← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kulasa bata yiba,zata wuce ta gefe kawai ya sha gabanta tareda Mika mata key “ga kinnan ki kaimun abincin Rana dakina,SULTANA kam kallon baka da hankali take masa,magana ya farayi cikin serious yace” abinci zaki Kai mun fah ,Kona taba aikenki dakinane yimun wani abun “ni bazan kai ba kabani hanyan na wuce tun Muna mutunta juna “ please kikai mun daki ni’ina garden da abokina ,idan muka gama abunda mukeyi zai ci abincin ne.

“ toh bani key na kai dan kana batamun lokaci ne “mika mata key yayi tare da juyawa ya nufi garden, SULTANA kam komawa tayi kitche ta zuba abinci a plate ya daura akan Trey ,ta dakko ruwan sanyi da Coca Cola a fridge ya daura akan tare da cup agefen.

Tana fita daga part din ya wuce boys quaters din, shiga tayi falone mai dan girma daya kawatu da furniture brown sai kofa biyu Wanda daya zai sadaka da dakin jabir daya kuma
Na khalifa,gefen dama shine na khalifa na hagu kuma na jabir na hagun ta nufa tare da sa ki ta bude kofan.

Tana shiga warin sugari da na shisha ya bugesa alamun ba’a dade da shaba sai da ta toshe hancinta dukda akwai niqab a fuskanta amma ta Tosha hancı ta kafun ta karasa cikin dakin ,dakin Duk a warga je kaman ba mutum ne yake rayuwa a ciki ba.

Komai a war gaje towel a kasa kayan da ya cire ma akasa ya wullar ga uban kwanuka a cikin dakin ya kasa fitar wa sai tashi suke yi,a jiye Trey tayi akan table din dake ajiye a tsakinyan dakin ,”kaman daga sama tayi an murda key a kofan dakin ,cikin sauri ta juyo ta duba ,jabir ne tsaye daga shi sai boxers ,tun a falo ya cire kayan ,dariya yayi” yau hakata ta cimma ruwa ,saina dandana zumanki na kauda kwadayina akanki,kullum kina zuwa Ina ganin kayan alatu a jikin ki amma ba daman tabawa ,Toh yaude ga dama ta samu sai yanda nayi dake,ya karasa maganan tare da yin dariya irin na yau kashinki ya bushe.

Wallahi idan tace bata tsorata ba karya takeyi amma sai ta dake tace” saboda bakada hankali jahilci yayi maka katutu aka kaida wancan kanwar taka ,zaka wani zo ka yaudareni da cewa na kawo maka abinci .

“Bukatar kadai insha Allah,Allah bazai Baka iko ba,wuce wa tayi ta nufi hanyan fita taji ya janyo hijabinta ya cire mata dan karfin mace dana miji ba daya ba .

Kokawa suka farayi ,har yayi nasar wullata kan gado,yana kokarin hayewa kanta b……

( koya zata kaya tsakanin jabir da sultana sai mun hadu ranan monday

2024/2024🔥

Written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE_*❤
️( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

🌎 Destiny,love ❤️‍🔥& Romance 💋

Written by AMID ✍️

2024/2025🔥

Bismillah Rahmani Raheem

Paid book ne

page 📃 12

Kokawa suka farayi,har yayi nasaran wullata kan gado ,yana kokarin haye wa kanta ,batayi wata wata ba ta dauki lamp dake kan bedside drawer ta kwada masa da’iya karfin da Allah ya bata.

Ai kuwa tana buga masa ya saki ihu yana tangal tangal jini har ya wake masa fuska ,sai ya fadi kasa sumamme.

