← Book details Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 24

Sashe 12

Sirrin Dake Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

page 📃 16

AFTER SOME HOURS

2:33pm

Ta gama abincin rana mommy ta fita anguwa tare da zainab da Aneesa amma dai sunyi sallama da aneesa “zainab kam tana ganinta Taita dariya harda habaici “ohh Duk wannan kyau din duk yanganan dai akan dan shaye shaye zaki kare “mudai zamuzo cin abincin biki “bakaken maganganu taita fada ma sultana kuma abun takaicin ma agaban mommy ba abunda tace sai ma dariya datake yi alamun itama abun ya mata dadi ba dan kadan ba.

Tana zaune a falo tana ganin tv ,idan ka ganta zakiyi tunanin hankalita yana kan tv ne amma sam ba haka bane tayi zufi cikin tunani.

A hankali khalifah ya isa wajan ta,wanda dawo wansa kenan daga office ,,sunanta ya kira”Sultana,Sultana Sultana har sau uku kafun ta firgita daga tunanin data tafi kallonsa tayi ,,da mamaki akan fuskanta dan bai taba mata magana ba agidan .

Cikin nutsuwa yace zamu iya magana ,sai datayi dan Jim kafun tace eh “zama yayi akan one seater dake facing nata yayi gyaran murya yace”maganan da zamuyi tanada matukar muhimmaci kidan bani aron hankalin ki ,dago Kanta tayi ta kallesa, ta gyada masa kanta “dan shi fah kalifa kyakyawane black beauty dan yafi jabir kyau nesa ba kusa ba dan munin mahaifiyasa jabir ya daukko tareda zainab kawai dai su farare ne farin mahaifiyar su suka dauko.

Yace “ shin abunda jiya naji jabir ya fada mana gaskiyane? Cikin jin ba dadi tace eh gaskiya ne ko akwai wani abune,gyara zamansa yayi yace “amma dan Allah karki yarda ki auresa dan kinfi karfin auren irin wayanan mutanen “cikin mamaki Sultana tace saboda mesa zaka ce hakan”saboda ina sonki,tun ranan Dana fara ganin ki sonki yaymun dirar mikiya please ki Fasa auren wannan abun .

Ki aureni nutkuma Zan baki gata da kulawa da duk mata take bukata a gidan mijinta karkiga laifina ,kullum dake nake kwana nake tashi , kisoni ko kadanne please,ya karasa maganan muryansa a rarrabe .

Cikin tausayinsa sultana tace kayi hakuri banida wani zabi daya wuce na auresa ,bawai dan bakamun ba”a’a kawai dai banajin hakan mai yuwuwane dan haka ina maka fatan alkairi,tana gama fadan hakan ta miki ,shima cikin sauri yamike yana cewa”please sultana karki mun haka dan Allah.

Girgiza kanta tayi tace” kai zan bawa hakuri please ka ajiye wannan magana a gefe tana fadan haka ta koma kitchen ta barshi tsaye kaman an dasashi yakasayi kwakwaran motsi.

Kashe gas din tayi ,ta sauke tukunyan ta juye ruwan zafin flask ta ajiye ta gyara zaman niqab dinta ta fita daga kitchen din,a falo taga Khalifa a tsaye a inda ta barshi tanufi hanyar fita bata cemasa kalaba tayi ta fiyanta ,shikuma da ido ya rakata dayayi jaaa sosai .

Komawa tayi gidan dan bata tunanin daga yau innah zata kara batinta ta fita,abun takaicin ba abunda zata, ma ta na alkhairi sai ma sharri.

Tana komawa gida ,ko minute 5 batayi ba wani yaro yashigo yace “ana kiranta a waje, ammasawa tayi da”toh, ta gyara hijab dinta ta fito waje ,a bakin kofan gidan ta samu garbati tsaye ya na busan taba ,harkan fuskanta,tuni ta hada rai ,cikin masifa tace wanna wani irin dabbanci ne yake damunka,zakana fesamun hayaki da kuma warin tabanka “duk wanda kasha a waje bai isheka har sai kazo gidan,kuma har kan fuskana saboda wulakanci.

Haba beb ko gaisuwa babu zaki hauni da masifa , gani nayi ya kamata ki saba tunyanzu kafun mushiga daga ciki ,kuma dakike cewa “nayi miki wulakaci ai ba abunda kika gani ,a cikin abunda na iyah,sai nan da kwana hudu daurin aurenmu zaki zama halaliyata anan zaki gane na’iya wulakanci “ki shirya fah dan zamuci “uwar sabada a daren farkon mu “duk dama dai nasan kema yar hanune.

Cikin bacin rai tace kagama ,kwai kuwa my beb ai je ta dabance kinsan ni mai sa’a ne gashi kuma zan auri balarabiya wai duniya tayi mun dadi ya fada cikin nishadi.

Ka ajeye wannan a kanka “kaganin nan ta fada tana nuna kanta tace”wallahi nafi karfin ka ,irinku ne fa ya kamata ace yanzu ma kuna gidan yari,insha Allah “sai gani sai hange ,hangen ma idan kasamu kenan “saboda bakada kunya harni zakazo kanamun maganan banza “toh bari kaji karka sake zuwa gidanan da sunan kazo waje na ,dan zan maka rashin mutuci wallahi.

Ko akan hanya ka ga mai kamata ka canja hanya dan nikam bazan dauki rainin hankali ba “Kaje can ka karata da shaye-Shayen ka ,kaji na fada maka .

Tana karasa fada bata sauraresa ba tayi koma wa ta gida ,ta barsa sai masifa yaki yi kaman ya ara baki.

