← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fitowa ,sojojin suka fara sara mishi ,daga musu hannu kawai yayi,direct wajan da aka parker motocin nasu yaje ,wannan sojan mai suna john Sara masa yayi hade da bude masa matan ,shiga yayi suka fita daga Gidan straight.

Basu dawo ba sai 8pm na dare suka dawo gidan,kuma har lokacin bai samu ya Karasar ba dan shi har ya sadakar sai yayi sai yayi punishment din’’BOSS LION’’ dan ba’a karya mishi doka.

Ruwa kawai ya watsa yabi lafiyan gado,dan kar ya makara zuwa ,dan zuwa karfe biyar (5am) jirgin ‘’BOSS LION “zai saka ,immediately after fajr prayers,jirginsu zai sauka ,shiyasa yake san ya kwanta da wuri dan ya dauko shi akan time ,idan ba haka ba kuwa ,ransa idan yayi dubu Toh zai baci.

Asuba ta gari mutanen”Ashman”✌️

_____________________________________________*✍️

Abuja

Kiran sallan Asuba ne ,ya tashe sa daga baccin gajiyan da ya dauke sa , ban daki yayi alwala ya fito, masallaci ya tafi, bayan an idar da sallah ya dawo gidan.

Dakisa ya wuce,zama yayi ,yai azkhar da karatun alqur’ani mai girma ,lokacin har Safiya ta farayi,kafun ya rufe qur’an ya kwanta ,yana kwanciya kuwa bacci ya dauke shi.

Shukrah kuwa ,Ammi ce ta tashe ta ,tayi sallah Asuba ,bata koma ba dukda kuwa yau Monday akwai school ,amma bata ra’ayi zuwa school yau ,shiyasa bata tashi ta shirya ba ,baccin Tama takoma.

Sai wajen fast 10 tukun ta tashi,daga bacci,a gurguje ta shiga wanka tafito,atampha me design na leaf,pink and purple ,sanan ta daura dankali,daurin Zara Buhari, tayi kyau ,black beauty skin nata dake ta glowing yana shining.

Falo ta fito,at the same time,shima yaya alameen ya shigo falon, Ina ganin shi bansan time din dana ci wani uwar burki ba,dan wallahi kwata kwata na matan da yadawo gidan.

Shikuwa alameen da mamaki yake kallan ta dan yasan dai yau Monday ne,kuma akwai makaranta, ranshi ba karami baci yayi ba dan yasan wannan laifin Ammi ne ,dan ta ta daure mata gindin zama, amma in Fasu san wata ba ,zasu san wata.

Cikin hade Gira yace ,ke shukrah meya hanaki zuwa makaranta “ammm wallahi ya alameen kaina ne yake mun ciwo shiyasa banje ni ba” ke ni sa’an wasanki ne da zaki fadamun wai kanine yake ciwo shiyasa baki je makaranta ba,”marairaicewa tayi tace ya alameen da gaske nake fah.

Gaga sama yaji murya Ammi Tana cewa, wai alameen meyake damunka ne,inadai tace maka bata da lafiya ne,ai zan ce ya kare, ni bansan me yarinyar Nan ta tare maka ba wallahi, ta fada Tana nufah daya daga cikin kujerun falon ta zauna.

Shikuwa alameen dama yasan za’a rina,dan wannan ba sabon Abu bane a wajenta bai san meyasa ba muddin zata yi fada a. Shukrah indai Tana wajen fah,bai isa mata ba.

Cikin warning ‼️ ya kalla shukrah da haryanzu take kalan sa yace wallahi nan gaba muddin ,kika ki zuwa makaranta haka kawai,wallahi ranki inyayi dubu to zai bace, kinjin ko “kanta ta gyada mishi”cikin fada fada yace, Ina miki magana da baki ,zaki wani dagamun kai ,yanda na miki magana da bakai haka zakimun "

Toh tace, insha allahu hakan bazai kara faru ba"good yace

dukansu suka tafi wajan dining cin abinci.

