← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe idonta tayi tana shakan daddadan turaren dakesa mutum ko ransa ya baci indai ya shaka to wannan perfume din to tuni hankalinsa zai kwanta ,dan ko Ina na dakin kamshin turarensa yakeyi kaman anan ya fesa.

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️

*_💋SIRRIN DAKE BOYE❤️_*
( The hidden secret 🌹)
Page 27

________________________________________✍️

Kwance take a falo,jikinta sanye da dogon riga yar kanti peach color mai design na roses a jiki kanta sanye da peach veil bakaramin kyau kayan ya mata ba daidai jikinta ,fuskanta ba wani kwaliya tayi ba power,kwalli,dakuma lipsticks,ga gashin tanan yasha gyara , ta gaban kaman wanda ta saka jel ,sai dai muce Tabarakallah Masha Allah,dan Allah yayi halita,junaid ne da kansa ya nuna mata yanda ake amfanin da abubuwan da suka siyo,bayan yayi mata ya jiki,kuma yayi mamaki ganin fuskanta ,ba kumburin dayayi jiya ,fuskanta fess kaman ba jiya tasha mazga ba,dan maganin da tasha ,sha yanzu mafani yanzu.

Zaman dakin ne ya isheta shiyasa ta dawo falo bayan ta gama break fast,bakowa dan duk kowa ya kama harkan gabansa, junaid ya tafi school amma tasan yanzu haka ya kusan dawowa shiyake ibe mata kewa,mikewa tayi da sauri tuno da maganin da ya bata,tabass kaman bata ganshi,a zuciyanta tace”tab yau na shiga uku agun mugun mutumin nan gwanda na shi naje naduba tukafu ya karyani a gidan nan,da gudu ta nufi elevator ta dan hawa na hudu ,sai kuwa ya budu,kawai shege wa tayi da sauri ,hankalinta ma baya jikinta jikawai tayi ta bugu da mutum.

Tariga da tasan wata buge ,ai take jikinta ya fara rawa ganin yanda ta bugesa,kuma ta buge wayansa,a kasa ,dagowa tayi ta kallesa kaman munafuka,saikuma taga ba’ita yake kallo ba wayan data buge masa yake kallo,dan jira yakeyi yaga zata mika masa kokuwa ciga da ganinsa zatayi”hanunta rawa yake yi kaman a jona mata igiyan lantarki ,mika masa wayan tayi yiyayi kaman baisan tanayi ba ,sai kuma can ya dago idansa ya kali yawan ,ba abunda ya sameta dan ba normal waya bace irinta kowa ,musaman ya bada a company aka masa ,ba wanda yake rike irinta,kuma shi kadai zai iya sarrafata.

Hanuntan yabi da kallo ganin yanda suke kerma ga kanta a sunkuye sai ruwan hawaye takeyi babu kakkaugawa,karban wayansa yayi a zuciyansa ya”ahh yarinya dakin bar kukannan kin tanada sa a inda zaifi miki amfani dan wallahi babu abunda zai hana yau bai hukuntata ba,shifa wani lokaci har mamamakin tsoronta yakeyi,mutum abu kadan tsorata kam farar kura,sake tamke fuskansa yayi sosai ,yanufi hanyan fita tare da cewa “ki biyoni,iya abunda ya iya fada kenan,jin hakan ne yasa sultana sake fashe wa da kuka dan wallahi kana ganin sa kasan ba wasa a maganan nan ubanta zaici.

Sum sum tabi bayansa ta koma main falon kan wani hadaden kujera ya zauna da ba wanda ya isa yazauna idan bashi ba yayi crossing na legs nashi ko ina fess fess a gyare sai kamshi yakeyi,”acan kasan cafet ta yi Neil down,shiru kusan 10 minute bai ce da ita komai ba ,sai daya bushe iska dan kanshi kafun kafun yace” up and down zakiya babu adadi, harsai idan nice nace ya isa idan kika kuskura kika tsaya zangani,a duk inda nake,so warn your self,one single mistake…..I will kill the hell out of you, so start right now”da sauri ta mike ta fara yin,guda biyar tayi sai da taji kafanta sun fara rikewa dan ba irin wannan wahalan ta saba ba,ta cikin ye taji haushi kare a bayan ta.

