Sashe 1
Tauheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
[6/14, 3:33 PM] Asmy B Aliyu 🥰: *TAUHEEDAH*
*PAID BOOK*
Asmy b Aliyu
1...
Ɗaga labulen ɗakin akayi, lokaci ɗaya tabi ƙofar da kallo ganin yadda hasken rana ke shigowa ta cikin ɗakin yana haska kyakkyawar fuskarta. Ɗan ɓata rai tayi ganin mahaifiyarta tsaye a bakin ƙofar duk a tunaninta kannenta ne kasancewar yau assabar babu makaranta boko sai islamiyya. Yanzu kam kusan sha biyu na rana ta riga da tasan sun dawo. Ji tayi mahaifiyar ta tace. "Sai ki taso kiyi mun wanke-wanke tunda nagama girkin wanda da na biye miki ba ɗorawa zaki yi ba." Ɗan turo baki tayi tana qara haɗe ran da ya ƙarawa fuskarta kyau tamkar ita tayi kanta. "Na riga dana faɗa miki Mama kaina na ciwo tun safe, nasan waheeda ta dawo dan Allah kibata tayi." Ta faɗa tana komawa ta kwanta. Kaɗa kai kurum mama tayi dan tama san wahalar da bakinta kurum zatayi indai akan Tauheeda ne ko zata kasheta cikin gidan nan bazata yi mata wanke-wanken nan ba. Idan ma ta sakata bazatayi ba sai dai ta nemo almajirai a waje su wanke ta biya su. Duk acikin yaranta mata 3 Tauheeda ita kaɗai ce batason aiki tana da wani irin son jiki na ban mamaki, kuma kaf itace babba a cikin su, sauran kannenta ba kamarta suke ba. Tauheeda irin matan nan ne masu masifar son jiki wanda ko motsawa basa son yi, kawai tayi wanka ta fita ganin gari idan ta dawo taci abinci tabi lafiyar katifa shi kawai ta iya sai kuma a haye yanar gizo ana kallon Tiktok. Wani irin nishaɗi takeji a duk lokacin da taci karo da wani bikin na masu kuɗi a yanar gizo, har hasaso kanta takeyi a matsayin su. "Tauheedah Allah ya cika miki burinki ki auri ɗanɗan mai kuɗi kamar yadda kike da wannan burin a kullum." Kullum addu'ar da mahaifiyarta ke bin ta dashi kenan, daga uwar har ya'r basu taɓa rokon mai albarka ba sudai kurum su samu mai shegen kuɗi suna ganin in hakan ta kasance jin daɗin su yazo. Tana juya ido zata amsawa uwar da amin kafin ta ɗora da faɗin "Kema Mama kinsan mai kuɗin zan aura dan nasan ina da kyau ina da dirin da maza dole su kalleni.
Kawai dai lokacin auren ne bai yi ba." Bata ba ta amsar maganar ba, kawai tace da ita. "Da kun gama cin abinci Waheeda kiyi wanke-wanke kinga Tauheeda tun safe take kwance batada lafia." Wacce aka kira da Waheeda ta wani irin yamutsa fuska lokaci ɗaya,tana bin Mamansu da kallo kafin ta ɗora da faɗin. "Ko jiya fa ni nayi wanke-wanke
Mama ita tafi kowa ne da kullum yazo kanta sai ta samu karyar da tayi kawai dan kartayi.
Ni bazanyi ba gaskiyya da nagama fita zanyi zanje gidansu Aisha na qarbo littafina." A hasale Maman ta ɗaga hannu tana shirin kai mata duka. Babu shiri Waheedan taja da baya tana turo bakin ta. "Ni dai bazan yi ba, kinfi sonta damu bayan duka mu Ƴaƴanki ne kawai dan tana kawo miki kuɗin samarinta sai kiyi kamar kina tsoronta." Wannan karon da tsananin fusata Maman tayo kan Waheeda da ta miqe a guje da sauran kwanon abincinta a hannu ta shige ɗaki tana rufo ƙofar, tana jin irin zagin da mahaifiyarta keyi mata ta wani juya ido ta zauna ta cigaba da cin abincinta tana yatsina fuska. Ita kam ta matsu tayi candy ta fara tara samari kamar yadda Yaya Tauheeda keyi, tana son makaranta tana matuqar kaunar karatu shi yasa bata kula kowa. Haushin yadda mahaifiyarsu ke fifitasu akan Yayarsu yasa ta fara tunanin kula samari itama idan tana ɗan shigowa da leda mahaifiyarsu ai bazata riqa jibga mata ayukkan gidan ba.