2024/2025🔥

Written by Amid✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

🌎Destiny,Love ❤️‍🔥& Romance 💋

Written by Amid ✍️

2024/2025🔥

Bismillah Rahmani Raheem

Book 1

Page 📃 5

_____________________________________🌹

USA 🇺🇸

Karfe hudu(4am)ya tashi sallan asuba, alwala ya dauro, kafun ya sauka first floor ,anan ya samu junaid ,uncle İbrahim da uncle tareeq a zaune suna jiranshi ,yana zuwa suka wuce masallacin dake gidan, dansu yau babu wanda yasan yau “BOSS LION “ zai dawo ba.

Suna fitowa daga sallah ,suka shigo cikin gida , cikin sauri “Ashman “ya shiga dakinsa,domin shirya wa ,dan jirginsu ya kusa sauka .

Shaf shaf ya shiga wanka ,bai wuce 10mins ba ya fito dan kar yayi latti,shirya wa yayi cikin kakansa na sojoji ,dan ya farajin karan helicopters 🚁 sunata shawagi, wannan yana nuna musu cewa mai gayya mai aiki ,zai dawo wato “FIELD MARSHAL “ zai dawo kasar .(zakin fama maija da shi sai Allah ).

Fito wa yayi daga daki cikin sassarfa,ya fito main falon , anan ya tarar da junaid dake tsaye yanata zazzare ido alamun ya nuna ya mishi laifi,sauran uncle İbrahim da uncle tareeq suma da suke tsaye dan cikinsu ya dura ruwa .Dan wannan karan helicopters din ,yana nuna fah “FIELD MARSHAL “ nanan ta fe🤪

Bai bi takansu ba ,waje ya wuce ,dan lokacin it already 4:40am ,duk sojojin a shiye suke ,suma cikin kakinsu ,dan suma kana gananin su kasan hankalinsu a tashe yake ,sai dai kawai dake wa irin na sojoji bazaka taba gane waba.

Cikin motocin suka shiga,dan sun iba motoci sukai guda goma sha takwas (18) dan dakko “FIELD MARSHAL “ gudu suke shararawa a hanya,shiyasa suka isah dawuri,dan lokacin time 4:56am , dan sai 5:00 jirginsu “FIELD MARSHAL “ zai sauka.

Fitowa sukayi gaba dayansu,daga cikin motocin , har da “Ash” dake tare da abokin sa farouq,suna tsaye suna magana ,karan saukan jirgi ya karade kunnuwan su,A hankali jirgin ya sauka.

Private jet 🛩️ ce mai shegen kyau da tsada ,a jikin jet din an rubuta , “BOSS LION “a ka rubuta a jikin jet din da manyan harufa masu style,kana ganin jet din kasan ba karamin billions of dollars 💵 aka karshe wajan kera taba, dan ya hadu ne iya haduwa, wai dan ma bamu shiga daga ciki ba.

Bayan yayi landing,baifi da five minute ba ,wasu jiga jiga sojoji ne wa yanda suka amsa sunan su sojoji suka fara dauko wa ,dan sukai su goma sha biyu ,hakanma mai gaiya mai aiki cewa wa yayi shi kai zai je amma Ina ,mutum ne mai muhimmanci d bazasu iya barinsa ya tafi shi kadai ba .

(Bari na leka muku cikin private jet ✈️ din naga meye ne aciki,dan gulma na cina 😂)

Wani saurayi na gani zaune akan kujera masu kyau ,a zaune yake yayi crossing legs nashi ,Baka iya ganin guskan sa dan akwai face marks a fuskan sa da kuma glass no respect,ga shin sa daya sha gyara(black curly hair) ,dan kana ganin yanda gashin yake yalki ,zakasan ba karamin kudi a ke kashewa gashin ba,dan ya sauko har kan fuskan sa,kana ganin sa kaga ingarman namiji , namijin daya amsa sunan sa namiji ,dan wasu matan suna suka tara .

Kansa jingine da jikin kujera,dan idan kagansa zakiyi tunanin bacci yakeyi ,yakai kusan 20mins a haka,kafun ya mike tsaye ,irin mazan nane masu tsayi,dan dogone ba karya dan jikin sa a murmurde yake ,kana ganinsa kasan ya mishi da training,dan wallahi irin wayanan ka kuskura wani Abu ya hadaku Toh sunan ka sorry 😢,

Sanye yake da wane black jeans da t shirt na gucci ,ya daura jacket a jikin Kayan,Kayan sun yi mishi wani shegen kyau,Kyan da idan aka ce kyau Toh ana nufin kyau,dan kayan ya fitar da asalin kyau shi,kana ganinsa kasan bazai wuce ,talatin da biyu (32) ba a duniya.

