary school.