← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After 30 minutes sai ga Ashman ya dawo tare da wani soja a bayansa hanunsa riqe da ledodi irin na boutique dinnan,yana ajiyewa ya fita ,shima Ashman din ,ganin ta juya baya,hakan yasa baiga fuskanta ba,shima ya fita daga dakin.

******

Boss lion kwance yake akan L-shape chair dake dakinsa idonsa a rufe kaman mai bacci amma baccin yakeyi ba,takaici kawai ya isheshi,dan wannan ihuuun da sultana tayi danshi a rayuwansa ya tsani hayaniya kwata kwata,ihuuu nata kuwa har cikin kokon kanta taji shi,shifa wallahi harya fara nadaman barinta da yayi ta zauna masa a gida.

Tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka,bayan ya fito ta wuce dressing room ya shirya cikin pajamas nevy blue masu kyau da tsada,kwanciya yayi dan shi bai cika samun lokaci yana yin bacci ba dan wani lokacin ma till down yake yi.

Karan bude kofan dakinsa yaji anyi,amma saboda miskilanci ko kadan bai nuna alamun yasan da mutum a dakin ba,danshi komin kankantan motsi idan anyi yanaji,dan kwata kwata bashi da nauyi bacci,inashi ina dogon bacci,suda da suke zuwa yaki,any time ana iya kawo musu hari.

Junaid tunda ya shigo yake dari dari dan yansa yayi lafi amma dole ya bada hakuri,cikin dauriya ya haye kan gadon boss lion ,ya rungumesa ta baya,yace”please yaya kayi hakuri,wallahi bada sanina na bugeta ba,kawai ganinta nayi a gabana,kuma kasan bawa baya taba kaucewa kaddararsa,duk inda kake sai kaje ka same ta,please yaya am so sorry it’s me your junior,please don’t be angry with,bazan kara fita ban fada maka ba,shima banyi tunanin zaka dawo ka samu bandawo ba,please and please my yaya .

Boss lion yana jinsa amma ko uffan bai ce masa ba yanda kasan ba’ayi ruwansa a dakin ba,tsabar miskilanci.

Ganin bai kulasa bane yasa ya fashe da kuka harda shesheka,dan yasan idan ba kukan ya masa ba dakyar ya kulasa,dan kwata kwata bayasan ganin kukan su.

Kukan da yake yi ne ya karyawa boss lion zuciya dan bayaso ganin kukan yan uwansa,wannan Alkawari ya daukawa kasa nace wa bazai bari suyi kukan maraici ba.

Jawo sa yayi jikisa yana bubuga bayansa alamun rarrashi ,duk da haka bai ce dashi komai ba,nan take junaid yayi shiru a jikin boss lion sai shakan dadda dan turaren jikin boss lion yake kamshi sai tashi yakeyi,tuni ya soma ajiyan zuciya akai akai ,Chan bayan 5mins dikinsa ya saki ,alamun bacci ne ya daukesa.

Tsayawa yayi yana kallon kyakyawan fuskan junaid dake sauke numfashi a hankali a hankali,abubuwa dayawa suna masa yawo a kai,janyo musu blanket din yayi ya rufe su , tare da yi addu’a ya fasha fa musu gaba daya,shima bai jima ba bacci ya dauke sa .

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

page 📃 23

***

Sultana tun bayan bari doctor da ashma ,ba wanda ya sake dawowa dakin,after 3 hours ta tashi ,bata jin wani hajijiya,sai dan ciwon kan da ba’a rasa ba,shima saboda buğulan da kanta yayi ne.

Kasa bude idonta tayi dan ji takeyi kaman an like matasu da gum,haka dai doctor yashigo ,ganin hanunta yana motsi ne ya tabbarar masa da ta tashi ,amma tasan bazata ita bude idonta ba,dan haka kawai ya koma yasa gobe insha Allah,idonta zai bude.

