← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid yana zaune Akan kujera an daure sa da igiya , darıya mutumin yayi tare da cewa kanin boss ya akayi ne, “gabriel since masa igiyan ,wanda aka Kira da Gabriel ne yaje gaban junaid ya fara sunce masa igiyan dake daure a jikin junaid din yayi tare da dauko masa abinci , mai rai da lafiya ya mika wa junaid yace karbi kaci kar ace mun kashe ka da yunwa dan mu bada kai zamuyi game in ba da yayanka zamuyi ,dan haka kaci abincin ka bamai maka komai muddin yayanka yazo amma idan be zoba kaima kasan sauran,yana karasa magana ya bar wajan .

Wanda aka Kira da gabriel kam yana tsaye a dakin yana jiransa, junaid kam kallo daya yayima abincin bai kara yiba dan yanaci,yasan sai an kwantar dashi a asibiti ,koma ya yayi baya ya jinginu da jikin kujeran tare da lumshe idanun sa ,skin nasa har yayi ja .

AFTER SOME HOURS ⏱️

Ganin lokaci ya ja ba “boss lion “ ba alamunsa , yasa Gabriel yace” boss benjamin let just finish him ,dan “boss lion ba zuwa zai yi ba ,kaga wanda mu kashe kanin nasa kowa ma ya huta,dan ba karamin son kaninsu sukeyi ba duk da dai har yau bansan ko sune logon saba ko sabanin hakan, idan yaso sai mu tura masa da gawan as a surprise ya fada tare da kwashe wa da dariyan mugunta .

Wanda aka Kira da Benjamin yayi dariya tare da cewa” gaskiya Gabriel kanka yana ja shiyasa kaga nafi mu’a mala dakai fiye da kowa ,kaga tunda bai zuba kawai mu tura masa death body of his brother,kaga ko banza munci riba ba zamuyi biyu babu ba ,ba tsuntsu basu ga tarke

Junaid kam ya girgiza dajin cewa zasu kashe shi ,dan duk mai rai bazai so ya mutu ba, amma duk da haka bai sare ba ,ya nata addu’an Neman Dauki daga wajen ubangijin sammai da kassai.

Benjamin in ne da Kansa ya dauki gun tare da yin huking na gun nasa, ya matso kusa da junaid yace” junaid or what they call u , yau zaka wuce barzaku,dan yayanka ya gagara zuwa karbanka dan haka kashe ka zamuyi .

Daganan ya kai gun in kan junaid da niyar harbinsa.

Yayinda junaid yake salati dan ya sadakar mutuwa zaiyi tare da rufe idansa gam gam yana jiran saukan bullet.

Benjamin yana niyan harbisa kawai sukaji ruwan bullet ta ko Ina a jikinsu dan yan ta’addan sunkai kusan su 100 zagaye da wajan ,within 10minute suka kashe kowa da kowa saura kawai Benjamin,Gabriel da wani dan uwansu daya suka rage basu kashe ba.

“Benjamin dake tsaye ya rasa inda zai saka ransa sai zufa yake hadawa kaman yanzu ya fito daga wanka ,dan jikinsa har karkarwa yake yi tsaban tsoro dan fah shi yasan ba komai bane dama kawai burgane yake damun sa da hassada yasa shi dauke junaid in,ji yake yi dazai samu gun daya harbe kansa dan wallahi da punishment in “boss lion” wanda ka kashe kanka kawai ka huta dan bayayin da sauki bare shi da yayi yunkurin kashe masa Kanin sa hmmm.

A hankali yake takunsa irin na ingarman namiji mai ji da kyau,kudi,illimi,wajewa,miskilanci ,fuskan nan a daure tamau amma haka bai sa kyawunsa ,kwarjinin fitowa ba jikinsa sanye da jeans with white t-shirt Ya daura black jacket akai masu tsada fuskansa dauke da face mask girar nan a hade fuka kaman zaiyi aman wuta 🔥, bayansa Ashman ne shima jikinsa sanye da da jeans blue da white t- shirts masu kyau sun amshe shi sosai ,shima fuskansa a daure dan shima ranshi ba karamin baci yayi ba .

Shigo wa cikin incomplete building in suka karasa yi ,cikin sauri wani soja ya dauko masa kujera mai kyau ya zauna tare da yi crossing na legs nashi .

Gabriel kam tunda yayi ido biyu da “boss lion” ya sake fitsari a wandonsa a hakan ma bai San yayi fitsarin ba tsabar firgita da yayi .

Benjamin kam tunda yaga “boss lion” yaji kansa ya fara juyawa saboda firgitan da yayi dan shikam yariga da yasani wata mutuwansa ya kama,ya tsokano abunda yafi karfinsa ,dan zufan da yake yi yanzu ya nunka na da ninkin ba ninkin .

Junaid kam yana ganin boss lion ya fada jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciya tare da cewa “ yaya boss nasani bazaka taba barin wani ya cutar da junior ka ba & I so much love you ,ya karasa magana tare da goge hawayen sa ya dago yana kallan boss lion da ganin sa kawai ya keyi amma bai ce komai ba danshi fah ba iya lallashi yayi ba.

Ashman ne yace “Lallai junaid wato kaga yayanka shine ka manta da dayan yayan naka ko, duk na damu amma ka wani shareni kaman badan kai nazo wajan ba ya karasa maganan tare da kara daure fuskan sa.

Junaid bai San lokacin da dariya ya kwace masa ba dan yaji abokin fadansa ya fara complain,sauka daga jikin “boss lion” yayi tare da zuwa ya rungume Ashman yace yaya ash kasan ai bazan manta da kai bako ya fada har yanzu da murmushi akan fuskan sa.