___________________________________________✍️

Abuja,Nigeria

Kwance take akan gado sai juyi takeyi takasa bacci ,gashi gobe da wuri zata tashi dan zasu raka ya alameen airport dan hutunsa har ya kare,tana jin ba dadi cikin ranta zai tafi dan duk abunda yake mata tanason yayanta kuma shima yana sonta,kawai dai muddin suka hadune sai sunyi fada koda kuwa abun bai taka kara ya karya bane.

Taya ma za’a ce basa san junansu bayan suna uwa daya uba daya .

Cikin ikon Allah bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba .

Washe gari

Ta danso ta nakara sallan asuba dan bata samu bacci da wuri ba jiya ,Allah ya sota ma yau weekend ne ,tashi tayi tashiga toilet tayi alwala tayi sallah .

Shiyawa tayi cikin dogon rigan atampha nevy blue and ash dinkin irin fitted din nan ne daidai Jikinta da akwai shape kam ba kaifi tayi daurinta mai kyau ,Masha Allah tayi kyau kaman ka saceta ka gudu.

Daukan ash gyale tayi ta fito dashi a hanun ta dan jirginsa 7:00am zai tashi gashi yanzu har 6:33am tayi ,,a falon kasa ta samesa da shida Ammi dan yanzu macewa yake “wai Ammi yariyar nan bazata fito bane saita batamun lokaci .

Cikin sauri tace ganinan yaya ina shirya wani,batar da yaganta ba yace ki dakko mun akwatina a daki ,kisame mu a mota,ta amsa da toh ,shikuma ya wuce parking space.

Gurin Ammi taje tace,”good morning Ammi “cikin kulawa ammi tace” morning daughter “ kintashi lafiya”,lafiya kalau ammi ,toh kije ki daukko masa abunda ya aike ki Nima ganinan zuwa,idan yaso saiki samemu a parking space”kinji? Eh baji ammi.

Dakinsa ta wuce taga karamin a kwantin a kan gado ta daukko ta fito ta samu har ammi ta wuce,itama sai ta fita .

Ta samesu a cikin motan ammi tana baya ,ta bude motan tace”yaya alameen ka budemun boot in din na saka akwatin,bude wa yayi batare da yace komai ,ta bude ta saka yashigo sai a lokacin yaga irin kayan data saka dan tayi mishi kyau amma yashi zafi yanda ammi bata mata magana akan kayan ba ta fito a haka kamar arniya.

Shiga tayi yaja mota da gudu har Ammi tana cewa”sannu alameen harka gaji da ganin mu kenan kakeso ka kashemu,cikin kwantar da murya yace ammi kiyi hakuri baza’a sake ba.

A haka har suka isa Nnamdi Azikiwe International Airport sauka sukayi dan har an fara kiran passengers dan sunyi latti ,daukan akwatinsa suka yi sallama da ammi “alameen dan Allah akula banda kula abokan banza ,ka tsaya kayi abunda ya kaika kaji,,Toh Insha Allah “Yauwa Allah yatsare ya bada abunda akaje nema ,,saduwan alkhairi “Ameen ya amsa.

Shukrah ma tace yaya Allah ya kiyaye hanya sai yaushe zaka dawo “hararanta yayi yace”Ameen amma dai nasan dama Allah Allah kikeyi na tafi dan kina ganin kaman ta kura miki nake ,yanzu saboda Allah kiga irin kayan da kika saka tsa kani da Allah kin kyautawa kanki kenan ,yayi kasa da murya yace please koda banan karki sake sa irin wayanan kaya koda a gidane dan bakisan wa zai shigo “kinji?

Eh yaya alameen insha Allah bazan sake ba “good sai na dawo kuma badda rashin ji please bye “Insha Allah tace tare da daga masa hannu ya wuce.

Ammi kam tana cikin mota batasan me suke fada ba ,sai da ya tafi kafun ta fito tawuce driver site ta zauna ,shukrah tana zauna a kujeran mai zaman banza ammi ta ja motan suka wuce gida.

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

page 📃 17

Yau saura kwana daya daurin aurenta damuwa da rashin mafita ne ga kuma rashin cin abinci ne ya sata agaba har tayi wani uban rama tayi wani fayyaw,sai haske data kara tass da ita kaman jini ya fito,ga kashin wiyan daya fito mata saboda rama.

Tayi kukan ,tayi kukan har ta godewa Allah,gashi ba mai kulata a gidan ,dan ko zulaihat da take kulata yanzu ta daina
,abun ba karamin damunta yake yi ba “tariga da ta yake shara datake ganin shi zai fisheta .

Habiba ce ta shigo daki ba sallama ba komai ,cikin rangwada da iyeyi tace,sai ki tashi kije babba yana kiranki munafuka aurene dai sai anyi sai dai bakin ciki ya kashe ki ,dan mu kokin mutu ba’abun daya damenu,tan tarasa fada tafice daga dakin tare da jan dogon tsaki tabar dakin.

Mikewa tayi ta dauki hijab nata dake gefenta tasaka ta fito daga saki,gidan shaw ba kowa ,kumawai a haka gobe ne daurin auren .

A kofan dakinsa ta tsaya tayi sallama kafun ya bata izinin shiga ciki ,shiga rayi ta samesa zaune akan taburman dake shimfide a tsakiyan dakin,ta durkusa har kasa ta gaishe shi.

Bayabo ba fallasa ya amsa,tsayawa yayi kawai yana ganin ta yana saka wani abu a ransa,danshi wallahi bai tsaneta ba kawai dai indai zai ganta ne,zaiji kwata kwata baya dinta a kusa dashi.
Chapter 12 · 0% Book details