Sultana kam jin ta kasa bude idonta ne ,yasa ta fara tunanin ko dai ta makance ne,a haka har wani baccin ya sake dauketa ,tsakar dare.

WASHE GARI😌

A hankali ya bude idonta ,abunda ya fara dawomata shine Toh dama ba makan cewa rayi bane.

Tashi tayi ta zauna tana kare sa dakin kallo ,kallon dakin takeyi,da mamaki dan tasan dai ba a nan dazu ta gantaba,Tuna a bandaki take ne yasa tayi saurin taba fuskanta dan taji shin har yanzu da jinine ko kuma A’a.

Jin abu komai a fuskanta ne yasa ta sauke ajiyar zuciya,tana zaune sai ga doctor ya shigo ,ya isa inda take yace”how are you and how is your body,a hankali muryan marasa lafiya tace,Alhamdulillah”I hope you are feeling better?”gyada masa kai tayi kawai.

Mika mata ledan da Ashman ya kawo mata yayi yace”ga kayan nan ki shiga kiyi wanka,ko zakiji dadi jikin ki”ok tace,daganan bata sake cewa dashi uppan ba.shima fita yay dan ya bata waje ta shirya,yana fita ta soma maganan zuci “ina nake ne yanzu,Allah yasa ba masu cutar wa bane,duk da dai bata ga alamun hakan ba,amma fuskan doctor a tamke yake ,kaman na ogansu dan basa daukan wargi.

(Karku manta duk maganan nan da English suke yi ,dan ita tayi school zu jss 3 ta tsaya )

Tashi tayi ,ta nufi toilet tana tafiya a hankali kaman wace kwai ya fashe a ciki,shiga tayi da ledan a hanunta tana budewa taga ,abayas kala biyar masu shegen tsada da kyau,stones din jiki sai shining suke yi,ga packeds na pants,bra,lotion,perfumes,lipstick , towel,sai takalmi guda biyu daya na yawo a cikin daki daya kuma na kwalliya.

(Karkuyi tunanin Ashman ne ya je yasiyo mata A’a ,saika wani soldier yayi yaje ya siyo,bayan ya siyo ne ya kawo masa,batare da ya duba ba,ya kawo mata cikin dakin)

Wanka tayi,mai kyau ta wanke duk wani datti dake jikin ta ,ta shafa lotion din sannan ta saka su pant,bra, duk da dai duk sun mata kadan da ta fah sultana,Allah ya albarka ce ta da dukiyan fulani ,gasu a tsaye suke churrrr,ga hips hmmm ba’a magana Coca Cola body ,kuke ji,ta daura abayanta akai ,gashinta data wanke ,ta dauki towel din ta tsame ruwan jiki ka fun ta yafa dan kawalin abayan,tayi kyau ta fito a asalin balarabiyar ta ,sai dai muce Tabarakallah Masha Allah,duk da ba tayi kwalliya ba amma fuskanta ba karamin kyau yayi ba kaman ,iya lipsticks kawai ta shafa.

Ta koma kan gado ta kwanta amma ba bacci take yi ba.

________________________________________🥰

Junaid kam tunda sukayi sallan asuba,ya koma dakinsa ,yay wanka a bunsa cikin ,black jeans with white t-shirt sunyi masa kyau ,abunku da ma tashi sai yalki yakeyi,ga gashinsan nan ya sha gyara abunsa.

Fitowa yayi daga part nasu direct clinic ya wuce,dan sunyi magana da Ashman ya fada masa an maidata clinic.

Yana shiga ,sojojin da suke wajan suka nuna masa inda dakin sultanan yake,da sallama a bakinsa ya shigo cikin dakin,yanda taje Dazu haka yashigo ya sameta,kanta hade da jikin gadon ,zama yayi a kujerun dake ,kusa da ita,kuma har lokacin bata dago taga wayene ya shigo ba,dan ita a tunanin ta doctor ne ya sake shigo wa.