Cikin sauri ta fita daga dakin da gudu tana sharar kwalla” zuciyanta zafi yake mata abun sun hadu sun mata yawa ,gidan ba dadi wajen aikin ma ba dadi ,har ta fito tsakar gidan bata sani ba,abunda yafi bata ma rai ma”kawai dan nanne wajan samun abincin ta zai yi kokarin ganin ya keta mata haddi”ji tayi ta buge mutum cikin sauri ta daga idonta danganin waje ne ,Ajiyar zuciya tayi ganin Aneesa ce “kiyi hakuri ban ganki bane ta fada tare da cigaba da tafiya.

Kamo hanun ta Aneesa tayi dan Allah kiyi hakuri ki dan biyoni ,gyada kai kawai sultana tayi,komawa sukayi falon ba kowa,wuce wa tayi da ita dakinta ,zama tayi a gefen gadon ,daga niqab din Aneesa tayi ta tsaya tana ganin kyakyawan fuskan SULTANA da yayi jajir saboda kukan da tayi.

Dafata Aneesa tayi “kiyi hakuri Duk da bansan meya faru ba naga kina kuka,kar kice na miki shishigi amma harga Allah amma harga banason abunda yan gidan nan suke miki ,kawai dai banida yanda zanyi ne,gashi baki bani daman da zan Ina miki magana ba ,ni kuma banason abunda zai kawo sabani a tsakanin mu .

Cikin sanyi murya mai hade sanyi jiki tace”babu komai kawai dai ina tunanin abunda ya farune kafun nabar gida ,idan natuna nakan kukan yazo mun ba tare da na shirya ba.

Cikin tausayawa Aneesa tace “kiyi hakuri ,komai dan hakuri ,wata rana zakici moriyan sa.

Jinjina kai SULTANA tayi cikin gamsuwa da maganan ta ce “insha Allah “,dan Allah SULTANA karki ce na dameki “can we become friends with you please,cikin murmushi daya subuce wa SULTANA tace “why not “dan Koba komai zata na samun sauki ta wajanta.

Cikin jindadi aneesa tace yau dai buri na yacika mun zama kawaye,murmushi kawai SULTANA tayi batare da tace komai ba, tana mamakin yanda taga Aneesa take sonta abun ta faranta mata rai .

Mikewa SULTANA tayi tace “nagode da kulawan ki a gareni ,zan tafi gida sai gobe “mikewa Aneesa ma tayi”toh bari na raka ki ,sultana tace ai da kin barshi ma basai ki wahalar da kanki ba”a’a ai ninace zan rakaki muje kawai,fitowa sukayi daga dakin,falon kasa ba kowa sai masu aiki dake goge goge.

Da kata tayi har bakin get din,sukayi sallama ta koma gida.

SULTANA bayan ta koma gida time ya kure na islamiya dan yanzu pass 3 kuma 3 suke shiga class .tana koma wa wanka tayi kawai ta kwanta dan Kanta ciwo yake mata sosai.

________________________________________________✍️

USA 🇺🇸
Harvard university,

Junaid ne zaune a cafeteria gama cin abincin sa kenan ya ga body guards Nashi dake kula da duk wani motsinsa koda yaushe suka shigo cafeteria.

Fuskansu duk da face marks ,ba lallai a iya gane suba “umarni daga “boss lion” cewa mu maida ka gida yanason ganin ka.

Cikin mamakin daya gagara boyuwa a fukansa yace”shi “BOSS LION “din ne yace muku kudauko ni ban gama lectures ina ba”how can that be possible,”brother amma dai kasan bama iya tsallake umarnin “boss lion “ko, daya daga cikinsu ya fada cikin rarrashi,dan in basu rarashe saba akwai matsala.

Maganan zuci junaid yake yi” wata kila wani abun yakeson ya fada mada masa” kai No “boss lion” bazai sa a dauko ni saboda wannan dalilin ba,to kodai wani abun ne yasamu ya Ashman ,,tuna hakan yasa hankalinshi ya tashi dan yasan shine bashida cikekken lafiya .

“Ok let’s go,junaid yace yayi gaba suka bisa a baya ,daya daga cikinsu ya bude masa kofa yashiga biyu kuma suka zauna a gaba sai wani motan a bayansu, suna fita yaga sun dauki wani hanya daban da inda zasu je.