Nandanan jikin ta ya fara rawa fiye da nada dan wallahi ba karamin tsoran kare takeyi ba ,ganin wani zudumeme kare tayi irina turawa katı dashi ga gashi sosai a jikinsa yanda kasan karen brolers haka yake,irin ne wayanda akayi musu training sosai ,ba abunda zaka ce su musu baza suyi ba,wajan boss lion yaje ya fada jikinsa yanata tsale alamun yaji dadin haduwa da boss lion dan da kullum suna tare wani lokacin ma tare suke kwana a daki,danshi Rainon boss lion ne,saukar shiyayi daga jikinsa yace” lucky kakula kasa ka yarda ta huta kokadan,idan ta tsaya kuma just bite her,understand,jijiga jikinsa yayi alamun ya gane tare dayin haushi,ganin hakan ne yasa boss lion ficewa daga falon yabar sultana da lucky tare abunsu.

Sultana kam tun da taga lucky ji duniyan gaba daya bayayi mata dadi ,numfashi ma dakyar take iya fitar wa dan ba karamin tsorata tayi ba jikinta kaman a tada jen sai rawa yakeyi ,cigaba dayi tayi dan wallahi tasan idan batayi bama zai sanine dan tasan gidanshi ne,yanada iko akan komai,idan batabi bama ita zata sha wiya,Lu koma dayake shima dan iskane ne sai ya wani zauna a waje daya yanata kallonta,duk dadai sa’an ta daya bai matso inda take ba ,shiyasa ta iya cigaba dayi har zuwa lokacin da boss lion zai ce ya’isa.

______________________________________________🥶
AFTER 40 MINUTES 🥹

Tun tana iyayi har abun ya gagara ,numfashita yana bara zanan daukewa,cinyanta yayi tsamin bala’i ,har ta fara dana sanin zuwa gidan,dan idai haka akeyi kullum to bada ita za’ayi ba,numfashintane ya dauke dipppp,jikinta ya saki,ya fadi akan carpet din,kafunta fadi wani abun al’ajabi sai ga lucky ya je ya tsaya a wajan ,cikin da bara irin na wannan Karen ya daga hanayensa sa sama wajan tareta dan karta fadi direct zataji ciwo,faduwa tayi a jikinsa kafun ya kwanta da jikinsa ya sauketa a hankali,dan irinsu lucky kawai ka gansu ka barsu dan ba karamin horo aka basu ba.

Zagaye ya cigaba dayi a wajan ,suna haka saiga junaid ya shigo falon bakinsa dauke da sallama ,shiga yayi kwata kwata hankalinsa baikai kansu sultana ba yana wani waje ,har ya kusa isa jiki elevator,kaman da sama yaga lucky a gabansa ,Allah idan yace bai tsorata ba karya yake kawai dai ya mazge ne ,ganin lucky ne ya sashi Jan tsakin,ya hayayyako masa”kai wallahi lucky anyi dan iska ,wato ka dawo dole kazo mun oyoyo,Toh bari kaji kamun haukan anan kagani jikin ka ya gaya maka.

Haushi lucky yayi masa yana kokarin nuna masa inda sultana take a kwance amma Ina bai gane ba,haya juya zai tafi,aikuwa yaja rigan sanyin dake jikin junaid ,yana haushi ya janyosa inda sultana take,ai kuwa sai idonsa ya kyallara masa inda sultana take a kwance kamar matacciya,ai baisan lokacin da yayi wufff ya isa inda ya gata ba,ganin yanda idanunta suka kumbura saboda kukan da tasha ,wani irin tausayin sultana ne ya kara kamashi,da baisan lokacin kuka ya kubce masa ba dan shikam ya gaji da ganin yanda yaya boss yake wahalar da baiwar Allah nan .