Tafiya yake yi cikin kasaita,irin na jarumin soja da mututanen da suka jika da hutu,ya zauna a jikin sa Fatan sa sai yalki yake yi ,yanda yake tafiya ma kadai abun kallo ne ,dan tafiya ne irin sojoji masu jini a jika.

Tundaga nesa “ash”da farouq suka hango sa ,su karan kansu sun sani,bakaramin burgesu yake yiba,cikin sanda farouq yabar wajen da “ash”ya koma can gefe ya tsaya.

Sara mishi sojojin suke tayi ,kam zasu yi mishi sujjada tsabar girmamawa,ga yan jarida ma ba’a barsu a baya ba ,dan suma dayawa sukazo,Duk da sunsan ba kulasu zaiyi ba ,hot one shima iya ka cin su dauke sa daga nesa,Duk da har yau acikin 100% baifi 10%ne suka taba ganin fuska sa ba dan koyaushe da face marks a fuskansa.

Ga sojoji ta koina dan ko shugaban kasa albarka dan ba Lallai idan zai samu mutane haka ba .

Kara so wansa kenan wajen motocin,Sara mishi “ash”yayi tare da kame wa , dan nuna ban girma ga yayansa kuma ogansa a wajen aiki.

Yi yayi kaman bai San da halittansa ba awajen,amma sarai yaganshi Jiki da Kai ne kawai.

Direct wajen wata shegiyar mota suka nufa ,mercedes -benz GLE 450 4matic ya nufa , cikin sauri “Ashman “ ya bude masa kofan tare da Sara mishi ya rufe, wuce wa yayi,shima cikin sauri john ya bude masa motan dake bayan na “BOSS LION “ din.

Wani irin gudu suke yi akan hanyan kaman zasu tashi sama,dan har yanzu garin bai gama waye wa ba ,dan bazai wuce 5:45am ba.

_________________________________________________💋

Gombe state
Gabukka

Washe gari Tana tashi sallan Asuba tayi,tan idarwa,tayi Sharada wanke wanke ,kafun ta daura musu dumamen tuwo ,cikin sauri tagama,ta shiga wanka.

Tana fitowa ,ta shiga dakinsu ta shiya cikin material orange color,abunka da farin mutum ta haska kayan,hijab ta dauka ,tasa tukun taje dakin Ina ,Tana tunanin komai zata tarar kuma yau.

Gaishe ta tayi Ina kwana ,wai ke kullum sai an mabaki amsa amma dake ke dakikiya ce kin kasa rike wa .

Ran SULTANA ya baci amma ta shanye dan tasan idan tanına ita zata sha wahala,cikin sanyin murya tace innah abincin “wallahi wannan yariya anyi jara babbiya ,Toh gashi ki dauka kije,Tana dangwarar mata da roban abincin, dauka tayi taje dakinsu tace ,dan ko kwatan koshi bata yi ba ,Tana gamawa ta fito daga gidan .

Tafiyan awa daya da kwata tayi,a hakanma sauri tayi ,Tana zuwa tawuce babban falon gidan, tana bude wa zata shiga ,shikuma zai fita.

Binta yayi da wani mayen kallo irin na tantiran yan iskan nan tare da cewa hey baby yafada yana kokarin Tabata ,saurin kauce wa tayi ,tare da balla masa harara da kyawawan idaonta, cikin masifan da tadade batayi ba tace dallah jabir ka fita a hanyata ,idan kuwa Baka fita a hanya taba zakayi danasani.

Wai Kai kana tunanin kowa dan iska ne irin ka toh wallahi bari kaji Duk iskan cikinka baka kaini ba dan haka ka fita harkanta ,dan nafi karfin ka ,sai gani sai hange tare da mit guda masa baki da harara babu ko dar a zuciyanta .
Chapter 4 · 0% Book details