Ashman dake kallon sa cike da soyayya yace na hakura badan halinka ba ,dan in zance dan halinka ne kam ai inaga bazan kara maka magana ba ,amma ya zanyi inason dan kanina,cikin jindadi junaid yace “ Nima Ina sonka yayan junaid ya fada yana dariya.

Mikewa “boss lion “ yayi ba tare da yace wa kowa komai ba ya fita daga wajan Ashman da junaid na suka bi bayansa.

Yayinda sojojin suka kama Benjamin,Gabriel tareda dan uwansu mutum daya da ba’a kashe ba aka saka su a gaba har cikin mota , yayinda “boss lion” sun rigada dunshiga cikin nasu dankara dankaran motocin bakake masu tinted suka fita da gudu kaman zasu tashi sama ,tafiyan 30min sukayi suka isa gidan saboda gudun da sukeyi.

Bayan sun isama ma sai da “boss lion “ ya ja musu aji kafun ya fito cikin kasaita da nutsuwa ya shiga cikin part in.

Bayan sun iso gida ne aka kada kan su ,Benjamin,Gabriel da dayan aka wuce dasu disipline room kuma dakin duhu ,aka rufe su.

Junaid da Ashman sun rigashi shiga har junaid yake tambayansa”yaya ash ya akayi kuka gane inda nake .

Anan Ashman ya bashi labarin abunda ya faru

WAYWAYE ADON TAFIYA ❄️

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌍 Destiny, Love ❤️ & Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ,game bukatan karanta wa ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar zaki iya turo katin shaidan ki ta wannnan number 08161857656 Nagode 🙏

page 📃 14

“ BOSS LION”

Zaune yake akan L-shape chair dake dakinsa ,da table na glass a ciki za kaga fishies 🐟 suna yawo da ruwa a ciki saman table in kuma a Kwai wasu roses 🌹 masu kyau each color a kwai ,idonsa a lumshe zakayi tunanin bacci yake yi,ga Ashman dake tsaye a gabansa ya rasa meke masa dadi,kan ganinsa kasan hankalinsa ba’a kwance yake ba,sai murza goshinsa yake yi.

Bai dade da dakko “boss lion “ a airport dan bazai dan bazai wuce 20mins ba suka samu sako daga sojojinsu dake biye dashi a baya, sojojin su kasu kashi biyu ne daya suna binsa a matsayi bodyguards nashi daya kuma suna lura da yanda wayancan suke nasu aikin dan “boss lion” ne ya zuba su saboda tsaro.

Cewa sukayi sojojin da suke kulada junaid fah duk an samesu a sume ,alamun wani abun suka shaka musu batareda sun ankara ba,gashi basuga junaid ba.

Cikin sanyi murya Ashman yace “ kuma duk wanda ya shakawa sojojin mu powder suka dauke junaid, tunda ya fara maganan “boss lion” baice masa Uhmmm ko uhuhm ba idonsa a lumshe har lokacin bai bude idonsa ba.

Abunda ya bawa Ashman mamaki shine yanda yaga boss lion yayi mishi banza kaman bai san yanayi ba dan ko ajikinsa mai nuna ya damu da abunda da Ashman ya fada ba dan shifa har cikin zuciyansa wannnan ba damuwansa bane.

Ganin bai kula saba yasa ya kara cewa yaya boss junior din kane fah ,da kakeso kuma kake basa kulawa da duk wani tsaro daya kamata,kuma baka barmu munyi kukan maraici ba karkasa niyanzu na fara,ka sanima ko yanzu junaid din kuka yake yi.

Ashman fa shi a dole dadin baki yake masa saboda ya damesa,idan ya damesa ko bayaso zai amsa masa saboda ya rabu dashi.

Kaman yanda Ashman yake Tunani kuwa hake da ba karamin damunsa yayi ba ko hutawa bai yi ba yazo ya tasa shi gaba da magana kaman zai cinye sa, bude lumsassun idon sa yayi da sukayi gray sosai da alamun gajiya a cikinsu ya bude labbansa a hankali yace” Ashman what going on , just relax, kasamu waje ka zauna kazı kawani tsayamun kerere a kai kaman na maka sata”ko Baka yarda da yayanka naka bane ,kai ma kasan wannan abun yayi kadan ya daga mun hankalina,dan baba tunnanin a duniya nan akwai abunda zai daga mun hankali,cikin fahimta yace “ nayarda dakai yayana.

Bayan 2 minute “boss lion” ya cewa Ashman “ miko mun system ina”toh ashman ya fada tare da wuce wa bed side drawer ya dauko ya ajiye masa a gaban sa akan table din gabansa ,bude wa yayi yashiga wasu wajaje yace” matso kaga ni,ba musu ashman ya matso yana kallon system din.

Abunda ya bashi mamaki shine yaga duk conversation din junaid da yan daban a cafeteria suka sace shi harda yanda yayi gaba suka bi bayansa , “ boss lion” yana sauka a kasan a ka turo masa wannan video.

Cikin yana yin damuwa Ashman yace” to ai bamusan inda suka kaisa ba”karka damu ,I will found it ,as soon as possible, indai har diamond watch in nan yana hanun sa ba abunda zai hanani gane inda yake,cikin mamaki Ashman yace which watch ? “ irin wanda yake hanun ka,yafada tare da nuna masa diamond watch din dake hanun sa, cikin gam suwa da bayanin sa Ashman yace “ok.
Chapter 10 · 0% Book details