Idan yasa bazai barta tayi jinya cikin kwanciyan hakaliba ai da ya nuna cewa shi bai yarda da zamanta anan inba.

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️

*_💋SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
( The hidden secret 🌹)
Page 28

_______________________________________________🙏

Daukanta yayi ya ajiyeta akan kujera,dakansa yawuce cikin dan dauko ruwa,yana zuwa ya yayyafa mata”huuuuummmmm taja ajiyar zuciya ,tana fitar fa numfashi a hankali ahankali,sai kuma ya fara hawaye yana gagaro ta gefen idonta,ganin ta fara hawaye ne yasa junaid yayi sauri goge mata danshi tundazu ya gama nashi kukan.

Tashi take kokarin yi danta zauna amma ina kafafunta ciwo suke mata ,ganin tanason mikewa wane yasa ya taimaka mata ta zauna dakyar,cikin muryan kuka tace “yaya junaid dan Allah inaso na koma gida ne dukda dai canma ba Jin dadin zama nakeyi ba,amma yafi zaman gidanan nesa ba kusa ba,dan indai na cigaba da zama a gidanan watarana saidai kuzo ku dauki gawana,,dan wallahi bazan BOYE maka ba yayaynka mun..gu..ne,ta fada a rarrabe saboda kukan dayaci karfinta ,bu buga bayanta yakeyi alaman rarrashi.

Kafun yada go fuskansu suna fuskanta juna ,cikin rarrashi yace “meyasa kikeso ki tafi bayan bashi yace ki tafi ba,dan shifa yaya boss bazaka ce ke zaki yanke wa kanki hukunci ba,dan bazaki zauna masa a gida ba kuma kice lokaci daya zaki tafi ba,”kuma kodan ni bazaki zauna a gidan ba ,kinga fa kekadai ce kanwata dake dashi,dan Allah ki daina maganan zaki tafi kibar ni,kinji ko”eh gyada kai tayi dan ,itama tanason zama ,Toh amma boss lion yanada wiyan sha’ani.

Yanzu ki fadamun,labarin ki,dan iso insan daga inda kika fito dahar zamancan dinma bai miki dadi ba”girgiza kai tayi tace”babu fah ya junaid ,ni banmasan na fada ba,”ai dole kice mun bakisan ma kifada ba”please sis sultee ki fadamun mun “Kodai baki yarda dani bane”a’a ya junaid na yarda dakai mana zan fada maka amma please karka fadawa kowa kaji “Shikkenan bazan fadawa kowa ba dagani sai ke sai kuma Allah.

Gyada kai tayi ta fara bashi labarin yanda ta zauna Insha tana muzguna mata tare da yayanta ga babanta baya iyayin komai ,komai zasu mata bazai ce komai ba har rayuwansa da tayi a gidansu jabir ta bashi labari,harzuwa ana gobe aurenta da dare akazo aka sace,har gidan karuwai da aka kaita,zuwa lokacin da ta gudu ya bugeta,,share hawayen daya zubo mata tayi”tace yaya junaid kaji tarihin rayuwata ,karka gayawa kowa,ya zama sirri tsakanina dakai,gyada kai yayi idanunsa sunyi ja jin tarihin rayuwanta.

Shikkenan dai yanzu tashi muje kiyi wanka,ki gasa kafanan naki da ruwan zafi kozaki samu yadauna miki ciwo”tashi tayi dakyar dan kafan harya fara yin tsami,riketa yayi ,shiko a jikinsa duk da ya kasance musulmi,amma rainon turawa,kwata kwata basusan wani abushi kunya ba,”dakyar take tafiya gar ya kaita daki ,ya fito ya barta dan tayi wanka ta shirya,yana fita daga daki tashiga toilet ta hada ruwa mai zafi tashiga ciki ,ta mammatsa kafafunta dan har su harsun yi tsami ,tanayi tana sharar kwalla,dan ba karamin zafi take ji ba.
Chapter 20 · 0% Book details