Cikin dan bacin rai junaid yace”wannan wani irin haukane zaku wani canja hanya bayan kunsan so nake na ganin a gida dan nasan meke faru wada ya Ashman ,dan shi zuciyanta tafi amminta da wata kila wani abune ya faru dashi .

Tsawa daya daga cikin motan yayi “kai ka shiga hankalinka ,kuma ka iya bakinka,dan kai karamin kwaro ne ,da yayanka zamuyi bada kai ba”so shut up your mouth and keep quiet 🤫 “.

Tunda suka yi mishi tsawa ya gane tabbass ba body guards nashi bane sai yanzu daya lura da kyau ya gane dan muryansu ma ba daya bane da irin na sojojin can”zuciyansa buga wa yake yi da sauri sauri ,sai kuma wani tunani ya fado masa “cewa duk inda zasu kaishi yasan “boss lion “bazai taba barin wani abu ya samu junior saba,da wannan tunanin yaji qwarin gwiwan yin magana.

“Taya zaku sace ni kuma kuce bazan yi magana ba ‘nasan duk inda zaku kaini a fadin duniyan nan sai “boss lion ya nemo ni cikin some minutes idan zai iya bar……., maganan ya tsaya ne saka Makon powder da suka shaka masa a hanci dan sunga alamun shima yaro zubinsa irin na”boss lion” ne basu da tsoro, gashi ance karsu yarda su taba shi.ga samu ga rashi .

(Ni kam nace Hmmmm shima yasan meya takane shiyasa yake fadan abunda yaga dama).

Tunda suka shaka masa powder a hanci,a take ya suma a wajan,daganan bai sake sanin inda Kansa ya ke ba dan yariga da ya suma,kuma suma kanin mutuwa ne.

(Toh fans dina,ina miko sakon gaisuwa gare ku)

SHIN INA ZA’A KAI JUNAID Namu

WAYE kEDA SA HANU WAJA DAUKE JUNAID

SHIN “BOSS LION “ ZAI ZO KUWA KAMAN YANDA JUNAID YAKE TUNANI,DAN KUNSAN DAI BAYA MA KASAR GABA DAYA.

kUNA GANIN JABIR ZAIBAR SULTANA TABUGE SA A BANZA

YA ZA’AYI SULTANA TA HADU DA MAI SANTA

SHIN BOSS LION ZAI RAGE FUSHI DA ZAFIN RAI, DAURE FUSKA
AKWAI WACCE ZATA IYA ZAMA DASHI KUMA BAYA SON GANIN MACE KWATA KWATA

WANI SIRRI NE DAKE BOYE DA BOSS LION BAYA SAN TUNA WA

( Ku biyoni a cikin wannan littafin zaku samu dukkan amsoshin da kuke bu ka ta dan ko kwata ba munyi ba a cikin wannan labarin,soyayya ,cin amana,kiyayya,karku bari abaku labari Ina godiya masoya na)

Wannan littafin na kudi ne 300 ne bayawa game bukatan karanta complete ga wannan account number 7068845514 opay Fatima mala umar zaka iya turo sha idar biya ta wannan number 08161857656 na gode.

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
(. The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

Written by AMID ✍️

2024/2025🔥

Bismillah Rahmani Raheem

Paid book ne

page 📃 13

Bude idanunsa ya farayi a hankali har ya bude su Akan wani dake zaune a kan kujera yayi crossing legs nashi,bakin fata ne ashida haske bakine sosai, ba wani mummuna bane
,Ashekaru bazai wuce 50 ba, amma idan kagansa zakayi tunanin 60 year dan yanada tsufan jiki da wuri.

Ga wasu bakkaken kaya ajinkinsu, baka iya ganin fuskansu sun rufe da bakin kalle ,hanunsu rike da gun manya.
Chapter 9 · 0% Book details