Yakai 4minutes ba Wanda yacewa kowa komai,sai can junaid yayi gyaran murya “how are you ,how was your body”sai a lokacin jiyo ta kalli junaid ,batasan lokacin da ta hadiye Yawun dole ba dan ba Karamin kyau ne da junaid ba ,sai dai Masha Allah,kasa magana tayi,ganin ya kasa magana ne yasa yace”kiyi hakuri ,bada sanina na burgeki ba,bansan kina wajan ba da bazan burgeki ba,and Allah ne ya kaddara haka zai faru,kuma bamuda ikon sauyawa.

Ajiyar zuciya ta sauke dan sai lokaci ta gane wayanda suka burgeta ne suka kawota ,inda take yanzu.

“Karka damu ,bakai ya kamata ka bada hakuri ba ,nine yakamta na baka hakuri dan ni nashiga gaban ka da gudu.

Junaid fah tunda ta dago ta kallesa ,ya shagala da kallonta dan sultana badai kyau ba,shifa baiyi tunanin yarinya bace ,dan a tunanin sa ma wata 28 ne dan sai yanzu yaga fuskanta mai kyau.

“It’s ok,then can we be friends,cause your beautiful,omg ,amma fah baki fi yaya boss kyau ba dan shi ,first class ne indai wajan kyau ne,ko kafansa baki kai ba yarinya,ya fada cikin tsokana,jin ya ambaci yaya boss sai da zuciyanta ya tsinke bata san meye saba,wayin cewa tayi.

Murmushi tayi tace”gaskiya baka da wata matsala Kanada kirki sosai,kuma ai kaima ka fini kyau sosai”haba yarinya ai ko makaho yasha fa fuskanki da nawa zai gane waye yafi kyau.

“Meye sunan kanwar tawa?,murmushi tayi mai sanyi tace Sultana,”wow nice name,ni zan ina kiranki da sis sultee,haka yayi miki ko A’a acanja “cikin jin kunya tace hakan ma yayi.
Dariya yayi yace”Toh ni bazaki tambaye sunana ba kenan ya fada cikin shagwaba,me sultana zatayi idan ba dariya ba tace”gaskiya shagwaba tayi maka yawa,Shikkenan meye sunan ka,”sai da kika gama jamun aji tukun zaki tambaye ni,zan fada miki badan halinki ba”my name is junaid”ok me too I will be calling you with yaya junaid,because you my elder brother,is it ok for you”yeah I really appreciate it,kinga nima yanzu nayi kanwa.

Toh yanzu dai ba wannan ba ,ki fada mun idan akwai abunda kike bukata sai na kawo ma my sis sultee ,”wani farrr da ido sultana tayi irin ya fasa mata kanan,ta shagwabe fuska irin na tabararun yaranan ,duk da bata masan ta iya ba tace”yaya junaid yunwa nake ji sosai ,”ohh Allah sarki sis karki damu yanzu zankawo miki abinci kin ji ki bani nanda 5 minutes yanzu zan dawo.

Bai wuce 6 minutes ba sai gashi ya dawo hanunsa dauke da basket 🧺 da abinci a ciki,shida kansa yayi saving nata ,chicken pepper,with potatoes chips,da kuma wani abincin su irin na turawa,masu ruwa ruwa,daura plate din yayi akan bed side drawer,a kwai table a wajan ya ajiye ye mata.

Sultana kam banda kallansa ba abunda take yi,ganin yanda bai Santa ba saisan daga ina take ba amma har yake kiranta da sister nashi,kuma ya kula da ita abun ba karamin farin ciki ya sata ba har idanunta sun ciko da hawaye amma bata bari sun zuboba ta shanye abunta.

Sakko wa tayi tana cin abinci junaid sai tsokanan ta yake yi abun gwanin burgewa,Masha Allah.

2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem
Chapter 17 · 0% Book details