← Book details Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har lokacin bakin Tauheeda yaki rufuwa saboda wata irin murna da alfahari wai itace aka biya sadakinta har 1m. abunda take gani a social media wurin ƴaƴan masu kuɗi shine yazo kanta, lallai Allah abun godiya ne alhamdulillahi dole ta gode masa saboda ya dubi zuciyarta ya bata daidai da zaɓinta.
"Yanzu dai duk ba wannan ba Yaya kin san Kawunan nan nasu ba kirki ne dashi ba, yanzu wurin masu katako kawai xamu miqa kuɗin nan ayi gadon dubu ɗari biyar kujurun dubu ɗari uku, sauran kuma sai ayi labulaye in yaso wannan na saka ranar mu tanadi na kayan kitchen." ko yaya kikace?"mama ta sauke ajiyar zuciya tunanin da nake tayi kenan hauwa,Allah ya rufa mana asiri
Sai ki wuce dasu sai ki kai inda kika san za'ayi masu kyau tunda kinada mutane.....wane wai kudi za'a kaine
Wa zaayiwa kayan katako,nifa mama ba anan tunani na yake ba kwata-kwata ,nida nake mafarkin a gyara gidanmu kafin biki kuke wani maganar kayan daki ,tiles nakeso ayi tsakar gidan nan a cire qaramar kofa a sawo get a saka Kinga idan yan uwansa sunzo bazasu rainamuba."
"Ni dai kawai ku aje maganar kayan katako ayi magana mai muhimmanci, nasan ma gidan Alkasim xai xuba mana komai basai kun wahalar da kank....." Kafin ta qarasa Aunty Hauwa ta ɗauke ta da marin da Tuheedah taji har cikin tsakar kanta. Dafe fuskarta tayi cike da mamaki take kallon ƙanwar mahaifiyar tata. Cikin dariyar takaici Aunty Hauwa ke fadin.
"Karyar da kika shirya kiyi kenan? toh kifitar da ranki akan waɗannan kuɗin sai idan wani wurin zakije ki samu kuɗi kiyi hakan. Shashasha kawai.." Ana nemar miki mutunci kina hauka? Ke  komai sai kin yi hauka? Wannan fa salan kijawa kanki raini ne a wurin dangin miji tun kafin ki shiga zaki wani ce shi zai yi kayan ɗaki. Lallai Tauheeda ashe baki da hankali tun can da tunani sai yanzu na tabbatar. Toh nabi tiles da saka gate da gudu shashasha kawai." Aunty Hauwa ta faɗa a fusace ta miqe tsaye da hijab a hannunta ta kalli Mama tana faɗin.
"Bari na tafi na samo mai adaidaita tazo na kwashi kayan da aka fitar mana na dangi, ni kam bazan iya jiran Waheedah ta dawo daga makaranta ba dan ta samo min ɗan sahu ba ƙara nabar gidan kafin zuciya ta debe ni na nakaɗawa Tauheedah shegen duka a yanzu yanzun nan." Bayan fitar Aunty Hauwa cikin shesshekar kuka  Tauheedah ta kalli Mama take faɗin.
"Ni meye ma laifina saboda Allah da Annabi Mama? Nifa mutuncin gidan nan fa zan kankaro. Kuma hakan da kuke yi shine yake neman zubar mana da mutunci kuda zakuyi mun kayan dubu ɗari takwas. Ni wallahi ko an kaini dasu sai an canja komai karma ku wahalar da kanku, dan bakuga gidan da Alkasim zai sakani bane. " Ta faɗa tana jan majina saboda kukan da tayi. Kai mata wani bugun taga Mama zatayi tayi saurin jada baya.
"Ai da kin tsaya ki gani marar kunya." Da gudu Tauheedah tabar ɗakin zuciyarta na mugun ta fasa. Shikenan Aunty Hauwa ta bata komai, dama batazo ba, tasan idan ta lallaɓa Mama ta mata daɗin baki zata yadda su saka tiles a tsakar gidansu a kuma fashe ƙofar shigowa ayi masu ɗan gate koda wanda ba a buɗewa ne. Aunty Hauwa bata jima ba ta dawo da ɗan sahu ta shigo da yara suka riqa ɗibar kayan suna fita dasu har suka kwashe ta yiwa mama sallama tace sai dai sunyi waya da haka suka yi sallama. Kwana biyu haka ta riqa cin magani bata kula kowa a gidan sai ta shige ɗaki su sha hirar soyayyarsu da Alkasim dinta ta waya. Ta ɓangaren Alkasim suma danginsa sun fara shirya masa kayan lefe nagani na faɗa wanda bai masa ba sai yace wannan bazai yiwa Tauheedah kyau ba a canja dai ya zabi wanda ya san zaiwa Tauheedansa kyau. Kullum cikin faɗa su ke da Zahra akan lefensa, sai tagama wahala ta zabi abu ta kawo gida dan a saka cikin kayan sai ya daka tsalle yace bai yi mai ba. Zahra har zuciya tayi tace zata mayar masa da kuɗinsa yaje duk inda yake so ya haɗo kayansa. Dakyar Yaah Hajja da mami suka shiga tsakanin su. Bayan kuɗin da mami ta turawa Zahra Galadima, sai da ya kara tura wasu 5m. a kasa yace komai da komai yake so a saka. Ta ɓangare ɗaya kuma ya mayar da hankali kan gyaran gidansa daman yana da gidaje zabar wanda duk yafi kyau da haɗuwa yayi aka canja fentin gidan. order ya saka ta funitures ɗin da za'a zuba a ƙasar Turkish masu tsadar gaske. Nan Yayun sa suka bashi shawara ya saka a part ɗinsa kawai saboda idan yace ko'ina zai saka kaya
Idan iyayen amarya sukazo ina zasu zuba nasu? Irin wannan ai bazasuji daɗi ba zasu ga an raina arzikin su tunda ya riga ya faɗawa su mami daman su Tauheedah ba karfi garesu ba, ya sanar da su mahaifin su ma ya rasu marayu ne. Duk da haka ya saka harda na ɓangaren Tauheedah idan kayan sun iso zai aje su a wani gidan idan da yiyuwar acanja na Tauheedah sai ya canja idan tana buƙatar haka. A ɓangaren shirye-shiryen biki tun acan Auta Najma Galadima ta turo masa parties har guda biyar da za'ayi ta WhatsApp, tun acan ya rubuta mata batada hankali shi waleema kawai za'ayi ai yasha faɗa musu shi bikinsa babu bidi'a. Nan take Najma Galadima ta kirasa vedio call. Yadda ta kumbura fuska sai ta baiwa Alkasim Galadima dariya. Fashewa kuwa yayi da daria dan ya kasa riqe dariyar.
"Hamma ka tsayar da wannan dariyar ka tsaya muyi magana. Wai me kake nufi ne? kana son naji kunya ne? Duk yadda na riqa faɗin bikin Yayana a wurin friends ɗina, wasu ma ba garin mu ɗaya ba amman zasu zo."
"Ina ganin mun gama wannan maganar naji? karki saka mun ciwon kai da fitinarki."
"Toh nidai za'ayi ka shirya kawai Idan kai bazaka yi ba mu zamu yi da amarya shikenan daman shine gudunmuwa na aini bance ka saka da sisinka ba." Sai kawai ta katse video call ɗin. Bin wayar yayi da kallo yana girgiza kai yana kara maimaita party har guda biyar aransa. Da gaske Najma batada hankali. Da yaje gidan Yaah Hajja ta faɗa masa sunyi waya da Najma ta kawo qararsa.
"Ki kyale Naj kawai Yaa Hajja, so take qarfin mutum ya qare duka kafin ya fara amarci." Dariya kurum Yaah Hajja tayi suka shiga tattaunawa akan tafiya kai lefen da za'a yi a jibi.

####

Itama gefen Tauheedah suna ta shirye-shirye sai rawar qafa take za'a kawo mata lefe duk da a gefe ɗaya wata irin fargaba ce takeji ta danne mata zuciya, tana tsoran idan kuma ƴan kawo lefe suka zo suka ga gidansu fa? tasan sha'ani na mata ba'a rabuwa da kanunun maganganu. A kwanakin nan tunani kawai takeyi Mama da Aunty Hauwa sun cuceta da yanzu an samu anyi wa gidan kwaskwarima babu mai gane suna cikin bakin talauci. Idan ta kalli yadda gidansu yake sai taji zuciyarta ta matse wuri ɗaya, ta kasa samun natsuwa musamman yadda Kasim ya dame ta da zancen Yayun sa mata suna so su ganta wannan qaron dasu za'a kawo lefen. Wani irin shiru-shuru ta zama a kwanakin nan tamkar ba Tauheeda ba.
"Daman yau zaki dawo shine baki faɗa mun ba." Zahra ta faɗa tana kallon ƙanwar mijinta Ikraam dake bautar kasarta a garin Kaduna. Ko jiya munyi waya amman baki faɗa mun zaki dawo ba." Murmushi Ikraam ɗin tayi, ita kanta zuciyarta ba'a nutse take ba, tahowar gaggawace ta same ta, wata cosin ɗinsu Zahra ƴar gidan Alh. Ibrahim Galadima, watau Yayan mahaifinsu Alkasim, wuri ɗaya suke bautar ƙasa da zahra har suka zama aminai. Suna chat take tambayar yaushe zata dawo?Ta faɗa mata sai takai wani satin, anan ne Halimar ke faɗa mata ya kamata ta dawo an kusa shan biki. Da mamaki take tambayarta bikin waye za'a yi? shine take faɗa mata Hamma Alkasim ne. Ikraam na kwance lokacin sai gata zaune ɗauke da wani irin shock da ya nuna tun daga kan fuskarta yake. Cikin rawar murya Ikraam ke haɗe sunan Alkasim tana kara maimaitawa tamkar mai bitar karatu. Wata irin dariya ta fashe da ita wacce babu farin ciki ko kankani acikin ta take cewa.
"Ki daina yi mun irin wannan wasan Haleema kinsan soyayyar da nake yiwa Alkasim Galadima saboda shi nazo bautar ƙasa cikin Kaduna."haleema  ta ce mata,
"Ai saboda nasan baki sani ba shi yasa na faɗa miki. Ni na ɗauka ai kin hakura dashi tun daga lokacin da ya faɗa maki babu soyayya a gabansa." Kalaman Haleema Galadima takejin kamar an zuba mata garwashi cikin zuciya, sai kawai ta kashe wayar ba tare da ta yiwa Haleema magana ba........

#Tauheedah
#Love/Romance
#Lovestory2025
#Asmy b Aliyu.
#08086207765
#paid book

Free pages sun kare ga mai bukatar cigabasa Zaiyi sai payment 1k ta wannan asusun *0004157137 Jaiz bank Asma'u Buhari Aliyu* shaidar biya ta wa'yannan lambobin...
#08086207764
#07065283730
Chapter 16 · 0% Book details